Daga Mu’azu Harɗawa, Bauchi
Shahararren Malamin addinin musulunci Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya shawarci ’yan majalisun Nijeriya, da su riƙa lura da maganganun samar da dokokin da za su haifar da cigaba tsakanin jama’a, tare da rage wahalhalun da ake fama a maimakon, ɓata lokaci kan maganganun da ake taso da su domin karkatar da hankulan mutane, zuwa ga abin da ba shi ne damuwar su ba.
Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da ya kira makonnin baya, inda ya bayyana cewa abokan gabar musulunci, ke kawo ruɗani don raba kan mutane da kuma shiga gonar Allah, tare da saɓa masa, don haka ya shawarci kowane mai faɗa a ji a Nijeriya ya koma ga Allah wajen ganin ya samar da abin da zai ciyar da ƙasa da mutanen ta gaba. Ya bayyana cewa a madadin musulmin Nijeriya duk abin da Allah da manzonsa suka ce a yi shine, suke yi, basa buƙatar shigar da mutane hanyar saɓawa Allah da manzonsa, saboda sun fi kowa ilmi da tausayin bayin Allah da sanin ya kamata, don Annabi (SAW) ya fi kowa sanin abin da ya fi dacewa da ɗan adam.
Saboda haka ya ce misali kan muhawarar da aka yi shekaru biyu kanmusulmi basu yarda da dokar da ake neman ƙirƙirowa na cewa ba a yarda mutum ya aurar da ‘yarsa ba, sai ta kai shekaru 18, idan ya aikata ya karya dokar ƙasa, ya ce, akwai dokokin ‘yancin ɗan adam dana addini a dokokin duniya waɗanda ko nasara ya amince dasu. Don haka musulunci shine ya tsara duk wata rayuwa, da ake son mutunta mutane da addininsu, donhaka wannan doka bata dace da musulunci da musulmi ba, saboda manzo (SAW) ya ɗaurawa Aisha aure tana da shekaru tara.Sayyidina Abubakar shima ya ɗaura aure da shekara tara. Ya ce, fito da irin waɗannan dokoki, yin karan tsaye ne wa musulunci da musulmi, da kuma neman ƙuntatawa musulmi.