Daga Abdulrazak Yahuza Jere
Jagoran Ahlul Faidhati Mai Diwani Group, Shehu Isma’ila Umar Almaddah ya bude Tafsirin Alkur’ani mai girma na watan azumin Ramadan da ke dab da shigowa a zawiyyarsa da ke unguwar Sabon Garin Tudun Wada a karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, cikin Jihar Kaduna.
Shehin ya bude tafsirin ne tare da maja-bakinsa Alaramma Malam Ahmadu a ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe biyu da minti ashirin da biyar na rana.
A zaman tafsirin na farko, Shehu Isma’ila ya shafe tsawon awa daya da minti talatin da doriya yana zuba karatu, inda a ciki ya gode wa Allah da ya sake nuna mana zuwan azumin bana tare da addu’ar Allah ya sa mu ga karshensa cikin koshin lafiya.
Malamin ya dauki lokaci mai tsawo yana bayani a kan falala da sirrin da Alkur’ani mai girma ya kunsa na zahiri da badini, ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmi a ko ina cikin duniya su sha damarar rubanya kokarin ibadun da suke yi domin samun Rahamar da Allah ya yi tanadi a cikin watan na Ramadan mai dimbin falala.
A ci gaba da bayaninsa, ya bayyana cewa, “Alhamdu lillah, muna godiya ga Allah da ya hada mu a wannan shekara mai albarka. Za mu bude karatun Tafsiri na kur’ani a shekara ta 1442 Hijiriyya (2021 miladiyya) a wannan waje mai albarka, zawiyya daga cikin Zawiyyoyin Shehu Tijjani Abul Abbas kuma zawiyyoyin ‘Yan Faidharsa. Da hali mai albarka wanda muke ciki mun tafi zuwa ga Allah har yanzu don mu ji maganar Ubangijinmu wanda sifa ce daga cikin sifofinsa, tajalli ne daga cikin tajalliyoyinsa, don haka ba makawa wanda yake so ya samu haka sai ya hada biyun. Sai ya hada jikinsa da ruhinsa bakidaya. Zuciyarsa da jikinsa, sannan zai iya amfanuwa da wadannan guda biyu.
“Mun taru don mu ji Tafsirin Littafin Ubangiji mai albarka wanda shi ne kundin tsari ko mulki wanda shi ne yake sanar da mu Ubangijinmu da Manzon Allah (SAW) ya zo ya sanar mana da shi. Duk abin da ka sayo a kasuwa sai ka ga an hada shi da littafinsa (manual) wanda zai yi ma bayani. To bayanin Ubangijinmu da na addini bakidaya ga shi nan a kur’ani. Haka nan bayani kan mu’amalarmu da inda muka fito da inda za mu je duk yana ciki.”
Shehu Isma’ila ya kuma jaddada muhimmancin aiki da kur’ani tare da Hadisan Manzon Allah (SAW), domin a cewarsa, Annabi Muhammadu (SAW) shi ne kur’ani a aikace tun daga Muhammadiyyarsa har Zatinsa.
Malamin ya kuma nunar da cewa duk fasahohin zamanin nan na kirkire-kirkire da kere-kere duk kur’ani ya kunshi bayaninsu amma sai ga wanda yake da ilimin abin, domin tajallin kur’anin ne ne a cikin dukkan hadarori.
Shehu Isma’ila ya kuma ja hankalin al’umma su kara girmama sha’anin bayin Allah, domin duk abin da suke jaddadawa a cikin addini sun samo ne daga kur’ani da kuma abin da Shari’ar Manzon Allah (SAW) ta kunsa. Yana mai cewa, “duk kasaitar Waliyyi babban abin da zai yi shi ne mayar da mutane kan shari’ar Manzon Allah (SAW) yadda take a zamanin Manzon Allah”.
Har ila yau, ya yi karin haske a kan bambancin farillolin addini da nafilolinsa da kuma yin kira ga wadanda ba su san kan ilimin addini ba su daina cakudi da kawo rudani a tsakanin al’ummar Annabi (SAW).
Ya yi addu’ar Allah ya dauke dukkan matsalolin da al’umma take fuskanta a kowane bangare na rayuwa, tare da hore wa kowa abin da zai yi sahur da buda-baki shi da iyalansa bakidaya.
Bude tafsirin dai ya samu halartar mutane daga ciki da wajen Kaduna da kuma wasu jihohi makota kamar su Kano, Katsina har da Bauchi da sauransu.