Connect with us

LABARAI

Shehu Sani Ga Buhari: Ka Kashe Kudaden Da Aka Kwato Na Abacha A Kan Ayyukan Da ‘Yan Nijeriya Za Su Gani

Published

on

Sanata Shehu Sani, Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya ki amincewa da yadda gwamnatin tarayya ta shirya kashe Dala Miliyan 320, kudaden da aka samu kwatowa aga cikin kudaden da tsohon shugaban kasa marigayyi Janar sani Abacha ya sata a lokacin yana mulkin Nijeriya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, za a ajiye kudadaen ne a wani tsari na musamman mai suna “conditional cash transfer (CCT)” inda za a rinka rarraba ga ‘yan Nijeriya masu fuskantar matsananciyar talauci.”
A ranar jumma’a ce, gwamnatin tarayya ta ce, ta shirya tsaf don fara rarraba kudaden ga iyalai 302,000 masu fuskantar matsananciyar talauci a jihohi 19 na kasar nan daga wannan watan na Yuli.
Da yake tsokaci a kan al’amarin ta hanyar kafar sadarwa ta Twitter, Sanatan ya ce, wannan tsarin ba zai yi tasiri ba don wadanda zasu amfana zasu fito ta hannun gwamnoni da ministoci da ‘yan majalisu da kuma makusantar Buhari, saboda haka ya bayar da shawarar a yi amfani da kudaden wajen yin aiyukan da kowanne dan Nijeriya zai iya gani.
“Rarraba Dala Miliyan 350 da aka kwato cikin kudaden da Abacha ya sata ga ‘yan Nijeriya Miliyan 180 abu ne da ba zai yiwu ba,” a sakon nasa na Twiter ranar Asabar “Daga karshe zai kasance ‘yan uwa da kuma sunayen da suka fito ne daga gwamnoni da ‘yan majalisa da kuma mutanen shugaban kasa ne kawai zasu amfana da wanna garabasar, ya kama a kashe kudin ne wajen yin aiyyukan da ‘yan Nijera za su iya gani da idonsu,”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: