Wannan wata shekara ce wanda ba za a taba mantawa da ita ba, ta zo da abubuwa masu yawan gaske musamman wadanda suka tsayawa al’umma a cikin zuciya saboda radadinsu, da zafinsu da girmansu bisa wannan da ma wasu dalilai zai sa a cewa 2020 bakar shekara.
Babu shakka idan za a ce a tambayi mafiywan ‘yan Najeriya domin jin ra’ayinsu dangane da wannan shekara mai karewa, kuma a ba su dama su bayyana irin abubuwa da suka ci karo da su tun daga farkonta har zuwa karshenta za ji kuma za a ga abin mamaki daga garesu.
Ina mai bada tabbacin abubuwa da za aji suna da yawa kuma akwai darasi so sai a cikinsu, saboda lallai kamar yadda na ambata kowa yana da abin fada game da wannan shekara ko dai na dadi ko akasin haka.
Kar mu je da nisa farkon wannan shekara dai anyi abinda baya mantawa a zukata da wuri, domin kuwa ba a dade ba aka fara yi karin kumallo da batun yajin aikin kungiyar Malaman jami’’o’I wanda har yanzu abin bai zo karshe ba.
Masana dabi’ar dan Adam sun bayyana cewa zaman da dalibai suka yi a gida suna jiran komawar Malaman jami’a ya ba su damar canza tunaninsu wajan yin aikin da shi ta hanyar da bata da ce ba, saboda haka ne ma aka rika ganin yawaitar manya manyan laifufuka daga matasa ‘yan makaranta.
Haka kuma sun kara da cewa, iyaye su kan su sun hadu da wata irin fitina wanda irinta ta ce ta farko a cikin wannan karni na 21, sai da kowane uba ya gwamace dansa na makaranta saboda yadda al’amura suka canza a cikin wannan shekara ta 2020.
Ya zuwa yanzu dan Najeriya ya riga ya saba da wahalar gwamnatin Buhari amma anyi wani lokaci da ake mantawa da wannan bala’I da aka shiga saboda neman abin sawa a bakin salati, lalai abu ya kai abu a wannan shekara da muke ban kwana da ita ta 2020 inda wasu masu gidaje suka rika satar garin tuwo domin kaiwa iyalansu.
Ana cikin kukan targade sai kuma ga datsewar kafa domin sabun labarin bullar cutar annobar Korona tasa ana ganin kamar yajin aikin da Malaman jami’a suka tafe wani dan ba na shiga babar matsalar da har yanzu ba a fita ba, sai dai Addu’a maganin kowane irin bala’i
Lamarin bullar wannan cuta a kasashen irin su Chine ya sanya duniya ta shiga taitayinta na ganin wannan annoba bata tarwatsa ba cikin duniya, amma da yake Allah Allah ne, tun ana jin labarin abin a nesa sai gashi ya isa kowace jiha kowane garin kusan kowane gida, amma har yanzu ’yan Najeriya na ganin baba rodo ne kawai ake yi masu da wannan cuta.
Amma kadda a manta, bullar wannan cuta a Najeriya a wasu jahohi musamman na Arewa abu da har duniya ta nade ba za a taba mantawa da shi ba, musamman dokar zaman gida da gwamnatoci suka kakabawa talakawa a lokacin da suka bayyana cewa baban maganin wannan cuta sai an hada da zaman gida.
Sannan a dai dai wannan lokacin jama’a na cigaba da jin gashin kuma na gwamnatin shugaba Buhari saboda karewar tattali arzikin kasa da kuma duniya baki daya, kuma gashi a gefe guda jama’a na namen abin kaiwa a baki salati saboda tsananin kuncin rayuwa.
Wannan yanayi na cutar kurona har yanzu shi ne ake ciki duk wani abin kirki da ake son kaucewa, sai a makala rashin yin sa akan wannan cuta da mafiyan ‘yan Najeriya ke ganin baba rodo ne kawai ake yi masu da sunan wata cuta wai ita korona , amma dai sun ce karya fure take bata ‘ya ‘ya…
Haka kuma a dalilin wannan muguwar cuta da ta hade kai da wasu shuwagabanin Najeriya, wasu ma’aikata sun danda kodarsu domin an rika yi amfani da wannan matsala ana zaftare masu kudadan albashin domin wai a yaki wannan cuta.
Idan za aiya tunawa a wannan shekara ne duk musulmin duniya suka shaida wani sabon bala’I fil a leda wanda ya yi sanadiyar hana kowa zuwa aikin hajj domin sauke farali, batun da masa suka ce an dauki shekara aro-aro rabon da irin haka ta faru.
Saboda haka wannan shekarar ta 2020 ta zama bakar shekara a wajan Musulmin Duniya kai harda wadanda ba Musulmi domin kowa abin ya shafi shi, in banda ma su mulki, duk da suna jin tsoron mutuwa amma ba su iya tsira ba.
Idan muka koma akan batun matsalar tsaro kuwa sai dai mu ce Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’u.! wannan al’amari yafi yin kamari a cikin wannan shekarar da muke ciki, sannan idan Allah Yaso muke fatan ganin karshenta a jibi juma’a Insha’Allahu.
Alal hakika wannan shekarar 2020 ita ce shekara mafi zaman a zukatan ‘yan Najeriya da masu ji dadinta ba, kuma ba zata mantu ba, kuma za a dade ana jimaminta tare da rokon Allah kadda ya maimaita irinta a wannan duniya da muke ciki.
Yankin Arewa maso Gabas ya sha wuya iya wuya a wannan shekara kuma a hannun gwamnatin Buhari, sai dai lokacin ba zai bari ayi bayani dalla-dalla akan irin asarar rayuka da aka tafka a cikin wannan shekara ba, da kuma irin asarar dukiyoyi da masu tada kayar baya suka haddasa a wannan yanki ba.
Duk da irin karfin arzikin da Allah ya yi Najeriya da wannan yanki, sai da aka fada a yanayin karewar tattalin arziki saboda abubuwa da suke faruwa kuma har yanzu ba su tsaya ba.
Yanzu haka ina nan ina kokarin tattara bayanin irin asarar rayukar da aka yi kowane wata a cikin wannan shekara ta 2020 wanda Insha’Allahi nan gaba zan kawo su daya bayan daya da kuma irin manyan hare-hare da aka shaida a cikin wannan shekara da muke bankwana da ita.
Kazalika shima yankin arewa maso yamma ya ji jiki fiye da kowace shekara mutanen wannan yankin sun karda shugabanci Buhari, sun rasa komi na su saboda gazayar wannan gwmanati a fannin tsaro, sun yi kuka har sun gaji sun barwa Allah komi.
Duk dai a wannan shekarar 2020 mutanen wannan yanki musamman Katsina da Zamfara suka yanke kauna daga samun wani tagomashi daga bangaran tsaro wanda yanzu har ta kai sun fara tunanin yadda za su kare kansu daga masu tada kayar baya saboda jami’an tsaro sun kasa yin komi.