Shiga Damuwa Da Matsalar Rashin Taimako A Tsakaninmu

Rashin Taimako

Rayuwar nan sai a hankali, in kai ne yau gobe ba kai bane, tafiya mabudin ilimi. Shi ya sa idan har kana so ka cigaba a rayuwan da muke ciki halin yanzu, ya zama wajibi a gare ka Dan uwa ka tashi haikan domin samun tabbatuwar hakan.

Mun tsinci kanmu a irin wani lokaci mai tsadar gaske, babu mai jiran wani ko mai tambayar wane hali wane ke ciki, kowa ta kansa yake da iyalansa.sune a gabansa su yake ƙokarin yima hidima domin inganta rayuwar su.gashi kullum rayuwar kara tsada take. talauci, fatara,  yunwa da rashin tsaro da tsoro sai yawaita suke a cikin al’umma.

Masu abun hannu suna kara samu su da iyalansu a yayin da talaka yake kara fan tsama cikin talauci da babu ranar fita.gidaje da yawa a lokuta da dama da kyar ake samun abun kaiwa bakin salati. Hukumomi da masu hannu da shuni duk da ikirarin da suke na cewa sun fito da tsaruka domin samun daidai to wajen fitar da dimbin mutane daga talauci, har yanzu kwalliya bata biya kudin sabulu ba.

Mutane in sun shiga cikin mayuwacin hali na damuwa sukan rasa wanda zasu tunkara su fadamawa,dalili kuwa shine sau da dama in sun kai korafin, sai angama jin sirrinsu gaba daya sai ace musu dama jiya ne kazo da anyi wani abu yanzu kam sai dai kayi hakuri bawani abunda zan iya yi.

Bayan rashin samun biyan bukata, asirin mutum ya kuma tonu shi kuma wanda aka kai korafin wurinsa bazai barma cikin sa ba ya dunga yawo yana fadama mutane cewa wane yazo wurinshi ya nemi taimako, kuma alhalin bai taimake sa ba.haka za’a ta yawo da sirrin mutum majalisa majalisa ana gulmace gulmace.

Ba tausayi ba tausasawa tsananin mu, Dan’uwa, makwabci, aboki makusanci yana cikin matsanancin halin rayuwa ya rasa inda zai sa kansa yai ta yawo da abunda a cikin ransa yana damuwa daga karshe yaje ya samu matsalar rashin lafiya da zaiyi sanadiyar mutuwar sa.

In ya mutu sai kaga yan uwa sun cika da waje ana zaman makoki, ana amsar gaisuwa daga masoya da abokan arziki ana fitowa da abinci da abin sha iri iri ana ci ana sha ana hira.kuma tabbas lokacin da mamacin ke raye irin haka yake nema ya samu ya rasa.

Mutane da dama suna mutuwa sanadiyar damuwa suke shiga, bakuma don sun rasa yan uwa da abokan arzikkin daza su taimaka musu bane, aa sai dai su wadanda ya kamata su taimaka din basuda zuciyar taimako.

Akwai mutumin dana sani da kwana nan ya mutu sanadiyar rashin lafiya na shan wan jiki, ciwo ya same shi ranar talata 12-01-2021 ya rasu ranar litinin 18-01-2021, kafin mutuwar sa mutumin nan Allah ya jarrabce shi da ibtila’i na rasa gidan sa sakamakon rikicin siyasa da akayi a shekarar 2011 a garin Zonkuwa dake kudancin jihar Kaduna.

Rikicin yasa mamacin barin mahaifarsa da rasa aikin sa, ya dawo Zaria shi da iyalansa bayan sun kwashe kwanaki a cikin rijiya don gudu kar su rasa rayukansu.kafin daga bisani Sarki Zazzau Marigayi Alhaji Shehu Idris ya aika da jami’an tsaro sukaje har gidan suka fito dasu.

Dawowansu Zaria, Mai martaba ya bashi gida ya zauna shida iyalansa, yana kuma tallafa masa daidai gwargwado.a haka da sauran abubuwan da yakeyi yake gudanar da rayuwan sa.

Ana nan cikin hakane kwatsam sai Sarki ya rasu gashi gidan da yake zaune Sarki yaba ma wanda yake zaune gidan shekara kamar 40 da suka wuce.

Daga nan ne mutumin nan ya kara shiga damuwa, gashi yana da yara mata kamar guda uku da suka isa aure, guda daya kawai ta samu miji, kullum tunanin shi ind yaran nan zasu kwanta da abincin da zasuci, yayi iya ƙokarin sa domin yaga ya sayar da gidansa na Zonkuwa domin sayan wani a Zaria abun ya faskara.rayuwar tayi kunci sosai gashi babu wata alamar samun taimako daga wani ko kuma hukuma.

Yana ta yawo da damuwa ba wanda zai iya fadamawa domin magance ta, ko abunda zaici shi da iyalansa da kyar yake samu, shima ba wanda zai wadata suba.ga tunanin wadannan yara yan mata na rashin miji kada halinda suke ciki na rashi yasa suje a 6ata masu rayuwarsu.

Duk irin wannan tunanin ne dana sauran damuwowi yasa ya yanke jiki ya fadi rabin jikinshi ya shanye baki ya karkace a ranar Talata bayan kwana shida kuma ranar litinin Allah ya kar6i rayuwarsa. Allah yaji kanshi da rahama Amin.

A jiya kuma abokina yake gayamun wani dan gidansu da aikin hanya ya rutsa da inda yake zaune sanadiyar hakan ya tashi ya koma wata anguwa mai nisa daga asalin gidansu, yana da yara takwas, Babbar yarsa zatakai kimamin shekara 14, gashi bawani aiki taka maimai da yake.saboda haka yaran ma ba tunanin a basu ingataccen ilimi ko kulawa ake ba. Aa yadda zaa samu abunda zaa basu suci shi ake.yakan tako a kafa daga anguwar da ya koma yanzu zuwa anguwar su kimamin kilomita 5 ko fiye da safe don neman wanda zai dan bashi abunda zai ka masu su karya.

Adadin mutanen da suke rayuwa a haka a cikin al’umma suna da damar gaske.gashi baa samun taimako daga hannun masu shi ga hukumomi musamman na jiha da kananan hukumomi da sukafi kusanci da mutane ba wani shiri da suke naganin sun kawo abubuwan da zai rage radadin rayuwan da mutane ke ciki. Allah ya mana gudunmawa Amin.

 

Exit mobile version