Jaridar Guardian ta kasar Birtaniya ta wallafa wani bayani a shafinta na yanar gizo mai taken “Amurka tana cikin shekara da ta fi samun yawan mamata a tarihi”, bayanin ya ce, alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, yawan mutanen da za su mutu a Amurka a wannan shekara zai zarce miliyan 3.2. Karon farko da wannan adadi ya haura miliyan 3, kuma matakin da ya sa shekarar 2020 ta zama shekara mafi hadari ga Amurka da ta samun yawan mamata mafi yawa a tarihi, matsalar dake da alaka matuka da cutar COVID-19.
Ban da wannan kuma, jami’in cibiyar CDC ta Amurka Robert Anderson ya ce, yawan tsawon rayuwar jama’ar Amurka zai ragu da shekaru 3 duba da yadda yawan mamata yake da matukar yawa. (Amina Xu)