Kamar yadda na yi alkawari cikin ikon Allah ga shi na dawo domin cigaba da wannan rubutu da na fara wanda yake da alaka da shekarar da ta gaba da kuma wannan da muke cikin da fatan dai Allah yasa mun shigo a sa’a ya kuma hada mu da alhairan da ke cikinta ya yi mana iyaka da sharrin da ke cikinta Amin summa amin
Babu shakka kamar yadda kowa ya sani shekarar 2020 shekara ce wanda ba zata mantu ba, sannan shekarar ce mai bakin tarihi, a bangarori da dama, kai muna iya cewa babu bangaran da bai shaida shekarar da ta wu ce ba.
A satin da ya gabata mun dan taba bangaran ilimi inda shima kadan ta rage a yi jana’izarsa a wancan shekarar domin dai ya shiga wani irin mugun hali da yanayi tare da taimakon mara sa kishinsa kuma masu ci da gumin ilimi da sunan cewa shine abinda suka sanya gaba, eh muna iya cewa haka! Shine kuka sa gaba domin ganin bayansa, sai dai Allah yasa da sauran kwanansa gaba, gashi ya iso wannan shekarar 2021
Haka kaiwa gwamnatin Muhammadu Buhari ta hada kai da kungiyar ASUU suka fito da wata shegantaka ta yajin aikin wanda ya yi sanadiyar kowamar karatun miliyoyin dalibai baya, wannan abu da ban takaici da kuma ban haushi yake, tsakanin Buhari da ASUU babu wanda ya samun yadda yake so.
Saboda haka ne ma yanzu kowa ya rasa inda zai sa kansa, ganin irin barazanar da ke tafe daga wannan bangare da ya samu baban gimi wanda cike shi yana da matukar wahala a wannan shekarar.-
Ita kanta wannan gwamnatin wanda ta taimaka dari bisa dari wajan ganin an shiga matsala ta fara tunani a fanni noma, ta yi wani sabon tunani inda take cewa ya kamata ta bude kan iyakokin Najerya domin shigowa da abinci daga kasashen waje abinda aka yi kira ba adadi domin ta duba haka ta yi kunne uwar shego da kiraye-kirayen jama’a.
A tarihin kafuwar Najeriya shekarar 2020 ta zama daya tamkar da dubu, domin kowane bangare ta tabo saboda haka ta zama bakar shekarar a tsakanin al’umma, wannan yasa komi za a yi yanzu dole sai an tuna da ita, masu iya magana sun ce kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba. Amma yanzu abin ya koma kowa tuna bara…. Na bar jama’a su karasa da kansu.
Duk dai a shekarar da ta gabata ta 2020 fadar shugaban kasa ta ciri tuta wajan harzuka ‘yan Najeriya da aka bari matsalar tsaro ta galabaitar da su, suka shiga halin ni ‘ya su, sannan duk lokacin da wani abu na bakin ciki zai faru an shirya irin kalar maganar da za a jefawa jama’a wanda aka tabbatar da cewa ba zata yi masu dadi ba.
Akwai mutane guda uku da ake kallon sune suk kwarai wajan yin irin wadannan maganganun da ba su yi wa ‘yan Najeriya dadi ba a madadin fadar shugaban kasa wanda har gobe ba a taba jin an ce maganar da wane ya yi, ya yi ta akan kansa ba.
Kadda jama’a su manta daman shugaban kasa gashi ga yadda yake sai kuma gashi ya samu ‘yan bani na iya, wannan tasa suka sheka ayarsu a shekarar 2020 ta hanyar yin abinda suka ga dama, maganar shashi fadi kuwa, ko gizo da koki sun jinjina masu a shekarara da ta gabata.
Malam Garba Shehu shi ne kan gaba wajan yin bita da kulli ga mutanen da suka cancanci tausayawa da rarrashi kasancewra wani bala’ai ya faru da su, shima tuna yana gefe guda yana jiran umarnin kaiwa ya fadi abinda yake wanda ya tabbatar ba zai yi wa jama’a dadi ba.
Da akwai bukata da mun yi bitar wasu daga cikin manyan maganganun da su Garba Shehu da Lai Muhammad da Sa’adiya Faruk suka saki wanda yanzu akwai sauran birbishin ta a zukatan jama’a, mafi shahararn magangun a shekarar 2020 sun hada da batun mutane fiye da 100 da aka yi wa rankan rago a Zabarmari ta jihar Borno da kuma batun sace daliban sikandire ta Kankara da ke jihar Katsina.
Su Malam Lai Muhammadu sun kwarai wajan fadin cewa babu wata gwamnatin da ta yi abin azo a gani tun kafuwar Najeriya kamar ta shugaba Muhammadu Buhari, ya zama lamba daya wajan shirya shifcin gizo a shekarar 2020 da ta wuce, (Ana kiran Lamam Shafi’u) kuma ga alama sun fara sakin sabbi fil a wannan shekarar da muke neman tsari kadda kasance kamar 2020.
Haka kuma idan muka koma akan abinda ya shafi fafiyar da rayuwa yau da kullin a shekarar 2020 ne aka shaida karin kudin man fetur kusan sau biyar da karin kudin wutar lantarki da hauhauwar farahsin kayan abinci da kayan masarufi, wanda duk ya tuna da shekara 2020 sai ya ce kadda Allah Ya maimaita mana irin wannan shekara.
Tarihi ya nuna cewa rashin tausayi da imani irin na shugaban Buhari tasa duk lokacin da ya sha fura da Nono babu abinda zai biyo baya sai karin kudin wuta ko na man fetur, hatta kungiyar da ke shiga tsakani idan irin haka ta faru a shekarar 2020 aka yi jana’izarta wato kungiyar kwadago a idon duniya ta hanyar nuna mata bata isa ta yi wani abu akan wannan batutuwa. Ya salam.
Saboda yanzu duk abinda wannan gwamnati ta ga dama haka zata yi bata jin kira bata sauraran jama’arta musamman na arewa, duk abinda suka yi niyyar yi sai an yi, sai dai wadda duk za ayi ayi daga baya.
Idan ba a manta ba, a cikin shekarar da ta bata ne, ‘yan kudu suka kara nunawa duniya cewa sun san hakkinsu kuma sun san abinda suke yi saboda haka ba za su laminta da duk wani abu da ya ci karo da bukatarsu ba.
Kowa ya ga yadda suka bijiro da zanga-zangar #End of SARS kuma duniya ta shaida haka a shekara 2020 wanda hakan ke nuni da cewa an bar yankin arewa a baya so sai domin su ko wani abu kamar hakan ya gagare su da sunan neman hakki.
Anyi mamaki mutumin da baya sauraran kukan jama’ar da suka ba shi kuri’a ya samu darewa kan mulki amma sai gashi kasa da awa 24 ya jin gashi ya saurari masu zanga-zangar #End of SARS kuma har ya dauki mataki nan take, wannan batu da ban kunya yake, abinda wasu ke cewa kura da shan bugu gardi da kwace kudi, ‘yan arewa da bada kuri’a ‘yan kudu da cin moriya.
Idan Allah Ya kaimu sati mai zuwa zan cigaba da wannan rubutu kuma zan tabo wasu bangarorin daban–daban da ‘yan Najeriya ba su manta da su a cikin shekarar 2020 da ta gabata.
Na gode .