Connect with us

LABARAI

Shekaru 20 Ina Ciyar Da Masu Azumi Kyauta, Inji Fatima Abdullahi

Published

on

Wata baiwar Allah mai suna Hajiya Fatima Abdullahi wacce take jihar Bauchi ta bayyana cewar kawo wannan Ramadana din, yau shekaru kusan 20 kenan tana ciyar da ma’azumta wanda kuma a kowace shekara ta fi maida hankali ga taimakon marayu, marasa galihu da kuma almajiran domin basu abincin bude baki a wata mai alfarma domin dacewa da falalin da ke watan.

Hajiya Fatima Abdullahi ta bayyana cewar a wannan shekarar a kowace ranar Allah tana ciyar da mutane dubu daya 1,000 a kowace ranar tsawon kwanakin watan na ramadana.

Jarumar matar wacce ta bayyana wa wakilinmu cewar ita ta jima da tana bayar da gudunmawa amma bata taba shiga hidimar siyasa ba sai a wannan lokaci, tana mai bayanin cewar makasudin shigarta siyasa ya biyo bayan ziyarar da tsohon gwamnan Bauchi Malam Isa Yuguda ta taba kawo mata ne biyo bayan rasuwar mijinta a 2015, ta ce a bisa haka ne ta ga za ta iya taimaka masa wajen ci gaba da kokanin ganin ya samu nasarar neman kujerar Sanata da ya fito yi a wannan lokacin.

Kamar yadda ta shaida, Yuguda ya nada ta a matsayin shugaban matan tafiyarsa gidansa a halin yanzu, tana mai bayanin cewar irin wannan gudunmawar da take bayarwa a watan Ramadana na zuwa ne domin neman dacewa da ladar da ke cikin watar.

Ta ce, “Muna raba kayyakin shan ruwa ga marayu da almajiran hade da sauran wadanda suke da bukatuwa ne a cikin wannan watan na Ramadan domin dacewa da falolin kyautata wa masu bukata a cikin watan. Tabbas akwai dumbin lada ga ciyar da mai azumi, Manzon Allah ya ce “Duk wanda ya ciyar da mai Azumi zai samu kwatankwacin ladar Azumi a wannan ranar,’ don haka ne na rungumi wannan hanyar domin dacewa da alkairan da suke ciki,” In ji Hajiya Fatima.

Ta kara da cewa, “Bayan hakan, a kowace ranar Alhamis ina irin wannan tallafin da gudunmawar mijina a dukkanin mako muna wannan tallafin. Shekaru biyu da ta gabata ne na daina ciyarwa duk mako-mako. Bayan rasuwarsa a 2015 sai na ce ba zan dakata da wannan aikin alkairi da ya daura ni a kai ban a raba abinci ga mabukata da almajiran a kowace watan Ramadana. A halin da ake ciki, a wannan watan Ramadan din, kowace rana mutane dubu daya suna zuwa gidana su ci su sha a lokacin bude bakin Azumi,” In ji ta.

Ta bayyana cewar mata, maza, yara da kuma dattijai sune masu cin wannan gajiyar a kowace rana, ta kuma shaida cewar a kowace rana, da misalin karfe biyu na kowace ranar Ramadan din ne take fara rabon kayan shan ruwa.

Wasu daga dama da muka zanta da su a lokacin da suke amsar abincin bude bakin Azumi a Jiya, sun shaida mana cewar wannan gagarumar ci gaba ne, suna masu shaida cewar Allah ka kara yawan masu jin-kan jama’a irin su Fatima Abdullahi.

“Sunana Adamu Sani, ni dattijo ne da nake fama da kaina, tun ranar da aka fara shan ruwa a wannan watan na Ramadan, kullum a nan nake zuwa na ci na sha na bude baki. Allah ya saka wa Hajiya Fatima da alkairi,” In ji Adamu.

“Sunana Hajara Muhammad ni ‘yar gudun hijrace, a nan na ke amsar kayan shan ruwa na azumi kullum. Wallahi ban san da wace kalma zan nuna godiyata ba, na gode Allah cika mata dukkanin burinta na rayuwa,” A cewar masu samun tallafin.

Wasu Almajiran uku, Hamisu, Da Sani da kuma Muhammad Asiru sun nuna godiyarsu da wannan tallafin suna masu cewa “tana bamu abinci kala daban-daban, yau in ta bamu iri daban gobe ma sai ta bamu iri daba, kamar in yau muka samu kunu da shinkafa, gobe sai a bamu doya da kankana, kuma goshi nake yi sosai, na gode Allah saka da alkairi,” In ji su.

Hajiya Fatima Abdullahi dai tana wannan rabon ne a gidanta da ke unguwar Madina Kuarters a cikin garin Bauchi kowace ranar

 

 

 

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: