Abdulrazaq Yahuza Jere" />

Shehu Ibrahim (RTA) Ma’abocin Faidha III  

Masu karatu Assalamu alaikum. Barkan mu da sake haduwa a wannan makon domin fahimtar darasinmu na yau kamar yadda ya dace, za mu dan yi waiwaye kadan daga darasin makon jiya.

Malami Mai Yawan Sani Wanda Ya Tara Ilimi Ya Kuma Fahimci Ilimin, Ma’abocin Yin Littattafai Manya Masu Yawa, Wanda Ya San Ilimin Walitta Mai Yawa, Khalifan Shehu Ahmadattijani (RTA) A Kasar Magrib“Morocco”, Jagora Shehu Sukairujul Ayyashiy (RTA), Yana Aikowa Da Ma’abocin Faidha Shehu Ibrahim (RTA) Wakoki Masu yawa (da wasikoki Masu yawa, ni ma ina da daya a hannuna da rubutun hannunsa mai albarka , wasikace doguwa mai tsawo wato yawa, har labarin cikin gidansa da na ‘ya ‘yansa da lamurmuransa bai boye wa Shehu Ibrahimba (RTA). Al’adar muridi da shehi, kuma Shehu Sukairuja ya san haka (RTA), amma Bawan Allah (TWT) ne, tun da ya ji daga majiya mai karfi kuma ya gani, ya taba, ya dandana, ya shaka, ya taka sannan ya kwanta a kai, to bari ya nuna a aikace. Allah ka ba mu koyi da shi cikin bin Ma’abocin faidha saw da kafa).

Da yake ba da shaidodinsa masu yawa akan wannan ma’anar (kuma akwai abin lura fa, duk shaidar da zai bayar sai ya ce gaya mar waridi ya yi, kuma ya sa shi ya fada, mun kuma san wane harshe ne yake yi masa waridin“maganar”, harshan Shehu Tijjani ne (RTA) mai tsarki, don Shehu Sukairuja (RTA) yakai ba kowa tsakaninsa da Shehu Tijjani (RTA) sai dai “Harazimiyya” , to yau ga Harazimiyyar ya gani da idonsa mai daraja, to me ya rage ma sa ban da mika dukkansa (RTA) don kar ya hwadi a idon Hadhara, kuma don kar masu koyi da shi da wadanda suka sa ido su ga me zai faru tsakaninsa da mai Faidha, su dogara da shi su ki bin Faidha, ba su san Shehu Sukairuja (RTA) mai arzikin lahira ba ne “sa’idi” kuma ba su san zafin bugun da Shehu Tijjani (RTA) ya yi ma sa ba don ya kiyaye shi halaka, – a zatona Shehu Tijjani (RTA) bai yi wa wani irin sa ba – ko Shehummu Muhammadul Hafizi na Misra (RTA) ai almajirin Shehu Sukairuja ne (RTA), ganin irin wannan sallamawa ta Shehu Sukairuju (RTA) da wasu dalilai ya mika wuya ya tafi kafa-da-kafa har cikin dakin Shehu Ibrahim (RTA) a Madinar Kaulaka, kuma Shehummu (Malam Abdullahi Masjidi) ya ji abin da ya gudana da kunnansa, ya kuma gaya wa Shehunnanmu, kai har ma shuwagabanninmu Sharifan Morocco, Shehu Sukairuju (RTA) ya yada Shehu Ibrahim (RTA) a wajansu kafin su ga Shehu (RTA) domin tafiyar Shehu Ibrahim (RTA) Hajji ta farko a 1935, da ya bi ta Morocco a garin “darul baidha’i”, Shehun garin mukaddamin zawiyya, malami mai yawan sani, mai jinjina Ilimin “nakadiy” mai yawan fahimta, mai gaskiyar soyayya cikin Shehu Tijjani (RTA), shugabanmu Muhammadu Dan Aliyyussusiy (RTA) ya karbi bakuncin Shehu Ibrahim (RTA), sannan ya kwankwashi Ilimin Shehu (RTA) da walittarsa (RTA) ya ga yaya?, Shi da kansa ya ce: wallahi waliyyi babba kuma mukaddami shugabana Husainul Ifriniy (RTA) ya yi gaskiya da yace: bakaken fata baramun walitta ne, “ma’adinin walitta, ma’ana ramin da ake hako walitta, sannan kuma shugabana Ahmadassukairuju ya ce min: kai ne malamin bakaken fata duka.)

 

Yana Daga Cikin Shaidodin Fadinsa (Shehu Sukairuju (RTA:

 1. Amincin (Allah (TWT) Da Ba’a Iyakance shi, Ba’a Iya Kirge shi (ya tabbata a gare ku ya Shehu Ibrahim RTA), Kuma Ba Irin Wannan Kyauta Ta Allah (TWT) Ce Ake Bincikenta Har A ce An kai Karshan Saninta A Tsakanin Halitta ba.
  2. Amma Wannan Baiwar Kai Ne Mai Ita (Shehu Ibrahim (RTA) Kuma Ka Cancance Ta Ne Saboda Abin da Allah (TWT) Ya sa A Cikinka Na daga Cika “Kamala” Wanda Babu Wani Mutum Daya Ko Waye shi “Ahadun” Da Zai ce Ya ga Tawaya A Wajanka (Alhamdulillahi, sai dai a yi hassada a dinga kago karerayi).
  3. Na yi Shaida, Na Gani Da Idona Nakaina Da Nabasirata, Na Tabbatar Ma(ma’ana na saki), Zan Ma Bayanin Abin Yadda Yake, Na Rantse Lallai Allah (TWT) Ya Yi Maku Budi Mabayyani (na yi bayani a cikin lamba ta takwas 8 ) Sabi da Abin da Ya Baku (ya Shehu Ibrahim (RTA),
  Kai Kadai Ubangijin Gaskiya (TWT) Ya Kyebanta Da Wannan Baiwar A Tsakanin Halitta.
  4. Kai Ka Gaje Khalifancin Shehu Tijjani RTA, (wato faidha), Na Gaya Muku (ya Shehu Ibrahim (RTA), Karatun Ka ji shi Yadda Yake (ko Ka sani ko ba ka sani ba ko wani ya gaya ma ko ba a gayama ba, to gashi na fada: kai ka gaje Khalifancin Shehu Tijjani (RTA)
  5. Ni (Sukairuju) Na ga Kuma Ina Ci Gaba Da Gani, Cewa Shehu Tijjani (RTA) Shi Zoben Waliyyai Ne (Wannan shi ake cewa “tauraya” a zo da magana mai ma’ana biyu, ta kusa da ta nesa, amma ta nesan ake nufi, kiran Shehu Tijjani (RTA) da zobe “katimu” ana nufin cika makamin walitta, kuma ya dau na zoben ma, ma’ana shi Shehu Tijjani (RTA) adon waliyyai ne, kamar yadda zobe yake adon hannu ko jiki ma, haka aka fassara a wajan cikamakon Annabawa kuma adonsu, Kakan Shehu Tijjani (RTA) Annabi Muhammadu (SAW).
  To Da Allah (TWT) Ya Nunamin Shehu Tijjanine Zoben Waliyyai (RTA)Sai Ya Nunamin Kaikuma (Shehu Ibrahim (RTA))Kaine Dutsan Kan Zoben,(wane mutum, da a ce irina ko Shehunnaina ma na bakar fata suka fadi haka da alkiyamar munkirai ta tashi, amma a ce Shehu Sukairuju (RTA) ya fadi wannan magana, to wallahi ka san ya keru (RTA) da kuma kiran Shehu Ibrahim da yake da lamirin jam’i, da kuma daukan nauyin yada Shehu (RTA) da ya yi a cikin sharifan jikokin Shehu Tijjani (RTA) da mukaddamansa na duniyar Larabawan Yamma da Arewacin Afirika, to jama’armu sai a yi hattara kwarai, lamarin Shehu Ibrahim (RTA) ya fi karfin wasa)
  6. Da Yawan Bujumai “Manya” Da Suka Daga Kai Da Alfakhari Har Aka Zaci Suna Kafada Da Kafada Da Ku (Ya Shehu Ibrahim (RTA) A cikin Wannan Matsayin, Amma Da Mai Ganin Haka Yana Da Idon Walittaka; Da Ya San Ai An Yanke Fukafukansu (ma’ana yankakkun sirri ne ba su da komi na walitta da na madadi, fanko ne sai dai kuri, to amma ba kowa yake ganewa ba, Allah ka sa mu gane mu tsaya wajan Ma’abocin Faidha albarkar Shehu Sukairujan (RTA) da yayi mana wannan ishara amin).
  7. Ya Kaicon Wanda Ya Zama Yana Yi Muku Girman Kai Da Jayayya (ya Shehu Ibrahim (RTA), To Wannan Mutum (mai wadannan halaye) Ya Hadu Da Shan Wahala Kuma Abin da Yake Nema Ba Zai Same shi ba Har Abada (‘yan uwana, Shehu Sukairuja ne fa (RTA) me fadar wannan, Allah ya saka masa da Alkhairi, a yi hattara fa).

Iya nan Shehu Muhammadu Abdullahi Dan Sayyidi ya kawo. Amma yana da ragowa, ina da ita cikakkiyarta amma na duba ban ganta ba, a yanzu don Allah in da mai ita, ya rubuto min don alkhairin ya game, na gode.
Daga Littafin “Min Akhbarish Shaiki Ibrahima” Na Shehu Muhammadu Abdullahi Dan Sayyidi Sharifi Batijjane Dan Faidha, Mutumin Shingida, Murteniya (RTA).

Exit mobile version