Sheikh Dahiru Ya Shirya Addu’ar Sabuwar Shekarar Musulunci

Daga Khalid Idris Doya,  Bauchi

Kamar yadda ya saba duk shekara, Shaikh Dahiru Usman Bauchi yakan shirya gami da gudanar da zikirin sabu shekaran musulunci na jihiriyya domin yin addu’o’i na musamman da kuma yin addu’a kan matsalolin da kasar nan ke fuskanta.

Taron na wannan shekarar 1439 wanda ya gudana a ranar Asabar din makon da ta gabata, a dakin taro na Multipurpose ya samu halartar dumbin jama’a daga sassa daban-daban na kasar nan.

A yayin taron, an sha jawabai daga Shehin Malamin inda ya bayyana muhimmancin zaman lafiya da kuma muhimmancin da addu’a kan matsalolin da ake fama da su a kowanne lokaci. A wajen taron wanda aka yi karatun Alkur’ani, zikirori da kuma Istigfari da dama, an fara taron ne tun da yammacin wannan ranar har zuwa bayan Isha’I inda aka yi ta jero addu’o’I da kuma fadakar da jama’a kan muhimmancin shekarar ta musulunci.

Da yake zantawa da manema labaru a wajen taron jim kadan bayan kammala addu’o’i da zikirorin shiga sabuwar shekara, Shehu Dahiru Bauchi  bayyana godiyarsa ga Allah da ya kawo mu wannan lokacin, inda ya nuna cewar yi addu’a da yin zikiri abu ne wanda ake matukar bukatarsa a kowanne lokaci, musamman irin wannan lokacin da Nijeriya ke fama da yawaitar tashi-tashina da kuma wasu yawan aiyukan ta’addanci a wasu sassan Nijeriya, sai ya be dukkanin wasu matsaloli da kuma damuwowin jama’a maganinsu dai shi ne addu’a “Maganin dukkanin matsalolin da suke faruwa a kasar nan shi ne addu’a, rashin tsaron da ake kukansa maganinsa Allah ne. kuma Allah mun rokeshi da ya kiyaye mana kasarmu, ya kiyayemu ya bamu lafiya da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali. Wannan shi ne maganin matsalolin Nijeriya a halin yanzu addu’a komai maganinsa Allah ne”. in ji Shehin

Dahiru Bauchi ya ce dole ne gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da samar wa matasa sana’o’in dogaro da kai domin ganin sun daina shiga cikin wadannan munanan halayyar da suke shiga na ta’addanci da kuma rikici “Ina rokon gwamnati da ta kirkiro wa samari marasa aikin yi, aikin da za su yi domin su samu aikin da zasu rika wanda zai basu dama su daina shiga wannan hatsarin da suke shiga a halin yanzu na ta’addanci da tashin hankalin jama’a”. In ji Shehin

Daga bisani ya yi kira ga dukkanin jama’a kan su rungumi addu’a da komawa ga Allah domin samun tsira a nan duniya da kuma gobe kiyama “Dukkanin musulman duniya ina kiransu da su zo mu tafi wajen Allah, manyan mu su ji tausayin kananan mu, kanananmu su girmama manyanmu a samu a tafi lafiya da zama lafiya”. A cewarsa

Wakilin LEADERSHIP A Yau, Lahadi ya rawaito cewar babban makasudin shirya wannan taron da Shehu Dahirun ke yi domin yi wa kasa addu’a da kuma bayyana abubuwan da suka kunshi shiga sabuwar shekara, kana da kuma yin tuba zuwa ga Allah kan laifukan da bayi suka yi a shekarar da ta wuce, haka kuma, akan yi addu’a domin samun shiga sabuwar shekarar cikin nasara da kwanciyar hankali. A bana ma kamar kowace shekara haka nan aka yi, inda gungun jama’a daga bangarori daban-daban suka yi ta zafga addu’o’in neman mafita daga kuma neman yafiya a wajen Allahu Subhanahu wata’a.

Manyan baki sun hada da Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar wanda ya samu wakilcin Dakta Malami, gwamnoni da sauran manyan malamai da zakirai daga sassa daban-daban na kasar nan. An yi  taron lafiya an kuma kammala lafiya inda aka samu dandazon mahalarta.

Exit mobile version