Haruna Akarada" />

Shekaru 59 Babu Abinda Arewa Ta Samu Face Koma-baya -Hanga

A ranar Talata, 1 ga Oktoba, 2019, ne Nijeriya ta cika shekaru 59 da samun yancin kai. Masana da sauran ‘yan mazan jiya sun bayyana ra’ayoyinsu akan wannan biki da kuma murna da wannan kasa yi a halin yanzu na samun wannan ‘yanci na kai.

Wannan dalili ne ya sa wakilin LEADERSHIP A Yau, HARUNA AKARADA, ya gana da wasu daga cikin gogaggun mutane wadanda su ka ga jiya su ka ga yau, domin jin ta bakinsu musamman wajen fayyace gaskiya komai dacinta, inda mu ka yi katarin samun ganawa da SANATA RUFA’I SANI HANGA, wanda sanin kowa ne cewa tsohon dan gwagwarmaya ne, wanda ya saba kalubalantar rashin gaskiya ko dai a jiha ko kuma a Tarayya. Ga dai yadda hirar ta kasance:

Mai girma Sanata, ga shi locaci ya sake zagayowa na cikar kasar nan shekaru hamsin da tara da samun ‘yancin kai, ko akwai wani cigaba da aka samu daga wajen Shuwagabaninmu na Arewa?

To, gaskiya sai dai kawai mu yi wa Allah (SWT) godiya, domin kuwa za mu iya cewa an samu canje-canje da dama musamman idan muka dubi irin abubuwa na zamani da aka samu a halin yanzu. Duk dai da cewa, akwai wasu kasashe wadanda suka samu wannan ‘yanci tare da kasarmu Nijeriya a lokaci guda, wanda idan ka kwatanta su da mu, za ka samu tuni sun yi mana nisa ko fintinkau ta bangaren cigaba.

Saboda haka ni a nawa ganin shi ne, yadda Shugabanninsu suke tafiyar da abubuwan nasu kasashen, ba haka namu Shugabannin suke tafiyar da su ba. Wato magana ta gaskiya ita ce, ko kadan ba mu yi sa’ar Shugabannin ba, domin kuwa babu wata rawar gani da suka yi akan wannan kasa tamu ko kuma wannan bangare namu na Arewa. Idan muka dubi Shugabannin Kudu, sun fi gina nasu bangaren fiye da namu na Arewa, idan kasa mutum a gaba babu wani abin a zo a gani da zai iya nuna maka wannan yanki namu naArewa, amma idan Ka je Legas da sauran kasashen Yarbawa; za ka tarar da irin cigaban da suka samu. Bayanan da ake samu a halin yanzu shi ne, a duk fadin yankunan Afirka Legas ce ta hudu a karfin tattalin arziki, ka ga kuwa ai dole ne mu yi hawaye, duk da cewa dai Jihar Kano babu laifi, amma dai ba haka aka so ba.

Sanata, a lokacin da su Sir Ahmadu Sardaunan Sokoto suka yi gwagwarmayar samun ‘yanci a wannan kasa, sun yi bakin kokarinsu wajen ganin kasar ta tafi dai-dai-wa-daida, amma sakamakon abubuwan da suka faru al’amura suka lalace, me ka fuskanta a wancan locacin?

A lokacin su Sardauna, ai Arewa ta fi ko’ina karfi a kasar nan, tare da karfin tattalin arziki, domin kuwa arzikin da muke da shi ko alama babu shi a Kudu, a takaice ma a wancan lokacin mu ne muke ciyar da yankin Kudun bakidaya da wannan arzikin da Allah Ya ba mu. Sannan ina so a fahimci cewa, hatta da Man Fetir din da aka hako da dukiyarmu aka yi amfani, amma abin takaici bayan an hako Man, sai aka zo ana yi mana gorin cewa wai cima zaune ne mu.

Har ila yau, a wadannan yankuna namu; binkice ya kara gano cewa mu ma muna da wannan Mai na Fetir, amma har yanzu babu wani shiri na sake hako shi sai yanzu ne ma ake kokarin maganar yadda za a hako shi din, sannan Man da muke da shi ai ya fi na ‘yan Kudu, ma’ana wanda muke da shi a Jihohin Barno da Bauchi. Sannan muna zargin cewa wannan ne yasa aka haddasa mana rigingimu a yankinmu na Arewa, ta yadda babu wani abun arziki da zai gudana.

Abu na biyu shi ne, tun a lokacin da su Sardauna suka zo muna da arzikin gwala-gwalai da duwatsu kala-kala, wanda za ka samu cewa wata kasar idan tana da guda daya kacal ya ishe ta gudanar da harkokinta kacokan. Da a ce tuni an mayar da hankali akan wadannan kadai, da kasashen da za mu yiwa fintinkau ba za su kirgu ba. Idan ka duba ire-iren wadannan kasashe za ka samu watakila abu guda daya kacal na ire-iren wadannan ma’adanai take da su ko ta dogara a kai, amma ta cigaba, mu duk muna da su amma mun je mun taru a wajen mai.

Jihar Kano a halin yanzu ta yi katarin samu Babban Ministan Gona na fadin kasar nan, ko akwai wata shawara da za ka ba shi musamman wajen sake habaka harkokin noma a wannan kasa?

Wato magana ta gaskiya ita ce, wannan maganar noma idan har da gaske ake yin ta, ana kuma so a farfado da ita, wajibi ne a fara gyara harkar da aka kawo na yadda za a yi a taimakawa manoma, domin kuwa ko shakka babu harkar abinci ta fi harkar Mai kawo kudi tare da bunkasa tattalin arzikin kasa. Abinda yasa n ace haka shi ne, mafi yawan kudaden da ake warewa domin taimakawa wadannan manoma, wawashe su ake yi; ma’ana hannun dama ne yake mikawa na hagu kuma yana kwashewa.

Wannan dalili ne yasa na kira lambar wannan Minista na gona, domin na ba shi shawarwari amma kuma wayarsa a kashe, to yaya za a baka shawara. Amma duk da haka yanzu ma zan ba da wata shawarar daga nan, domin kuwa wadannan kungiyoyi guda biyu gaskiya sun yi kadan, kamata ya yi a fadada su domin Arewa na da fadi.

Duk da cewa yanzu haka shekaru hamsin da tara kenan da samun ‘yanci a wannan kasa, amma kusan kullum abubuwa sai faman kwan-gaba-kwan-baya suke yi, wace shawara za ka baiwa gwamnatoci, musamman na yankunan Arewa don ganin wadannan al’amura sun gyaru?

Babbar hanya dai ita ce, hanyar noman nan wato bayar da tallafin noma ta hanyoyin da suka dace tare da sanya idanu da kuma jajircewa don tabbatar da ganin abubuwan sun tafi yadda ya kamata. Sannan ina sake jaddada cewa, wadannan kungiyoyi guda biyu masu bayar da wannan tallafu sun yi kadan, wajibi ne a kara su.

Kazalika, akwai wasu wadanda ba a nema ba, to gaskiya a kyautu a neme su domin akwai wadanda suke tare da al’umma; sannan idan aka ba su wannan tallafi na noma za su yi bakin kokarinsu su ma a nasa bangaren. Amma yanzu wadannan kungiyoyin guda biyu karya ne ba su wadata ba ko kadan, illa kawai dai hannun dama ne yake mika wa na hagu kuma yake karba, ina da cikakkiyar hujjar fadin haka.

Mutane da daman a zargin cewa akwai bata gari cikin wannan gwamnati, wadanda suke aikata abinda ransu ke so, yaya kake kallon ire-iren wadannan zarge-zarge?

A gaskiya dai akwai matsala, domin kuwa a kodayaushe za ka ji ana cewa, wani ya sace makudan kudi, amma sai ka ji shiru babu wani abinda ya faru. Ko shakka babu, wannan ba karamar matsala ba ce, sai dai kawai ni tawa shawarar a nan ita ce, duk wanda aka samu da aikata irin wannan laifi a hukunta shin an take ba tare da wani bata lokaci ba, ma’ana kawai a yi ba sani ba sabo; sannan kuma sauran a rubuta musu takarda kowa abinda ya ci ya dawo da shi, ina ganin idan aka yi haka mutane za su samu sauki sosai.

A karshe, yaya Sanata yake kallon salon mulkin da da kuma na yanzu?

Gaskiya maganar da ake yi yanzu abubuwa sun canja kwata-kwata, a sanina na da Ma’aikatan Gwamnati babu ruwansu da Kwangila, amma yanzu duk wani Ma’aikacin Gwamnati shi ne dan Kwangila sun tare komai, kuma wannan ba daidai ba ne, domin komai akwai gurbinsa.

Yanzu haka Abuja, duk wasu manya-manyan gidaje da ka gani na manyan Sakatarorin gwamnati ne, a cikinsu  akwai mai gida hamsin; akwai mai sama da haka, haka nanDaraktoci su ma akwai mai gida talatin, sai masu gidaje dari kuma su ne suka fi kowa kudi, amma sai a ce iya ‘yan siyasa kadai ne da gwamnoni barayi. Muna da hujjoji, sannan ko a lokacinmu ana ba da Kwangila, amma lis ake yi da manya da kanana kowanne a sammasa, komai kankantarsa  kuwa, sannan duk dan Kwangilar day a yi aiki mai kyau, sai a sake kara ma sa.

Exit mobile version