Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
A dai dai lokacin da jihar Katsina ke cika shekaru 30 da kirkira tuni an kammala shirye-shiryen yin bukukuwan ta hanyar bayyana wasu daga cikin irin cigaban da jihar ta samu tun daga lokacin da ake kirkirata ta fuskar kasuwanci musamman shekaru biyu na gwamnati mai ci yanzu
Kamar yadda tarihi ya nuna, a yau Asabar 23 ga watan Satumba 2017, jihar Katsina take cika shekaru 30 cif-cif, wanda hakan ya zo ne bayan shekaru biyar da yin murnar cika shekaru 25 da samun wannan jiha, wanda a baya an fuskanci kalubalan tsaro da dama wanda hakan ya taimaka wajan hana taka rawar gaban hantsi.
Sai dai kuma jihar Katsina ta samu wani tagomashi da za a iya cewa irinsa ne na farko tun bayan da ta samu jiha a shekrarar 1987, wanda ya sa ta yi wa sauran jihohin Nijeriya fintinkai ta fannoni da dama, sakamakon samun hazikin gwamna wanda ya ke zummar ciyar da jiha gaba watau Gwamna Aminu Bello Masari (Dallatun Katsina).
Jiha ta kara haskakwa ne lokacin da aka dawo turbar Dimokoradiya a shekarar 1999 zuwa yau, inda ta yi sa’ar samun shugaba wanda ya daga martabarta, ya kaita ga shiga tsare a idon duniya, tare da bugun kirji da irin abubuwan da ta samu na cigaba, sannan aka samu Gwamna Ibrahim Shehu Shema wanda shi ma ya dora daga inda ‘Yar’adua ya tsaya, to sai dai jiha ta samu wani irin cigaba a cikin karamin lokacin da gwamna Aminu Bello Masari ya karbi jagorancinta.
Ko tantama babu, gwamna Aminu Bello Masari ya karbi jagorancin Jihar Katsina a ranar 29 ta watan Mayu, 2015. Bai tsaya wata-wata ba ya dora harsashen gina jihar wanda a nan gaba za a yi alfahari da shi, sannan yana son ya bar abubuwan da mutanan Katsina da na kasa baki daya za su rika tunawa da shi ko bayan ya kammala wa’adin mulkinsa. Akan haka babu wanda ke da shakku duba da irin abubuwan da ya fara yi cikin kankanin lokacin da karbar mulkin.
A jihar Katsina tarihi ba zai taba mantawa da Shekarar 2017 ba, domin kuwa jihar ta cika shekara talatin da kirkira, wanda hakan ya bada wata dama ta cin gashin kanta, sannan ta cika shekaru goma cif-cif da wa’adin hazikin shugaba wanda ya yi mulkin tsawon shekaru takwas, watau Marigayi tsohun shugaban Kasa, Malam Umaru Musa ‘Yar’adua tun bayan dawowar turbar Dimukraddiya.
Tun daga lokacin da Malam Umaru Musa ‘Yar’adua da Ibrahim Shehu Shema da kuma gwamna mai ci yanzu, gwamna Aminu Bello Masari jihar Katsina ta samu cigaba marar musaltuwa, wanda yanzu ana iya nuna wasu abubuwan da jihar ta amfana da su ta fuskacin shugabancin wadanda suka gabata da suka hada da Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua da Filin sauka da tashi na jirage da babban filin wasa da Muhammadu Dikko da dai sauransu.
Idan muka dubu a bangaren gwamna Aminu Bello Masari kuwa ya zo da wasu abubuwa wadanda suka yi daidai da muradun jama’a na wannan karni na 21 lokacin da al’umma ke neman wanda zai tseratar da ita daga tudun mun tsira. Kwatsam sai ga kyakkyawar manufar nan ta Gwamna Masari ta sake fasalin da kuma dawo da martabar jihar Katsina a idon duniya (Restoration Agenda).
A cikin shekaru biyu kacal da ya yi yana shugabanci an samu gagarumin cigaban ta fuskacin Ilimi da harkar tsaro da Noma da kiwon lafiya tare da inganta rayuwar jama’a ta bangaren bunkasa tattalin arziki jihar Katsina zuwa wani babban mataki.
Kazalika akwai wasu bangarori wadanda idan a ka yi duba za a ga cewa jihar Katsina ta sha kwana a karkashin shugaban Gwamna Aminu Bello Masari, misali harkar noma wanda aka canza fasalinsa zuwa na zamani tare da bullo da sabbin hanyoyin da za a amfana da shi fiye dacan baya.
Haka kuma babu wani mai musun cewa harkar ilimi a Katsina ba ta matsa daga inda take ba ganin cewa wannan bangaren ne gwamna Aminu Bello Masari ya fi maida hankali akan shi. Abubuwan da bangaren harkar kiwon lafiya ya samu a wannan gwamnatin ido ba zai iya ganisa ba, haka ma kunne ba zai iya jin sa ba.
Muna da misalin irin yadda aka canza fasalin asibitocinmu wadanda ada sun koma kamar makabarta, hatta jama’ar kauye na tsoron zuwa cikin su amma yanzu sai dai Allah sam barka. Gyaran Asibitocin Katsina da Daura da kuma Funtua da kuma Kankia sun isa mai hankali ya gane cewa harkar kiwon lafiya a jihar Katsina, ba a yi mata rikon sakainar kashi ba.
Kafin zuwa wannan gwamnati asibitocinmu da kuma harkar kiwon lafiya a jihar Katsina suna cikin halin ni ‘ya su, saboda yadda suka rasa duk taimakon da ya kamata a ba bangaren kiwon lafiya da suka hada da kayan aiki da magunguna da kuma ma’aikatan lafiya, uwa uba lalacewar asibitocin da wuraran amsar magani.
Wannan yasa ba dare ba rana gwamna Aminu Bello Masari ya dukufa wajan ganin wadannan wurare sun dawo cikin hayyacinsu, ta yadda jama’a za su Amfana da rumon dimokoradiya, bayan da ya kaddamar aikin sake masu fasalinsu na din din din.
Baya ga sake fasalin asibitocin jihar da maida su na zamani tare da samar da sabbin gine-gine, a farkon wannan shekarar da muke ciki, gwamna Aminu Bello Masari ya ware miliyoyin nairori domin sayan kayayyakin aikin na zamani, da za a sa asibitocinmu, ga kuma daukar ma’aikatan lafiya mutun 600 da aka yi wadanda za su rika aiki sa’o’I ashirin da hudu a dukkanin asibitocin da ake da su a fadin jihar Katsina.
A cigaba da ba bangaren kiwon lafiya mahimmacin wannan gwamnatin ya kara inganta yanayin karatu a makarantar koyon aikin jinya da ke Katsina, inda ya kara yawon daliban da ake dauka duk shekara daga 50 zuwa 100 domin fadada wannan fanni da ba wasu damar yin karatu kiwon kafiya, wanda haka ya zama na farko a tarihin jihar Katsina.
Wani abin burgewa da kuma jinjiwa shi ne, gwamna Aminu Bello Masari ya kudiri aniyar samar da asibitin koyarwa mallakar gwamnatin jiha, inda yanzu haka magana ta yi nisa kuma ana sa ran kashe kimanin naira miliyan dubu daya da miliyan dari uku sannan ga wani tallafi da bankin cigaban Musulunci zai bada wani rance na dalar Amurka $110 domin kara inganta asibitocin a karkara.
Duk dai a wannan bangaren na kiwon lafiya, inda wannan gwamnatin ta fara sake fasali da kuma daga darajar wasu asibitoci da suka hada da na Musawa da Jibia da Malumfashi da kuma na Dutsinma domin a tabbtar da bada ingantancen yanayi da zai zama dai dai tsarin kiwon lafiya, wanda zai taimakawa mata masu juna biyu da kuma kananan yara.
Jajircewar wannan gwamnatin yasa duk da irin karancin kudin da take fama da shi, amma tana iyakar kokarinta na ganin ta samar da isasun kudade ga ma’aikatar lafiya domin samar da magunguna ga asibitoci da kuma cibiyon shan magani wanda kuma babu wanda ke musun haka.
A bangaren Ilimi kuwa kai ka ce abinda wannan gwamnatin ta zo yi ke nan, domin tun zuwansu gwamna Aminu Bello Masari ya sha alwashin sake fasalin yadda harkar ilimi take tafiya a wannan jiha ta Katsina, ganin cewa jihar Katsina ce jiha ta farko da take da kwalejin Ilimi da manyan shuwagabani suka halarta a shekarun baya.
A kan haka ne, gwamnati ta shirya cewa maganar Ilimi bata da ta biyu, a karkashin jagoranci Aminu Bello Masari, inda bai wani bata lokacin ba wajen sake tsari da kuma yanayin da ake karatu a jihar Katsina, inda ya canza shi baki daya domin a cewarsa ta haka ne kadai za a iya bambanta da wadanda suka yi wa harka ilimi rikon sakainar kashi a baya.
Wannan fa yana cikin alkawarin da wannan gwamnati ta dauka a lokacin yakin neman zabe inda ta ce sauya fasalin ilimi da bada ingantace ilimi da gyara makarantu da daukaka darajarsu da samar da kayan aiki na daga cikin abubuwan da za su lamushe makudan kudade idan har suka samu nasarar darewa karagar mulki.
An zo wajen, idan ana maganar Ruwan sha, gwamna Aminu Bello Masari kwarare ne a wannan fanni, saboda haka ma yake jin matsalar ruwa kodayaushe a cikin ransa, matsalar Ruwan sha a jihar Katsina ta kai matuka tun daga lokacin da aka kirkiri jihar Katsina, matatun ruwa suna aiki ne a kasa da kashi 50 na ainahin aikin da ya kamata su yi saboda kayayyakin matatun Ruwan sune har yanzu.
Sannu a hankali, yanayin aikin matatun ruwa sai da ya kuma yana aikin kasa da kashi 10, a ya yin da yake iya samar da ruwa lita 120 a rana. Fiye da wuraran samar da ruwa na musamman 41 da daya da ake da su a sassa daban-daban amma dukkansu ba sa iya aikin da ya kai kashi 20 sannan sauran kuma basa aiki kwata-kwata.
Sai da matatar ruwa ta garin Daura ta daina aiki baki daya, fiye da shekaru hudu, matatar ruwa ta Malumfashi ta daina aiki fiye da shekaru bakwai. Matatar ruwa ta Ajiya tana samar da kashi 60 cikin 100 na abinda ya kamata a samu, a ya yin da matatar ruwa ta Jibiya da Dutsinma suka koma yin aiki na sa’o’I shida zuwa takwas a rana saboda wani lokacin akwai matsalar hasken wutar lantarki..
Daukar matakin gaggawa da gwamna Masari ya yi wa harka ruwa ta sa an dauki matakin gyara matatan ruwa ta garin Daura mahaifar shugaba Muhammadu Buhari a shekarar farko ta mulkinsa (2015) wanda yanzu haka sun fara amfani wannan gyara. Haka kuma matatar ruwa ta Malunfashi wanda ta daina aiki tun shekarar2009 an ware mata naira miliyan 141 wanda yanzu haka sun fara amfani da matatar ruwa a watan Mayu na wannan shekarar 2016
Babbar matsalar ruwa da ta addabi birnin Katsina sakamakon rashin yin aiki da Babbar madatsar ruwa ta Ajiwa ta fuskanta, yanzu haka matatar ruwan na cikin wani gyara da ba a tabayin iris ba tun kafa wannan matatar ruwa, ta kuma lashe kimanin naira miliyan dubu daya da miliyan dari tara wanda idan aka kamala zai bada lita 50,000 a rana.
Kamar yadda aka bayyana a baya samar da tsaftatacen kuma wadataccen ruwa a Katsina na daya daga cikin kudurorin wannan gwamnati, hakan ya sa a kasafin kudi na shekarar 2017 aka ware kudi naira miliyan dubu sha hudu domin a fuskanci wannan matsala wanda yanzu ana ganin amfaninta.
A kokarinsa na ganin an kara inganta rayuwar mutanen Katsina gwamna Aminu Bello Masari ya cigaba da ayyukan hanyar da ya gada daga tsohuwar gwamnatin da shude inda yanzu haka yake gab da kammala su, kuma ya ware kudi har naira miliyan dubu sha biyar domin yin wadannan ayyuka da suka shafi ko’ina a Katsina.
Gatan da bangaren noma ya samu a karkashin jagoranci gwamna Aminu Bello Masari abin ba a magana, ganin yadda aka ware kudi har naira miliyan dubu uku da, miliyan dari biyar domin sayan takin zamani domin a daukaka darajar noma a jihar Katsina wanda yanzu ana gani a kasa
Masana sun tabbatar da cewa hanyar da wannan gwamnatin ta dauko na yin gyara da daukaka darajar asibitoci a wannan jihar ya zo akan daidai kuma haka ya kamata tun asali.
Magana ta karshe yanzu a jihar Katsina, kowa ya aminta da cewa gwamna Aminu Bello Masari ya zo ne da zummar daukaka darajar mutanan Katsina da kuma jihar baki daya, ta kowane bangare. Abin jira a gani shi ne irin sabbin tsare-tsare da wannan gwamnati ta ke tafe da su a shekara mai zuwa. Allah raya jihar Katsina.