A jiya Juma’a ne shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari ya ce; Gwamnatinsa za ta yi aiki tukuru domin ‘farfado da karfafa fatan ‘yan Nijeriya ta fuskacin hadin kai da ci gaban Nijeriya.’
A jawabinsa na musamman kai tsaye ga ‘yan kasa dangane da sabuwar shekara, Muhammadu Buhari ya shaida cewar, shekarar 2020 da ta gabata a matsayin shekara mai dan karen wahala wadda ta jigata jama’a da aka wuce ta cikin wahala biso barkewar annobar Korona wacce ta yi illa ga fannoni daban-daban na rayuwar jama’a.
Kan hakan, Buhari ya baiwa ‘yan Nijeriya kwarin guiwa da sabon fata kan cewa a 2021 za su kara zage damtse domin tabbatar da farfado da ababen da suka kasance nakasu ne a 2020 domin ciyar da rayuwar jama’a gaba.
“Bisa yadda muka shaida, 2020 ta kasance mana mai tsananin wahala matuka, hakan ya nuna jajircewarmu da kokarinmu na mu rayu a kowane hali, sannan ta ba mu sabon babin daura fata na fuskantar duk wani kalubale da ke gabanmu a sabuwar shekarar 2021 da ma bayanta.”
Buhari ya ce; gwamnatinsa mai jin korafe-korafen jama’a ce, kuma a shirye suke su cimma dukkanin bukatun da masu zanga-zangar EndSARS suka gabatar domin kwalliya ta biya kudin sabulu lura da cewa sun fahimci “Mun fahimci cewa muna yi wa kasa fatan alkairi ne,”
Shugaban ya sha alwashin cewa kabulalen da suke akwai za su fuskanci himma da kwazon gwamnatinsa domin tabbatar da shawo kansu cikin kankanin lokaci tare da samar da tsare-tsaren da za su kawo sauki ga ‘yan kasa.
Ya tabo batun matasa, inda ya nanata kudurinsa wajen ganin ya kyautata rayuwar matasa da jawosu a jika domin taimakawa gami da karfafa musu guiwa domin gina matasan da za su kasance jagororin gobe tare tare da inganta fatan Nijeriya nan gaba.
Buhari ya nuna matasan Nijeriya a matsayin alkibla da fatansu a nan gaba don haka ya ce dole su tashi tsaye su kyautata musu rayuwa domin gobe ta yi kyau.
“A matsayinmu na gwamnati za mu kara himma da kokari wajen fito da tsare-tsare da shirye-shirye domin matasanmu.
“Kan hakan, za mu yi aikin hada da ‘yan majalisu domin bunkasa yanayin karfafawa da taimaka wa matasanmu domin kyautata musu rayuwa da daurasu bisa tafarkin daidai a sassa daban-daban na kasar nan.
“Hakan zai bada damar a samu guraben ayyukan yi, albarkatun noma, kasuwanci da kuma bunkasa masa’antu,” ya shaida.
Buhari ya ce tunin gwamnatinsa ta gano tare da yin nazarin cewa dole ne fa ta kara tashi tsaye kan matsalar tsaro, “Dole mu hanzarta kara zage damtsenmu da himma domin gabbatar da daukan matakan da suka dace don ganin aikace-aikacen ‘yan ta’adda bai kai ga zama ruwan dare ba.”
Kan bayaninsa ga kasashen makwafta da Afrika ta Yamma kuwa, ya shaida cewar bude iyakoki da Nijeriyan ta yi a baya-bayan nan na nuni da cewa a shirye take ta baiwa kasashen da ke sha’awar hada kasuwanci da ita damar gudanar da harkokin kasuwanci cikin gaskiya da adalci.
“Wasu daga cikin muhimman fannonin da za mu maida hankali a kai sun hada da: “sake karfafawa da sake maida hankali kan tsarin tsaronmu, kayan aiki da su kansu jami’an tsaronmu na soji da ‘yan sanda da nufin bunkasa karfin guiwarsu da himmarsu wajen ganin sun iya cimma nasara, waiwayen bada da sanya himma gaba domin tabbatar da dakile matsalar ‘yan ta’adda na ciki da na waje da suka addabi wasu yankunanmu.
“…. Gwamtinmu tana da cikakken masaniyar nauyin da ke kanta na tabbatar da mun kare rayuwa da dukiyar dukkanin ‘yan Nijeriya. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba dangane da fuskantar kalubalen tsaron da ke fuskantar kasarmu da kyautata rayuwar jama’a.
“Dangane da tattalin arzikinmu, mun maida hankali kan farfado da tsarin tattalin arzikin kasa ta hanyar ajandarmu na karfafa tattalin arzikin kasa da ke taimaka wa sashin wadatar da kasa da abinci. Wannan matakin zai taimaka mana wajen rage matsaloli da barazanar karancin abinci da ke akwai lura da irin matsatsin da aka shiga sakamakon kullen Korona watannin baya.
“A yanzu haka mu na nan muna cigaba da sake ginawa da kwaskwarima wa hanyoyinmu, layukan doguwa na jiragen kasa, gadoji, manyan hanyoyi na birane da karkara tare kuma da kyautata filayen jiragenmu.
“Sauye-sauyen da muke a fannin wutar lantarki zai tabbatar da burinmu na samun isasshiyar wutar Lantarki da mutane za su samu a gidajensu da masana’antu.
“Gwamnatinmu yanzu haka ta samar da shirye-shirye na musamman da aka tsara domin samar da ayyukan yi da taimakon matasanmu a fannin sana’o’i da dogaro da kai.
“A bisa bude iyakokinmu da muka yi a baya-bayan nan, muna sa ran bukatun da ake nema ta hanyoyin da suka dace da kuma cinikayya a tsakanin kasashen waje zai bunkasa tare da kyautata kananan sana’o’i da kananan kamfanoni dama wadanda suka dogara daga sashin kasuwanci da masana’antu a Nijeriya.”
A bangaren rashawa da cin hanci kuwa: Ya ce, yana daga cikin muhimman abun da gwamnatinsa ta sanya a gaba da dakile cin hanci da rashawa wanda ya ce, “Gwamnatinmu ta samu nasarori sosai wajen rage cin hanci da rashawa zuwa yanzu kuma a wannan shekarar, mun himmatu wajen cigaba da rage kaifin cin hanci da rashawa ta hanyar aikin hada da majalisar zana doka ta kasa.
“A yayin da muke aiki da majalisar dokokin kasa don tsara dokokin da za su karfafa yaki da cin hanci, za mu sa ido mu sabunta dokokinmu don tabbatar da cewa wannan yakin ya kara karfi sosai.