Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna
Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, ya mayar da kakkausar martani ga Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufai, dangane da kalaman gwamnan akan Sanata Shehu Sani, a yayin da gwamnan yake gabatar da wani shiri da ya saba gabatarwa kai tsaye a kafafen yaɗa labarai a duk ƙarshen wata, wanda kuma ya gabatar a jiya Lahadi.
Sanata Shehu Sani ya ci gaba da mayar da martani da cewa, “Duk abin da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufai zai gaya maku kan maganar bashin nan ƙarya ne kawai. “
Sanata Sani ya ƙara da cewar, “Dama ya saba da zuga ƙarya da yaudaran Jama’a ta hanyar ƙarya da yaudara. Kwamintin da nake shugabanta a majalisar dattijai ita ke da alhakin bayarwa ko kin bayarwa, zage zage ba zai sa mu bayar ba, babu kuma Sanatan da zai sa hannu sai da ni kwamarad Shehu Sani.”
Gwamnan da yace Bukola Saraki bai da biyayya ga jam’iya, gwamnan da ya taimaka wajen gurfanar da Bukola Saraki a kotun CCT, gwamnan da ke kan gaba wajen sukar Bukola Saraki wai baya son Shugaban Ƙasa Buhari.”
“ Idan gwamna yaji haushi ya hau dutsen kufena ya wuntsulo, idan har kace Sanatoci 108 sun yarda a baka bashi amma Sanata ɗaya ne ya hana har yanzu ba’a baka bashin ba to, to, ashe Sanata ɗayan nan ne dahir.
Tabbas El-rufai ya ruɗe, ya birkice, ya zare saboda bashi. Lallai al’ummar Jihar Kaduna sai kun yi masa ruƙiya tun kafin ya koma Sambatu. SabodaYace ni ‘mahaukaci ne’ saboda na Hana shi Bashi. Shin akwai baban mahaukacin da ya wuce Mai zagin Sardauna?
Akwai baban mahaukacin da ya wuce Mai ikirarin ya kai Marigayi Shugaba Umaru Yar’adua kabari?
Akwai Babban mahaukacin da ya wuce Mai zage zage ba dalili? Akwai Babban mahaukacin da ya wuce Wanda ke shirin Koran Malaman makarantu har mutum dubu 20,000? Akwai baban mahaukacin da ya wuce mai Koran Hakimai dubu 4000?”
Sanata Shehu Sani ya ƙara da bayyana cewar, “Akwai Babban mahaukacin da ya wuce mai rushe ma Mutane gidajen su? Akwai Babban mahaukacin da ke son Hana wa’azzi?. Akwai Babban mahaukacin da ya wuce mai rawa cikin jama’a ko ba kiɗa? Ko da yake kun san ranan lahadi Mammy market dake 44 kusa da gidan gwamnati cika yake da manya.
Allah ya raba mutanen Jihar Kaduna da bashin da ya’yansu da jikokin su za su gada. A cewar Sanata Shehu Sani.