Connect with us

MANYAN LABARAI

Shekarau Zai Koma Jam’iyyar APC

Published

on

A yau Juma’a ciyaman din jam’iyyar APC mai mulki ya ziyarci jihar Kano don ganawa da Malam Ibrahim Shekarau wanda yake shirye-shiryen sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki tun bayan dawowar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso jam’iyyar ta PDP a kwanakin baya, dawowar Kwankwason ke da wuya sai rikicin cikin gida ya dabaibaye jam’iyyar, inda uwar jam’iyyar ta kasa ta rushe shugabannin kwamitin gundanarwar jam’iyyar na jihar Kano.

Shugaban jam’iyyar Adams Oshiomole ya samu rakiyar gwamnan jihar Kano Umar ganduje zuwa gidan tsohon gwamnan jihar Kanon wato Malam Ibrahim Shekarau, daruruwan magoya bayan ‘yan siyasar sun yi dafifi a wajen gidan Shekarau din don nuna goyon bayansu ga sauya shekar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: