A yau 18 ga watan Yuni Dokta Mamman Shata Katsina ya cika kwanaki 7,300 da rasuwa, wanda ya zo daidai da shekaru 20 cif. Allah Ya gafarta masa, Ya gafarta ma iyayen mu gaba daya, Allah Ya sanya Aljanna ta zama masaukin su, tare da mu na dindindin.
Tun daga ranar da zakin mawaka ya rasu na yi tuntuni, na cewa idan Allah (SWA) Ya raya ni na kai shekaru 20 bayan rasuwar sa zan duba in yi tambihi akan matsayin sa a lokacin. Babban abin da za a duba a yau a game da Shata shi ne yanda mu’amullar sa da mutanen sa da tauhidin sa ga Allah suka yi aiki ga rayuwar sa lokacin yana raye, da ma bayan babu shi. Iyayen gidansa wadanda ya yi ma wakoki sun tallabe shi cikin mutunci, sun nuna masa gatanci na musamman ma. Wannan shi ne dalilin da ya sanya a farko da tsakiyar zamanin sa bai ji kunya ba, bai ji kunyar makada da mawaka abokan hamayyar sa ba. Watau na game da cika baki ya furzas da ya rika yi a wakokin sa da dama, na ratar da Allah (SWA) Ya hukunta ya ba sauran mawaka. Kalmomin da ke nuna cika baki ya furzas sun hada da: ‘….Zaki mai banka mai ban kasha, Mamman…’ da kuma: ‘…ruwa ya bace sai kwarawan asali, kauce yaro kada kadannu su kashe ka…’ Yakan kuma ce: ‘….Yanda Yai man, Bai yi ma maroka ba, ko makadi, ko wani mai waka, ko wanene…’ Wadannan kalmomi suna matukar dugunzuma tare da hasala mawaka, don dai babu yanda za su yi da shi. Amma yana shan zagi a wajen su kamar kurar bara.
Komi na musamman aka yi ko aka nuna masa, na gatanci daidai gwargwadon baiwa da daukakar da Allah (SWA) Ya yi masa, da kuma fifikon da Ya yi masa akan sauran mawaka.
A cikin shekaru 20 da rasuwar Shata, a yau, kamar makadin yana raye, tunda ga wakokin sa nan barkatai ana ta jin su kullum. Ba ma jin su kadai ake yi ba a yanzu, har da rubuta su ake yi, ana karantawa. An yi bincike-bincike masu yawa da rubuce-rubuce da tarurruka masu yawa akan mawakin.
A cikin kwanaki 7,300 da rabuwar Shata da Duniya an rubuta littattafai akalla 3 ko 4 akan rayuwar sa, kuma a ciki an zubo wasu daga cikin baitoci na wakokin sa jefi-jefi. Bayan wannan ma Farfesa Sa\idu Gusau ya wallafa littafi na Diwanin Shatan da ke dauke da wakokin sa kawai ba tare da tarihin sa ba. Sannan kuma Hukumar Tarihi ta Jihar Katsina ta wallafa wasu littatafai biyu suma akan Diwani ko rubutattun wakokin makadin. Wannan ya nuna maza-maza yanda hukumomi da masana suke yunkurin adana wakokin sa ta sigogi daban-daban, sabili da tasirin su da sakonnin da suke dauke da su. Sannan kuma ga dalibai nan masu karatun digiri daga na daya zuwa na uku a jami’o’in mu suna bincike a fannoni daban daban a kan rayuwa da mu’amulla da kuma sigogin wakokin makadin. Saura ga su nan kala-kala a manyan makarantu, da har ana yawan turo wasu zuwa gare ni ina duba masu ina ba su duk bayanan da suka kamata.
Yanzu ma abin ya ci gaba, abin ya dauki sabon salo, kowanne dalibi sai ya dauki wani fanni na daban akan rayuwa da wakokin makadin. Wasu su kan yi bincike akan wakokin sarakuna, wasu akan wakokin mata, wasu akan wakokin zambo, da sauransu. Ko kuma a wakokin sarakunan ma (duk da yake an dade ana rubutu akan wakokin fada ko na iko, amma dai Shata shi ya dada fadada wakokin fada tunda al’amarin sa yana da fadi) ko na mata, wasu su kan tsuke abin su takaita kurum akan binciken wakar sarki daya ko ta mace daya da makadin ya wake. Malam Hamza Usman Kankara na Kwalejin Ilimi mai zurfi ta Katsina ya yi nazarin digirin sa na biyu akan wakokin Shata na ta’aziyya. Bashir Dankaura ya rubuta kundin digiri na farko akan wakokin Gagarabadau ta Shata da ta Mammalo yaron Shatan. Misalai biyu ke nan. A kuma fanin tarurruka don kara wa juna ilimi a manyan makarantu, nan ma al’amarin Shatan ya dauki sabon salo, manazarta ko masana kan dauki wani bagire daya tilo su yi batu a kan sa. Wannan ya nuna cewa an ma samu sabon fage a nazarin adabi. An samu mawaka na zamani masu tasowa wadanda ke amsa sunan Shatan, ko da kuwa mutum (wasu kade-kade yake daban) ba kwaikwayon Shatan ya ke ba, kurum saboda kwarjinin sa. Shi kan sa Shatan bai san cewa za a raja’a a yi ayyuka a kan sa kamar yanda ake yi a yanzu ba kafin ya rasu. Yau gas hi, shekarun sa 20 a kasa amma ga Shatattaki nan ko’ina a Arewacin Nijeriya da ma wajen ta suna fadada adabi da sunan sa.
Akwai abubuwan lura ga Shata a nan. Ko da ake ce ma sa ‘Mahadi mai dogon zamani’ ana nufin duk tashen mawaki, duk kwarjinin mawaki, duk ficen sa ba ya wuce shekara 10 zuwa 30, dole za ya kwanta ko tauraruwar sa ta dushe, ko wanene shi. Kai ko da kuwa Ibrahim Narambada
Tubali ne ko Musa Dankwairo Muradun. Tunda mun binciki mawakan Hausa masu yin ‘kuriga’, Narambada na a cikin su. Narambada na hawan gwaji ko ‘kuriga’ kafin ya gabatar da waka, akalla na sati biyu. Saidai ko bayan shekaru 30 a canza ma wakar wani sabon salo, ko yara su zaburo su amsa, kai ubangida kana a gefe guda a matsayin jagora kurum. Shi ko Shata ya shekara 63 yana waka, yana yin abu daya. Wannan shi ne sababun wannan kalma ko inkiya.
A sha’anin tashe, na san ba mawaki ba, ko budurwar kauye tana iya yin sa, watau ta yi zamani kafin ta yi aure. Wasu mawakan ma kafin su cira sun kwanta. Irin wadannan, zamanin su ba ya wuce shekaru 5 zuwa 10, kamar su : Aura, Turai Rimaye, Ayashe mai kidan duma Fanteka, Aliyu Disco Baby Argungu, Ahmadu Monkey, Murtala Kaura, Sa’idu Ziti, Sani Dan Indo, Sani Sabulun Sunlight Kanoma, Ali Makaho mai gurmi, da sauran su. Lissafin ba ya karewa.
Gaba daya idan ka tattara zancen zaka iya daure shi da tsumma daya, na cewa babban abin fata ga rayuwa shi ne mutum ya roki Allah idan karshen sa ya zo ya zo da kyau, Allah Ya kawo mataimaki wanda za ya tallabe shi.
Da Allah Bai kawo ma Shata dauki da Jarman Kano Muhammadu Adamu Dankabo ba da ya samu nakasu da wulakanci daga maroka a shekaru 10 na karshen rayuwar sa. Da sun yi masa dariya, na yanda karshen sa za ya kasance. Ma’ana, da Allah Bai kawo masa Kabob a da bai samu yanda yake so ba, su kuma da sun samu yanda suke so.
Akan ba ya da lafiya, cikin 1998 a Kazaure a bukin sabon Sarki Alhaji Najib Husaini Adamu, makadin na kwance a masauki watau Rest House, da safe sai Abdu Wazirin Danduna ya yi masa sallama don samun na ceface. Ko da jin muryar Danduna, sai Shatan ya yi karfin hali ya yi wuf ya tashi daga kwance ya fizgo babbar riga ya sanya cikin hamzari, sannan ya zauna bisa kujera kamar ba abin da ke damun sa. Ya ce ‘a ce masa ya shigo’. Ya shigo. Suka gana, har makadin ya ba shi babbar riga mai asake da naira dubu 5. Sai da ya fita Shatan ya ce ‘duk makiyin ka kada ka nuna masa ba ka da lafiya, da ka nuna masa, to ya samu yanda yake so’. Shatan ya kara da cewa: ‘ba wai kudi suka kawo shi ba karya yake yi, zuwa ya yi ya ga yaya jiki na yake don ya ji an ce ba ni da lafiya, yanda za ya ji dadin zuwa gaba ya tallata ni, har y aba mutane labarin irin yanayin da ya same ni’.
To haka ya yi ta fama da maroka; munafukai kuma mahassadan sa. A gaban sa su nuna su masoyan sa ne, amma ba su kaunar sa a boye. Abin nan da Hausawa ke cewa ‘ka ga mutum a fuska Annabi Musa amma a zucci Fir’auna’ Tauhidi da yawan nuna ikon Allah da yarda da Allahn su suka ceci Shata daga hannun makiyan sa maroka.
Tun daga farkon zamanin sa, da maroka suka lura da irin baiwar da Allah Ya yi masa ta musamman ce, suka shiga yi masa asirrai da sammace-sammace don kada ya yi tashin gwauron zabon da ya yi. Daga karshen rayuwa kuma abokan gaba da Shatan ya faskare su suka zura idanu su ga yaya rayuwar sa za ta kare. Shin za ya mutu cikin halin wulakanci koko cikin rufin asiri ? To sai ga shi Allah Ya ba su kunya, ba su samu yanda suke so ba.
Ko da yake wani na iya cewa ‘ai Allah na iya aiko da wani makamancin Dankabo din. Amsa a nan ita ce ‘a’a’. Ba a yi kamar Dankabo ba, ba kuma za a yi kamar sa ba har kasa ta nade, a ta fuskar Alhaji Shata dai, dama wadanda suka yi mu’amulla da shi. Gurbin Kabo yana da wahalar cikewa. Zan fadi dalili a gaba.
Dalili, duk wani ubangidan Shata, sai da makadin ya sallaci gawar sa. Ma’ana, duk kusan iyayen gidan sa sai da suka rasu sannan shi ya rasu daga baya. Ga su nan birjik, kamar su Usman Liman Sarkin Musawa (1939), Sule Musawa (1936), Isan Torobi (1940), Magajiyar Musawa (1940), Inuwa Mammada Ketare (1940), Sulen Jebu Jos (1959), Sheriff Mamuda Kano (1955), Sheriff Sidi Kano (1955), Jabbi Dan Fulani Jos (1960) (ba na Kaura Namoda ba), Doki Dan Karoni Guru (1954), Ahmadu Na-Funtuwa (Sa’in Katsina; 1954), Sule Jikan Korau (1948), Makaman Katsina Idris Nadabo (1943), Sardauna Gamji Dan kwarai (1962), Sulen Garo (1960), Balan Goggo (1965), Iro mai ‘yankunne Sokoto (1965), Waziri Ibrahim (shugaban GNPP; 1978), Sarkin fawa Dan Gawan Kano (1957), Kwasau Kaura (kakan Sahabi Liman Kaura) (1952), Alin Katako Maiduguri (1960), Abu Dan Lagai-Lagai (1956), Haruna Kasim Kano (1955), Maude Tabako (1962), da sauran su.
Wadanda suka rage wadanda farat da garaje ba za su iya yi masa wani abu ba ne ko da wata hidima ta taso, saidai suna amsa sunan iyayen gidan sa kurum. Wasu ma daga cikin su ciwo ya cinye su ko kuma Duniya ta yi ambaliya ta ture su waje daya, ko in ce zamani ya daina yayin su. Wasu kuma sun gama aiki sun koma gida sun zauna, al’amurran rayuwa sun yi sanyi, zamani ya hadiye su, an ma manta da su. Irin su, ina iya tuna Bukar Mandara (1960), Maitama Bello (1980), Sani Stores (1947), Bello Katagum (1969), Cuku Dan Sale Dankamasho Damagaran (1952), Janar Sani Abacha (tsohon Shugaban Kasa; 1993), da dai sauran su da ba lallai azimun sai an lissafa su a cikin wannan bagiren ba.
Dankabo sutura ce babba, kuma uba ne ga zakin mawakan. Na maimaita, Allah Ya suturta Shata da Dankabo. Duk addu’o’in da makadin ya yi ta yi a cikin wakokin sa, da nuna tauhidin da ya yi ta yi (ba ma dai a cikin wakokin Bakandamiya wadda ta ke uwar wakokin sa): Allah don Allah Allah, da kuma ‘…ya ji ya yarda…’, ko kuma da ya ce: ‘…Da yanda na ce Mai Jalla. Bugu da kari akwai wurare a Bakandamiya kuma da ya kan ce: Ka raba mu da mahassada Allah, don girman zati, ya kan kuma ce: Da kan Ka na hada Ka Allah, ban hada Ka da kowa ba Allah, Ka yi mani don girman zati. Ya kan kuma ce: Na dai gane maroka tsoro na suke ji, to ku tafi na yafe ku, na daina batun ku ‘yan tselen hwannan’. Duk a cikin tauhidi yak an ambaci: ‘…don yau da gobe ta Allah ce, jibi, gata fa, Mamman ta uban wacece, fada masu duk ta Allah ce, har tsitta, na san haka, sai yaya? A ci gaba ne yak an ce: ‘….ya zo man ya sa baki, ya ci durin hwashi…’ da sauran su.
Daga baya kuma yana cewa: ‘…Ga Shata ya zo, zai duba maroka tun ba su mai barna ba…’ A wani wurin kuma sai ya ce: ‘…Ga Shata ya zo ku gudu maroka, sai kaka? Daga kurkusa kuma yana cewa: Allah babu inda Bai yi gwani Nai ba, ga gwani daya, ni wurin waka, eye. Gaba dayan Bakandamiya waka ce ta tauhidi da neman Allah Ya raba Shata da sauran mawaka lafiya, kada fitinar sammace-sammacen da asiran su su iso gare shi, ko kuma idan sun iso kada su yi tasiri ko aiki a kan sa. Su mawaka sun san haka, shima Dodo ya san dalilan da suka sanya ya rika nuna tauhidi ga Allah, don ya gama lafiya. Da farko an yi Dangaudu (ko Dangaure) yaro Shata wanda a cikin 1940 a Jikamshi lokacin da makadin ya tafi ya gaishe da kakar sa ta wajen mahaifi watau Dije maikitso, ya hada kai da wani mai kudi na garin ya sato masa layu da gurayen da Isan Torobi ya sanya aka yi ma makadin don kariya daga abokan gaba, mahassada. Bayan sace su (don wuri guda suke kwanciya, da Shata da Dandaugu din) wanshekare mai halin nan ya kona su, shi kuma wanshekare ya mutu, sannan Dandaudu ya makance, duk a dalilin wadannan guraye da layu da aka raba da Shata.