Sheikh Dahiru Bauchi Ya Goyi Bayan Kalifancin Tsohon Sarki Sanusi

Kalifanci

Daga Khalid Idris Doya,

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya amince tare da nuna goyon bayansa ga nadin da Babban Kalifan Shehu Ibrahim Inyas, Sheikh Mahiy Inyass ya yi wa Tsohon Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II a matsayin Kalifan Tijanniya a Nijeriya, inda ya nunar da cewa wannan nadin abu ne da ya dace.

Dahiru Bauchi wanda ya bayyana amincewarsa a yayin da tsohon Sarkin, Muhammad Sanusi Lamido Sunusi ya kawo masa ziyara a gidansa da ke Bauchi ranar Litinin, yayi amfani da wannan damar wajen jawo hankalin sabon Kalifan da kada ya ji cewa shi yana gaba da wani, ya sani an nada wasu Kalifanci kafin shi kuma ta hanyar nuna musu biyayya da girmama su ne zai kai ga cimma nasarorinsa.

Sheikh Bauchi ya hori Sanusi da kada ya bari siyasa ko ‘yan siyasa su shigo domin farraka kyakkyawar alakar da ke tsakaninsa da shi, yana mai cewa kalifanci babban abu ne wanda ake bukatar ka da a hada ta da lamarin siyasa, “Khalifanci babban abu ne, kada ka bari siyasa ya shiga tsakani.” In ji shi.

Dahiru Bauchi ya bayyana cewar Kalifofin da Shehu Ibrahim Inyas ya nada da kansa su ne asalin Khalifofi, kuma an hada Sanusi ne bisa nazarin cewa kakansa ya taba zama Kalifa wanda Shehu Ibrahim Inyass ya ba shi da kansa, “Khalifofin Shehu suna nan da yawa, Khalifanci kamar Janarorin Soja ne, a gidan soja akwai Janarori da yawa, amma wanda ya fara zama Janaral sauran Janarorin suna sara masa da cewa ‘Mon Sir’, haka abun yake, wadanda suka riga zama Khalifofi sun fi wadanda aka basu yanzu, don haka kada ka ji nadin da dan Shehu ya maka kamar ka fi sauran Khalifofin Shehu ne, a’a, Khalifofi suna da yawa a Nijeriya.”

Shehin ya yi fatan a sake samun kyakkyawar danganta, kuma yana mai fatan wannan nadin zai kara bunkasa Darikar Tijjaniya da kuma addinin Musulunci a Nijeriya da ma Afrika.

Tun da farko a nasa jawabin, Khalifa Muhammad Sanusi, ya shaida cewar sun kawo ziyarar ce domin neman goyon baya da shawarwarin su Shehin dangane da wannan nadin da aka masa a matsayin Khalifa. Ya bayyana cewa Shehi uba ne a gare shi kuma shi da ne gare shi, don haka ne yake neman goyon bayan yadda zai samu nasarar hidimta wa Darikarsu dari bisa dari.

Sanusi ya nuna dadaddiyar akakar da ke tsakanin Shehi da Kakansa a matsayin wata alakar da ta jima kuma za su kara dinke ta. Ya kuma yaba wa Shehin bisa tsayuwa masa da ya yi ta yi a rayuwa tun lokacin da aka fara maganar tsige shi har zuwa ga tsige shi a matsayin Sarkin Kano. Ya gode masa kan hakan kuma ya sake neman hadin kai da goyon bayansa.

 

Exit mobile version