Daga Abubakar Abba, Kaduna
Shugaban gamayyar kungiyoyin matasan Arewa (CNG), Alhaji Shettima Yerima, ya ja kunnen gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai, ya na mai cewa hawainiyarsa ta kiyayi matasan Arewa, inda bayyana cewar, ya na wasa da wuta ne a kan cewar da ya yi a cafko ’ya’yan kungiyar da su ka baiwa ‘yan kabilar Igbo wa’adin daya ga watan Oktobar shekarar 2017 su gaggautawa ficewa daga yankin Arewa.
Yerima, wanda ya na maida martani ne a kan takardar da gwamnan ya ce ya karbo daga kotu don cafko su, ya ce, yunkurin na gwamnan ya nuna a zahiri shi makiyin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne.
Ya ce, kodayake kungiyar ba ta son yin wata jayayya da gwamnan, domin a yanzu abin da ke gabanta shi ne ganin an gina kasar nan. “Watakila gwaman yana kokarin karkatar da hankalin gwamnati ne, mu kuma ba za mu yarda da a yi amfani da mu ba wajen hakan,” in ji shi.
Game da batun kamo su kuwa, Shugaban kungiyar cewa ya yi “ba a ba mu sammaci ba, kuma in an ba mu za mu gurfana, domin kuwa ba mu fi karfin doka ba.”
Ya yi ikirarin cewa, “ba inda za mu gudu saboda barazanar El-Rufai, domin mu ba matsorata ba ne. ‘Yan kasar nan su ne za su yi alkalanci don gano ko el-rufai dan kasar nan ne na asali, kuma mai son zaman lafiya a kasar nan?”
Da a ka tambaye shi akan sanarwar da Atoni Janar na kasa, Abubakar Malami ya fitar kwanan baya, inda ya ce ba za a kama ‘ya’yan kungiyar ba saboda yanayi na tsaro a kasa, Yeriman ya bayyana cewa, abin da El-rufai ke nufin yi, yana son ya janyo hatsaniya ne kawai a kasar nan.
Ita ma a nata bangaren, kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF gargadi ta yi da a kiyaye duk wani abu da zai yi wa zaman lafiya zagon kasa. Sakatare Janar na kungiyar, Mista Anthony Sani, ya bayyana cewar, karbo takardar da gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta yi daga kotu don cafko ‘ya’yan kungiyar gamayyar matasan Arewar ba wani abin dole ba ne, illa neman fitina.
Sani ya yi nuni da cewa, karbo takardar zai janyo koma-baya akan kokarin da Gwamnonin Arewa ke yi na tabbatar da zaman lafiya, bayan da Gwamnonin suka umarci matasan su janye wa’adin, kuma suka janye.
A cewarsa, “ni ma na bi ra’ayin wadanda suke cewa karbo takardar ba wani abu ne na dole ba, tunda gamayyar kungiyoyin tuni sun janye wa’adin. Karbo takardar zai janyo rusa kokarin kawo zaman lafiyar da Gwamanonin Arewa suke yi karkashin jagorancin Gwaman Jihar Borno, kuma Shugaban kungiyar Gwamanonin Arewa, Kashim Shettima, da kuma kwamitin zaman lafiya da tsohon Shugaban kasa Janar Abubakar Abdulsalami mai ritaya ke yi, ba lallai ba ne sai gwamnati ta karbo takardar ta kama matasan ba daga Kotu.