Ranar 10 ga watan Janairun shekara ta 2011, ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona suka zama kan gaba a jerin wadanda zasu lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya wato Ballon d’Or.
Lionel Messi ne ya zama zakara a shekarar, ya yin da takwaransa Davi Hernandez dan kasar Sipaniya ya yi na biyu, sai daya dan uwan nasu, Andres Iniesta wanda shima dan Sipaniya ne ya yin na uku a shekarar.
A lokacin Barcelona tana kan ganiyarta ta lashe wasanni da kuma kofuna domin watanni shida tsakani ta lashe gasar cin kofin zakarun turai wato Champions League kuma na hudu a tarihin kungiyar.
A shekarar 2011, Messi da Davi da Iniesta ne suka mamaye kyautar Ballon d’Or ta gwarzon dan kwallon duniya kuma Messi ya fara lashe kyautar Ballon d’Or a shekarar 2009 da 2010 da 2011 da 2012 da kuma 2015.
Ranar Asabar Barcelona ta je ta casa Granada a wasan mako na 18 da ci 4-0 wasan da dan wasa Griezmann ya zura kwallaye biyu a raga sannan kaftin din kungiyar Messi shima ya zura kwallaye biyu a fafatawar.