Nasir S Gwangwazo" />

Sheikh (Dr.) Yusuf Ali: Rayuwa Da Ayyukan Gina Al’umma (7)

Takardar da Dr. Bilkisu Yusuf Ali ta gabatar a taron kasa da kasa, don karawa juna ilimi a sashen koyar da harsunan Nijeriya da kimiyyar harshe na jami’ar jihar Kaduna ranar 2-4 ga Afrilu, 2016.

Cigaba daga makon jiya.

3.6 Kafofin Sadarwa

Bilkisu (2013:35) ta bayyana kafofin yada labarai da wata kafa ce ta isar da sako don fadakarwa da ilimintarwa da nishadantarwa, zuwa ga al’umma. Misali kafofin sadarwa a yau sun hada da talabijin da radiyo da jarida da mujalla da akwai na gwamnajin jiha akwai na gwamnatin tarayya akwai masu zaman kansu da na kasashen waje. Bayan wadannan akwai kafofin sadarwa na zamani na facebook da whatapp da twitta da sauransu.
Sheikh Dr. Yusuf Ali ya fara shiga radiyo a shekarar 1972 ya fara sfciga gidan radiyon Kano ne lokacin ana kiransa da NBC duk ranar alhamis karfe 5:30 na yamma inda yake hira da masu rubuta wakokin Hausa shi ne yake jagorantar mawakan shi yakfc nemo mawakan. Shirin ya samu nasara ne da jajircewar Sheikh Dr. Yusuf Ali .An ci gaba da shirin har zubya 1983 lokaci mulkin Buhari na farko,sai radiyon Kano ta kirkiri shiri don yaki da rashin da’a. Shi ma wannan sun fara da karanta wakoki sai dai a kan yi shimfida da nasiha kafln a karanta wakokin daga nan ya fara sakin jikinsa ya yi wa’azinsa ba fargaba. A ranar farko ya fara da matsayin shan taba a musulunci. A lokacin an sami jigo daban-daban wadanda suka magana kan tarbiyya da da’a ya yi wakoki daban-daban misali cin hanci da rashawa da shan taba da zumunci da girman kai da karya da sace-sace da tsafta da rashin da’a da cin amana da shaye- shaye da taimakon gajiyayyu da sauransu.
A shekara 1984 ya fara wa’azia talabijin na CTB a shirin Daren Juma’a da mu’amulat. A 1987 rediyo Kano suka ba shi shiri na shi na kansa mai suna “mai gida kan gida da hasken muslunci tun daga 1987 har zuwa yau ana gabatar da shirin a radiyo Kano.
Shirin gyadar dogo da mai gida kan gida da sahabbai da hasken imani duk wadannan’ ana gabatar da su ne a gidan Radiyo Kano. Akwai na NTA Kano da Radiyo Najeriya na Kaduna da kama akwai hasken muslunci a NTA Jigawa, haka a DITB ta Kaduna shirin kar tsaya yake gabatarwa a kira a waya ya ba da fatawa kai tsaye a kan duk wani abin da ya shafi duniya da lahira.
Shi ne malami na farko a arewa da ya fara shiri kai tsaye na kiran tyaya a shekarar 2000 a shahararren shirinsa na Ilimi Kogi. Haka akwai shirye-shiryensa a NTA Kaduna da NTA Zamfara da NTA Sokoto inda aka sa tafsirin sa duk shekara.Shirin sa/’ria adabul islam ana gabatar da shi a CTB Kano da jihar Borno. A shekarun baya da akwai TB Kogi da nagarta radiyo wanda duk talata ana yi shirin a baya, KSTU Kaduna.
Akwai shirin dausayin musulunci da har yau shehin yana ba da gudummawar cikinsa duk sati. A freedom radiyo shi ma a yanzu haka ana gabatar da shi duk ranar laraba na mumbari malamai ranar Juma’a da laraba ana gabatar da shirinsa kai tsaye mai suna zauran malamai da karfe sha daya zuwa sha biyu na dare a gidan radiyo na edpress.
Ya na ba da gudanarsa lokacin zuwa lokaci a gidan radiyo na BBC da muryar Amurka da muryar Jamus. Akwai jaridun irin su Almizan da Albishir da Alfijir (wanda take zuwa da ajami) da mu’amalat da trumph da kuma dillaliya. Akwai jaridar leadership Hausa inda suka ba shi shafi biyu don gabatar da fatawa a baya.
Duk shirye-shirye da ake gabatarwa kamar ilimi kogo da .tafsir da karatun Riyadussalihin na talabijin din NTA da CTB da na radiyo Kano duk shehin kan ware makudan kudade ne daga aljihunsa ya biya karatun da al’umma za su ji. su amfana. Akwai Tafsirinsa da ake sawa a radiyo Kano duk ranar lahadi a yanzu haka. Sannap akwai sokoto da Jigawa da Kaduna da ake sa Karatun tafsirinsa duk azimi wanda duk shehin ke biya da aljihunsa saboda yada addinin muslunci da daukaka Kalmar Allah.
4. Tasirin Ayyukan Sheikh Dr Yusuf Ali

Duk aiki in har ya zama na alkhairi ya kan yi naso na kwarai ga al’umma. Sheikh Dr Yusuf Ali kamar yadda bincike ya gabata yana kan gina al’umma ne tun daga tiasowarsa zuwa yau bai ko numfasa ba duk da nauyi da ke kara karuwa kan sa kullum.
Duk abubuwan da ya yi al’umma ke anfanuwa misali duk wandaya zo da bukata da bukatarsa ta biya ko ya sami waraka ya sami tasiri na aikinsa. A yau abin alfahari ne a tasirin ayyukan Sheikh Dr Yusuf Ali yadda aka sami masu rukiyya da masu islamic chemist ciki da wajen Kano.
Daliban nazari ba za su taba mantawa da tasirin ayyukan Sheikh Dr Yusuf Ali ba inda a shekarar 2004 Salihu Muhammad Dalibi a jami’ar Bayero ya yi a lcundin digirinsa na farko me suna “Rayuwar Ustaz Yusuf Ali Da Ayyukansa Kan Adabi.”
An yi amfani da wakokinsa da dama ba adadi an yi nazarinsu dalibai sun sami abin dogaro a duniya adabi, wakokin sun cike gibi kan jigon soyayya zalla a rubutattun wakbki. misali a littafin Dauusayin soyayya da Wakokin hikima da sauransu. Haka malamai sun yL amfani da wakokin don kafa hujja a mukalolinsu misali akwai Mukalar Farfesa Ibrahim Malumfashi me suna “Soyayya Hawainiya ko Dala “ inda ya kafa hujjoji da wakokin soyayya na Sheikh Dr Yusuf Ali. A littattafan yara ‘yan sakandire Hanyar Nazarin Hausa sun yi amfani. da wakarsa a karkashin jigon soyayya.
Ko shi a kan kansa Sheikh Dr Yusuf Ali ayyukan sun yi tasiri kan sa don yana alfahari da su burinsa ya cika wakokinsa na soyayya tun daga wancan lokacin har zuwa yau yana kan bakansa kuma suna cikin abubuwan da yake alfahari da su.
A bangaren gidajen radiyo kuwa Sheikh Dr Yusuf Ali ya bar abin koyi me kyau inda ba gidan radiyo ko talabijin din da ba sa shirin fatawa a kira waya kai tsaye ba wanda nasort shirinsa ne na “Ilimi Kogi”.

 1. Kammalawa
  Wannan takarda ta kunshi gwagwarmaya da fadin -tashin Sheikh Dr Yusuf Ali tun daga lokacin haihuwa da kuruciya da neman ilirainsa, yadda muka ga kacokam din rayuwarsa a zangon farko duk ya yi ta ne a neman ilimi. Ko da burinsa ya cika abin nema ya samu mun ga yadda gwagwarmayar ta sauya salo inda ilimin da aka samu ya zamana an sadaukar da shi ne ga al’umma ta hanyar ayyukan gina al’ummar. Daga cikin ayyukan akwai; Malanta da magunguna da wa’azi da sufanci da adabi da kafofin sadarwa. Kwalliya kam ta biya kudin sabulu sai ‘yan abin da ba a rasa ba wanda wannan bincike ya hango wanda da za a kara akan kokarin baya da tabbas za a kara wa daben makuba.
  Yana da kyau a taskace ayyukan Sheikh Dr Yusuf Ali don za a fieme su watarana, musamman na wakokinsa don amfana da baiwar da Allah ya yi masa ta tsara waka da dinban – kalmomin da yake amfani da su da dama tsantsar Hausa ce da a yau ba a amfani da su ko don wayewa ko maraya inda aka cakuda harshenmu da na baki alhalin ga’muda wadatattun kalmomi. Masana da ke yin kamusu yana da kyau su nemi ire -iren wakokinsa don samun rumbun kalmomi. Wallafa ita ke dauwama, duk abin da yake a rubuce; ya fi wanda alia haddace don haka laccocin Sheikh Dr Yusuf Ali yana da kyau a taskace su a mayar da su littafi inda ko me dadewa za a sami littafin.
  Duniya yanzu ta koma a tafin hannu don haka yana da kyau wa’azin Sheikh Dr. Yusuf Ali da sauran aayyukansa na gina al’umna ake sa wa talabijin da radiyo da wadanda yake yi a lokacin tarurruka kamar laccoci irin na azimi da wadanda yake yi lokacin mauludi da saukar karatun kur’ani da sauransu a sa su a a kafofin sadarwa na duniya irin su youtube, da Tubidy da Bidclip da internet da sauransu.
  Hannu daya ba ya daukar jinka. Duk da Sheikh Dr Yusuf Ali ya yi kokari gun gina website dinsa wanda ke dauke da wasu abubuwa da suka shafi ayyukansa akwai bukatar kari. Don an dauki shekaru ba a bibiyi sashen ba yana da kyau a sami matallafa da za su ke-dura sababbin abubuwa a sashen.
  Tsangaya a wancan lokacin duniya ce guda wadda tarihinta da tasirinta tsahon lokaci in har ba a yi rubutu an adana ba tarihinta zai gushe duba da a.yau irin wannan tsangayun babu su saboda gari ya tarar da su in ma kuma akwai an sami tasirin bakin al’adu ga kuma yadda karatun boko ya cudanyaa rayuwar yau. Samun wanda ya san tsangaya da abin da ta kunsa kamar gwarzona a zamanin nan abu ne me wuya.
  Akwai bukatar rubuta littafi don tarihin Sheikh Dr Yusuf Afi duba da rubuce – rubucen da a ka yi baya kansa ana daukar wani sashe ne kawai a duba irin gudunmawar da ya i bayar ba a shiga dukkan bangarori na tarihinsa. A wannan takardar da na rubuta na lura. tamkar a maliya ne ka dibi komayya.
  Daliban Nazari na dukkan bangarorin uku harshe da adabi da al’ada yana da kyau su bibiyi gudunmawarsa don za amfana da ilimi da darussan rayuwa musamnlan ta yadda za a fahimta ba a hawa sama tsanin kuwa shi ne ilimi da jajircewa kuma babu maraya sai rago.
  Burin Sheikh Dr Yusuf Ali ya cika sai fatan al’umma ta dora daga inda ya tsaya tare da bibiyarsa don neman shawara. Alkalanci aiki ne mai girman gaske inda ba wanda ya cancanta da ya zamo alhaki sai mai ilimi malami. Aikin Alkali shi ne yin sharia ta hakki da sauransu.
  Daliban naziri na dukkan bangarorin uku harshe da adabi yana da kyau su bibiyi gudunmawarsa don za su amfana da ilimi da darussan rayuwa musamman ta yadda za a fahimci ba a hawa sama. Tsanin hawa shi ne ilimi, da jajircewa kuma babu maraya sai rago.
  Burin Sheikh Dr Yusuf Ali ya cika, sai fatan al’umma ta dora daga inda ya tsaya tare da bibiyarsa don neman shawara.

Karshe!

Exit mobile version