Mustapha Ibrahim" />

Shekaru 21 Da Dawowar Dimukuradiyya Akwai Yabo Da Kaico –Shugaban Matasan APC

Barandau

Hon. Sule Lawan Shuwaki shugaban matasa na Jamiyyar APC na kano ya bayyana cewa shekaru 21 da mulkin farar Hula ansamu cigaba a kasa dama nan kano musamman na gina Jamio’i 2 ga Gadojen karkashin kasa da na sama birjik a kano ga kuma ginin Asibitoci kamar na Giginyu da na Khalifa Sheikh Ishak Rabiu na Zoo Road da Gwamnan kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje ya kammala wadannan Asibitoci da dai sauran aiyuka da kano ta samu a shekarar 21, wannan abun yabo ne a cewar Shuwaki shugaban matasa APC na kano a yayin hira da manema labarai a kano a wannan makon da ya gabata.

Har ila yau ya ce haka kuma a matakin kasa ga aikin hanyar kano zuwa Barno ga na Abuja zuwa Kano ga daukar yan sanda dubu 10 ga tsarin bawa matasa aikin dogaro da kai na daukar doban matasa aikin yi da dai sauran ayuka a matakin kasa ga kuma aiyuka daban-daban na yaki da cin hanci da rashawa da kokarin kawo tsaro kasa duk da irin matsalolin da ake ciki a halin yanzu.

A karshe ya bayyana cewa idan akai laakari da irin matsalolin da ake ciki da wanda aka fuskanta daga jamiyyar PDP da ta shekara 16 tana mulki da kuma rashin katabus da ta yi a wasu wuraran abin ta kaici ne da kuma kaico a shekara 21 da kaiyi ana mulkin dumukkaradiyya a Najeriya duk da ya ke bamu kai irin shekara 200 ko sama ba anayi ta kamar yadda abin ya ke a kasashen Turai amma dai ansamu Alfanu mai yawa da abin kaico! a mulkin farar Hula na shekara 21 a Najeriya.

Exit mobile version