Shekaru 20 Bayan Shigar Sin WTO Harajinta Ya Ragu Daga Kaso 15.3 Zuwa 7.4 Bisa Dari

A gobe Asabar ne kasar Sin ke bikin cika shekaru 20, da shiga kungiyar cinikayya ta duniya WTO a hukumance. Kuma wasu alkaluma da hukumar haraji ta kasar ta fitar, sun nuna yadda cikin wadannan shekaru 20, hukumomin kasar masu alaka da ayyukan haraji, suka himmatu wajen yin hadin gwiwa da takwarorin su na kasa da kasa, wanda hakan ya haifar da raguwar mizanin daukacin harajin kasar ta Sin, daga kaso 15.3 zuwa kaso 7.4 bisa dari, wanda ya gaza na da dama daga kasashe masu tasowa. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version