Ranar Lahadi ne Maulanmu Sheikh Ibrahim Niass ya cika shekaru 45 da rasuwa, wato ranar 26 ga Yuli, 1975, Maulanmu Sheikh Ibrahim Niass ya koma ga mahalincinsa. Ya tara almajirai miliyan takwas a fadin duniya tun ya na raye. Tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu kullum almajiransa karuwa su ke yi. Ya yi yawo kasa da kasa a duniya, domin yada addinin Musulunci.
Shi kadai ne malami da ya musuluntar da mutum 4,000 a rana daya. Shi ne bakin mutum na farko da ya amsa fatawa kuma ya jagoranci sallar Juma’a a shahararriyar Jami’ar nan ta addinin Musulunci da ta ke Misra (Egypt). Shi ne malamin Musulunci da ya kai Musulunci a fadar Paparoma ta Batican lokachin Pope Giobanni Cardinal Montini, Paul B1(1963-1978).
Shi ne malamin da ya yi wa Shugaban China, watau Mao Zedong, tayin shiga Musulunci, amma babu rabo. Don haka bai karbi Musulunci ba, domin shi ya riga ya yi imani da Karl Mard. Duk da haka ya yarda cewa, Annabi (SAW) ya yi kokari wajen ceto bil adama daga zalunci. Kuma Shehu ya nemi alfarma da Mao ya ba shi izini ya kai ziyara kabarin Sahabin Annabi (SAW), watau Sa’ad bin bi Wakas (RT) a Canton. Mao ya ba wa Shehu izini ya kai ziyara kabarin Sa’ad bin Abi Wakas a canton din.
Haka Shehu ya kai ziyara zuwa tsohuwar Tarayar Sobiet lokacin a na tsakiyar muzguwa masu addinin Musulunci da Kiristoci. Shugaban Sobiet na lokacin, Nikita Khrushcheb, ya yi maraba da Shehu kuma ya ba shi izinin kai ziyara masallancin Imam Bukhari da ke Bukhara a Uzbekistan.
Sarkin Saudi Arebiya, watau Sarki Faisal, ya nada Shehu daya daga cikin majalisar manyan malaman duniya, watau Rabi’atu Alami da ke Jeddah, domin Shehu ne ya ba da shawara cewa, yakamata a kafa majalisar malamai na Musulunci da za su tattauna abin da ya shafi Musulmin duniya.
A nahiyarmu ta Africa, Shehu ya taka mahimmiyar rawa ga addinin Musulunci. Shugaban Gold Coast (Ghana a yanzu), Kwame Nkrumah, ya girmama Shehu da ba shi izini wajen yada addinin Musulunci a Ghana duk da cewa shi ba Musulmi ba ne. A kasarmu Nijeriya, zamanin Janar Yakubu Gawon, lokacin yakin basasa (1967-1970). Janar Gawon ya nemi Shehu ya taimaka wa Nijeria da addu’ar Allah Ya ba wa sojojin Nijeriya sa’a duk da cewa ba Musulme ba ne. Allah Ya karbi addu’ar Shehu; Igbo su ka mika kai.
Shehu ya ziyarci kasashe kimanin 75, domin abubuwa hudu:
1- Yada addinin Musulunci a duniya.
2- Tsarkake zukatun Musulmi da zikiri, domin nuna mahimmancin zikiri, watau ambaton Allah a koda yaushe.
3- Sanya tsantsar soyayyar Annabi (SAW).
4- Muhimmancin haddar karatun Alkur’ani da aiki da shi da neman ilimin addinin Musulunci.
Wannan shi ya sa almajiransa su ke shuhura a fannin addinin Musulunci daban da daban. Ko a Nijeriya akwai manyan almajiransa, kamar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a kan tafsiri Alkur’ani, wanda a yanzu a Nijeriya ba tafsirin da ya ke tara mutane, musamman lokachin rufe shi a dandalin Murtala da ke garin Kaduna a duk watan Ramanda, kamar wannan, Sheikh Sharif Ibrahim Sale Maiduguri, Shugaban Majalisar Koli ta Fatawar Malaman Nijeriya kuma mamba a Rabi’atul al-alami da ke Jeddah a Saudiyya da Sheikh Tijjani Bin Usman ’Yanmota a Kano.
Akwai kuma su Sheikh Atiku Abubakar Sanka, Sheikh Ibrahim Mushadudi Jos, Sheikh Yahuza Zaria, Sheikh Abubakar alfulty Jos, Sheikh Gbirima Nguru, Sheikh Mahiru Rabi’u Dantinki Baba, Khalifa Isiyaku Rabiu, Abulfahi Maiduguri, Sheikh Al-Muskiyn Maiduguri, Sheikh Balarabe Gusau da dai sauransu.
Sheikh Sharif Ibrahim Sale Maiduguri a yau a duniya an yarda kusan babu masanin hadisi kamarsa. Saboda haka ya ke da kujera a Rabi’atul Al-Alamiyah ta Saudi Arebiya.
A karshe, Allah Ya saka wa Sheikh Ibrahim Niass (RT), ya kuma gafarta ma sa, domin Rasulurrahmati, sallallahu alayhi wa salim.
An dauko wannan bayanin ne daga Zauren Tarihi na WhatsApp.