Connect with us

LABARAI

Shehun Bama Ya Rasu Ya Na Shekara 65

Published

on

Sarki mai daraja da daya a masarautar Borno, Shehun Bama, Alhaji Kyari Ibn Umar El-Kanemi, ya rasu a asibiti a birnin Maiduguri bayan gajeruwar rashin lafiya ya na da shekara 65.

Da ta ke tabbatar da rasuwar basaraken, Gwamnatin Jihar Borno, ta bayyana cewa ya rasu ne da ranar Litinin a birnin na Maiduguri.

Marigayin, dan kimanin shekaru 65 a duniya, shi ne Shehu na Bakwai a tsohuwar Masarautar Dikwa da su ka kunshi Bama, Dikwa, Ngala da Kala-Balge a yankin karamar hukumar Bama a jihar wanda daga bisani a ka raba ta gida biyu zuwa masarautun Bama da Dikwa.

Kwamishina a ma’aikatar al’amuran yau da kullum, yada labarai da al’adu a jihar Borno, Babakura Abba Jato, shi ne ya sanar da hakan a sa’ilin da ya ke zanta wa da manema labarai a birnin Maiduguri a zaman da kwamitin yaki da yaduwar Korona a jihar.

Haka kuma, Kwamishina Jato ya kara da cewa, kamar yadda a ka sani, Mai Martaba Shehu ya dade ya na fama da rashin lafiya, musamman a irin shekarunsa na tsufa.

Haka zalika kuma, a bangarennshi, Hakimin Nganzai, Bakaka Abubakar Ibn Umar Garbai, Al-Amim El-Kanami ya sanar da rasuwar Shehun Bama.

Ya ce, “Shehun Bama ya rasu ne jim kadan bayan sallar la’asar a birnin Maiduguri,” inda ya bayyana cewa ya rasu ne a asibitin koyarwa ta Jami’ar Maiduguri.
Advertisement

labarai