Haruna Akarada" />

Shekarau Ya Kaddamar Da Aikin Sanya Fitilu A Kananan Hukumomin Kano 15

Kananan Hukumomin Kano

A makon da ya gaba ta ne Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya kaddamar da aikin sanya fitilu masu amfani da hasken rana a wasu mahimman wurare a Jihar Kano. Wannan Kaddamarwar an fara ne da Karamar Hukumar Nasarawa da ke cikin birnin, a mazabar Kaura Goje, bayan da aka gabatar da jawabai daga manyan baki.

A sibitin kwararrafa shi ne ya amfana da wannan fitila. Alhaji Haruna Gama shi ne babban bako mai jawabi a wajen, ya nuna farin ciki da kawo wannan aikin da Sanatan.

Ya ci gaba da cewa yayin kaddamar da wannan fitila tun da farko ya yi godiya ga Allah da ‘yan jam’iyyar APC da jama’ar mazabar Kaura Goje da ma’aikatan a sibitin da za a kafa wannan fitila. yana mai cewa mun fara da wannan guri ne domin su tabbatar da aikin na alheri wanda za’a sanya a kananan hukumomi 15 dake fadin jihar.

Ya kara da cewa sun yi godiya da farin ciki da wannan tare da mutanen wannan mazaba suka yi ya ce wannan sandan wuta za a kafa a mazabu 11 ko ina za a je a sa guda bayan kammala wannan taro mun sami tattaunawa da wasu daga cikin wanda su ke da ruwa da tsaki a taron. Musa Umar Faruk ,wanda ake cewa Oska daya ne daga cikin shugabannin asibitin kwararrafa da ke Karamar Hukumar Nasarawa Kwanar Jaba PRP, ya ce sun yi farin ciki da kawo wannan aikin sanya fitila, idan ka duba yanda a sibitin nan yake yana bukatar haske, dama akwai alkawarin da ya yi mana na gyara wannan a sibitin muna godiya.

Shi ma kwamared Jibirin Muhammad Nas shugaban a sibitin na PRP ya bayyana farin cikinsa da kawo wannan abin alkhairi ya yi kiraga a samar wa asibintin wuta ta domin akwai gadaje akalla guda a 20. Farin cikinsa na biyu shi ne, Mai Girma Malam Ibrahim Shekarau ya dau alkawarin gyara wannan asibitin shi ma Kabiru a yau kansila mai wakiltar mazabar gwagwarwa ya bayyana jin dadinsa da kawo wannan aikin mazabar gwawarwa ya ce, kowa ya san Mai Girma Sardaunan Kano jajirtacce ne a duk abin da ya samu zai kawowa mutanensa.

Exit mobile version