Shen Haixiong: Ya Kamata A Mai Da Hankali Kan Matsayin Sabbin Kasashe Masu Saurin Bunkasuwa Da Na Masu Tasowa

Shen Haixiong, Shugaban babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG ya yi kira ga kafofin watsa labarai na kasa da kasa da su mai da hankali kan watsa labaran da suka shafi matsayin sabbin kasashe masu saurin bunkasuwa da masu tasowa, a kokarin samar da dandali ga cudanyar al’adu daban daban.

Mr. Shen ya fadi hakan ne da yammacin jiya Litinin 5 ga wata, yayin taron dandalin tattaunawa tsakanin kafofin watsa labarai da masana masu ba da shawarwarin da ke da nasaba da batun tattalin arziki da sha’anin kudi na kasa da kasa na Hongqiao da aka yi a birnin Shanghai.

Mr. Shen ya kuma kara da cewa, dole ne labaran da ake watsawa kowace rana su shafi lamuran da ke faruwa yanzu. Dalilin da ya sa kafofin watsa labarai da jama’ar kasa da kasa suka dora matukar muhimmanci kan bikin CIIE da ake yi a birnin Shanghai da ma ra’ayoyin kasar Sin, shi ne, sabo da ra’ayin goyon bayan manufar kasancewar bangarori da dama da yin cinikayya cikin ’yanci ra’ayi ne da ya samu amincewa daga yawancin kasashen duniya.

Bugu da kari Mr. Shen ya ce, babu wanda zai iya hana ci gaban zamani. A matsayin ’yan jarida, tsayawa tsayin daka kan dunkulewar tattalin arzikin duniya guri guda, da ma kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya cikin adalci nauyi ne da ke sauke a wuyansu.

Game da yanayin da ake ciki yanzu, wato yadda wasu kasashe ke  adawa da manufar habaka cudanyar tattalin arzikin duniya, ko kuma kalubalen da ake fuskanta a wannan fannin, shugaba Shen Haixiong yana ganin cewa, kamata ya yi kafofin watsa labarai su yi hakuri da juna, domin gujewa adawa da juna, tare kuma da samar da wani muhallin jin ra’ayin jama’a, domin cimma matsaya guda yayin da ake amincewa ko biyayya ko kawar da bambancin juna, inda ya ce da haka za a kara sanya sabon karfi kan ci gaban tattalin arzikin duniya. Shen ya jaddada cewa, kamata ya yi kafofin watsa labarai na kasashe daban daban su yi kokarin kiyaye tsarin tattalin arziki ba tare da wata rufa rufa ba, haka kuma su sa kaimi kan cudanyar dake tsakanin sassan da abin ya shafa, yana mai cewa, muddin aka nace ga manufar raya tattalin arizkin duniya mai cin moriyar juna, to za a kafa tsarin tattalin arzikin duniya mai adalci da daidaito.

Har ila yau, Shen Haixiong ya gabatar da ra’ayinsa game da yadda ba a watsa ra’ayoyin kasashe masu tasowa kan harkokin kasa da kasa yadda ya kamata, inda ya bayyana cewa, ya kamata kafofin watsa labarai su taka rawa wajen cudanyar dake tsakanin wayewar kai daban daban, sannan ya dace su yi biyayya ga matsaya da ra’ayi daban daban, haka kuma su kasance gada dake tsakanin sassa daban daban, ta yadda za a raya aikin gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya lami lafiya. (Masu Fassarawa: Kande Gao, Jamila Zhou, ma’aikatan sashen Hausa na CRI)

Exit mobile version