Daga Abubakar Abba, Kaduna
Tsohon Ministan Kudi lokacin Jamhuriya ta biyu, Alhaji Abubakar Alhaji,ya bayyana cewa Hukumar bada lamuni ( IMF), ta taba zuwa Nijeriyarancen kudi a shekarar 1974.Alhaji Abubakar ya bayyana hakan ne lokacin da Sanata Shehu Sani ya kai masa ziyarar ban girma a gidansa dake Jihar Sakkwato.Tshohon ministan yace,, da kansa ya sanya hannun yarjejeniyar badabashin lokacin yana a matsayin Babban Sakatare a ma’aikatar kudi tatarayya.
Alhaji, koda yake bai fadi yawan kudin ba, yace, “na yiwa Nijeriyakuka a kan yadda ta zama a yau.”Ya yi nuni da cewa, Allah ya albarkaci kasar nan da ma’adanai da dama,wadanda in anyi tattalin su, zasu kai kasar tudun mun tsira.Ya ce, a shekarar “1974 lokacin ina rike da mukamin Babban Sakatare,a ma’aikatar kudi ta tarayya, hukumar ta IMF ta zo ta same mu a kan tana neman a bata bashi.”
Alhaji ya ci gaba da cewa, “ Ni da kaina na rattaba hannu a kanyarjejeniyar ta bada bashin a madadn gwamnatin tarayya”.Yace, sai dai abin takaici, a yau kasar Nijeriya ta fada cikin karayartattalin arzikin kasa.Ya yi nuni da cewar dogaro a kan Man Fetur da Nijeriya ta yi kacokam,shine ya jefa ta cikin wannan matsalar.
Alhaji Abubakar ya kara yin nuni da cewa, baya ga Man Fetur da aikinnoma, kasar tana da Masana’antu da suke samarwa da kasar nan kudin shigana sashen waje.Ya nuna bacin ransa a kan yadda aka yi watsi da harkar noma da
masana’antu a kasar nan, don kawai ana ganin an samu Man Fetur, indakuma sai gashi harkar ta Man ta fadi war was. Alhaji ya yi nuni da cewa, jihohi talatin da shida da ake dasu a kasarsun yi yawa, kuma cike suke da zargin cin hanci da rashawa da ake yi masu, inda ya ce, kudaden da gwamnati ke kashewa suna da yawangaske.Ya yi nuni da cewar yawan jihohin da ake dasu da sai kuma karin yawancin hanci da rashawa ya karu.Ya ce, kamata ya yi a kasar ace ana da jihohi shida ne ko sha biyu.
A kan masu fafutukar yankin Biyafara kuwa, Abubakar ya ce, ya cekamata ya yi Nijeriya ta zamo a hade waje guda.Ya ce, “ba abin da yafi dace wa damu sai mu kasance kasa daya Al’ummadaya, inda yace, muna da albarkantu da idan an sarrafa su yadda yakamata kowa zai ji dadi.