Mohammad Albarno" />

Shekara 6 Da Batun ‘Yan Gudun Hijirar Gwoza, Wane Hali A Ke Ciki

Garin Gwoza, daya daga cikin kananan hukumomi 27 da ke jihar Borno wanda suke fama da matsalolin tsaro. Wanda yau kusan shekara 10 kenan da rashin samun cikakken zaman lafiya a yankunan, tare da rasa rayuka da zaman dar-dar da jama’a ke yi.
Yau kusan shekaru 6 kenan da al’umman garin suka yi hijira sakamakon harin Boko Haram da ta kai a shekarar 2014 tare da kafa daula, wanda suka kira ta da, Daulatul Islamiya.
kungiyar Jama’atu Ahalis Sunna Lida’awari Wal Jihad, ko Islamic State in West Africa (ISWP) wanda aka fi sani da Boko Haram, wun shiga garin Gwoza da misalain karfe 4:00 na yamma, a ranar Talata 5 ga watan Agusta 2014. daruruwan mutane ne suka rasa rayukan su, sannan sama da mutum Dubu 300 ne suka kauracewa gidajen su zuwa hijira wani gari.
kungiyar ta yi ikirarin kafa hukumar Musulunci, tare kuma da karbe duk wasu madafan iko, tare da sauke tutar Nijeriya sannan suka daura bakar tuta mai dauke da hatimin sunan Allah a rubutun Arabiya.
Wani daga cikin wadanda suka gani da idon su yayin da abin ya auku, ya shaidawa wakilinmu cewa “Ina tashan danbua sai muka ga motoci suna ta fituwa ta hanyar zuwa danbua daga Gwoza. Mun dauka motocin sojoji ne sai daga baya mukaga Babura a gefe da rawani akan su. Sai mukafara gudu kowa na gudu, suna isowa kan titin Mubi zuwa Maiduri sai suka fara harbi. Daganan muma muna gudu, wasu a keke, nima a keke nake, wasu a kafa daganan sai suka harbi wani a kusa dani shikuma a kafa yake, sai na jefar da keke na yi wani gida, a inda muka boye mu 3”.
Isowar su kan hanyar, sai suka yi hanyar Gidan Gwamnati da yake Low Cost, suka tarwatsa jirgi mai saukan angulu na Sojoji, wasun su kuma sunyi hanyar TC, sukayi ta fafatawa da jami’an tsaron dake mashigar gari daga Adamawa.
Akalla sun share kusan sati guda suna ta barin wuta, an kashe mutane da dama, an kuma yi asarar dukiyoyi masu yawa.
Wani ma’aikaci a babbar asibitin garin Gwoza, ya ce, “Ni dai a binciken da na yi ya nuna kimanin mutum sama 3000 suka rasa rayukansu a karamar hukumar Gwoza”.
Binciken shi kenan wanda ya gudanar a shekaru 4 da suka gabata, yace “Abinciken da na yi a 2016 ya nuna masa cewa, kimanin mutum sama da 3000 ne suka rasa rayukansu, kuma an yi asarar dukiya sama da biliyan biyar 5
kungiyar da ta fara ikirarin kiran kafa Daula tun a 2006, anyi yakin farko a shekara ta 2009, bayan kashe Shugaban su, Muhammad Yusuf da Jami’an tsaro sukayi, da shekara 2 sai suka fara dauki dai-dai a Borno, tare kuma da tashin Boma-bamai. Yayin da su Mutanen Gwoza abin ya fara zuwa musu ne a shekara ta 2012, Wanda wani mai Suna Ibrahim Tada Ngleke ya jagiranci kungiyar. Yana bin gida-gida cikin dare, yana kuma daukan rayukan wanda ya zaba, da sunan aikin Allah yake. Musamman a wasu unguwanni na kudancin garin.
Kamar yadda wani bincike na nuna akalla mutane 10,000 ne suka rasa rayukan su a jihar Borno, saboda barkewar rikicin Boko Haram, wanda dubu 3 sune jimmillar mutanen da suka mutu a Gwoza.
Bayan barazanar kunhiyar a garin Gwoza, da kuma huduba da suka yi, har zuwa yanzu babu wanda yasan adadin mutanen da aka kashe. Amman wasu na cewa, lokacin da shugaban kungiyar na yanzu, wanda shine ya jagoranci karbe garin, bayan ya gama hudubar, mutanen sa sun fara ruwan wuta, tin daga karfe 4:30 na yamma a ranar Talata 5 ga watan Ogusta ta 2014, sai kusan 12:30 na dare suka daina harbi. Daman akwai manyan tsaunuka a garin, mutane sun gudu kan tsaunukan don tsira da rayukan su, Asubah na yi, kungiyar ta kira sallah, mutane sun dauka ai gari yayi lafiya, saboda sun ji kiran sallah daga masallacin Fadar Sarkin garin na Gwoza, wannan yasa suka sauko daga tsaunukan don komawa gidajen su. Suna isowa sai sukayi Alwala suka shiga masallaci, shigar su keda wuya, duk babu wanda ya fita da rai a cikin su.
Mutane da yawa yankar rago aka musu, wasu kuma yayin da suke barin garin ake sara su da sheber, ko adda, har sai sun mutu.
Wani dan kasuwa daga garin mai suna Bk, lokacin da yake hijira ya sanya kayan mata, yayin da ya kai shingen Boko Haram, sai suka gano shi na miji ne, suka sara shi, tun yana tsaye har ya kai kasa, wannan bidiyon na sara shi ya girgiza al’umma su sosai, domin yadda abin yazo da tausayi.
shin tayya akayi mutane suka yi hijira? Sannan me ya faru da su bayan hijira? Ta yaya aka fito da Sarkin Gwoza?
Shin bayan Sarki ya yi hijira ina ya wuce? Za mu yi bayanin su a mako mai zuwa insha Allah.

Exit mobile version