A ranar Lahadi ne aka gudanar da Maulidin Manzon Allah da shugaban kanfanin SKY, Alhaji Kabiru Sani Kwangila ya saba shiryawa da gudanarwa duk shekara.
Taron Mauludin wanda ya gudana a kusa da gidansa dake kan titin zuwa Gidan Gwamnati ya sami halartar dinbin jama’a maza da mata yara da manya da kuma Shehinnan malamai da dama da kumakuma mawaka masu yabon Manzon Allah.
A dai taron zaman Maulidin malamai sun yi jawabai akan halaye da dabi’un Manzon Allah da yanda yakamata mutane da shugabanni su koya su yi aiki dasu don samar da al’umna nagari abin koyi.
A lokacin zaman Maulidin an yi addu’oi ga kasa Allah ya kauda halin matsalar tsaro da ake fama dashi da kuma yi wa shugabanninta da shi kansa mashiryin Maulidin Alhaji Kabiru Sani Kwangila addu’a tare da yaba masa akan irin hidima da dawainiya da yake wa Manzon Allah ta raya kaunarsa a zukatan al’umma ta shirya irin wannan gagarumin Maulidin duk shekara.
Daga cikin malamai da manyan baki da suka albarkaci wajen Maulidin sun hada da Wazirin Kano mai murabus limamin masallacin juma’a na waje Sheik Nasir Muhammad Nasir da Sheik Tijjani Bala Kalarawi da kwamishinan ayyuka na musamman na Kano, Dokta Muktar Ishak Yakasai da sauran jama’a. A yayin.Maulidin an yi rabon kayan abinci ga dinbi mabukata.