CRI Hausa" />

Shekarar Sa: Bikin Sabuwar Shekarar Sin Ya Yayata Fasaha Da Hadin Kai

Da misalin karfe 8 na daren jiya Alhamis bisa agogon birnin Beijing ne, aka fara gudanar da bikin sabuwar shekarar sa, ranar da ta kasance jajibirin bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta al’ummar Sinawa ta shekara 2021. Manazarta na ganin bikin na bana, ya nuna yadda kasar Sin na cimma nasarori masu yawa a fannin ci gaban fasaha, da hadin kan al’ummar ta.

Gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya watsa kasaitaccen bikin da ya samu matukar karbuwa irin sa na farko, inda ya yi amfani da fasahohin 8K Ultra HD, da AI+VR da 3D, don nuna bidiyon hotuna masu matukar burgewa. Bikin ya kuma kunshi shagulgula masu nuni ga kafuwar al’umma mai wadata a dukkanin fannoni, wadda ta yaki talauci, mai cike da burika, kana wadda ta cimma nasarar kandagarki da shawo kan annobar COVID-19.
Wasu alkaluman kididdiga sun nuna cewa, ya zuwa tsakar daren jiya, shirin kai tsaye da kafar CMG ta watsa, na bikin sabuwar shekarar kasar Sin, ya kai ga masu kallo biliyan 1.14. Cikin su har da masu amfani da sabbin kafofin watsa shirye shirye miliyan 569, da suka kalli bikin har karo biliyan 1.778, adadin da ya karu da mutum miliyan 548 bisa na shekarar da ta gabata.
Rahotanni sun bayyana cewa, masu kallon bikin kai tsaye ta kafar talabijin sun kai mutum miliyan 571, adadin da ya yi kusan daidai da na shekarar bara. Kaza lika, kafofin watsa labarai sama da 600, na sama da kasashe da yankuna 170 sun watsa wannan biki mai kayatarwa.
Kafofin dai sun hada da na Amurka, da Faransa, da Jamus, da Italy, da Rasha, da Japan, da Brazil, da Australia. Sauran sun kunshe na India, da Hadaddiyar daular Larabawa, da Malaysia da Afirka ta kudu.
Bugu da kari, yawan mutanen da suka kalli bikin a ketare kai tsaye ta kafar YouTube da Facebook, sun kai sama da miliyan 18.66. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version