Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Shiga Jirgin Kasa Sai Da Katin Shaida – Gwamnatin Tarayya

by Tayo Adelaja
August 22, 2017
in LABARAI, MANYAN LABARAI
1 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da cewa duk wani fasinja da zai shiga jirgin kasa mai aiki daga Abuja zuwa Kaduna dole ya nuna katin shaidarsa, ministan sufurin Nijeriya, Rotimi Amaechi ne ya ba da wannan umarnin ga hukumar kula da tashar jirgin kasa.
 Amaechi, yace, ‘duk wanda zai siya tikitin shiga jirgin toh sai ya nuna katin shaidarsa saboda daga yanzu za a dinga rubuta sunan kowa akan tikitin sa baro-baro saboda maganin masu babakeri.’
“Mun yi wannan tsarin ne saboda korafe-korafe da ake yawan samu daga matafiya, wanda ake zargin wasu ma’aikatan jirgin kasan na tara tikitin taragon farko wanda yake na masu sukuni, domin su siyar wa masu hannu da shuni, da kuma masu siyan tikitin dan su siyarwa wasu fasinjoji daban”, Inji Amaechi.
Ministan ya kara da cewa, ‘mun canzawa wasu daga cikin ma’aikatan da ake zargi da boye tikiti wajen aiki, sannan mun tura wasu ma’aikatan da za su tabbatar da aikin da wannan sabon umarnin.
 A karshen ya tabbatar da kokarin hukumar sufurin na ganin sun inganta harkokin sufurin jirgin kasa, ta yadda fasinjoji za su iya dogaro da jirgin kaco-kam.
Taragun jirgin hudu daya na masu sukuni ko `yan kasuwa, ragowar uku kuma na sauran jama`a, sannan an kayata su da na`urar sanyaya daki, ga kuma makewayi.
Batun tsaro na daga cikin abubuwan da ke kara wa jirgin tagomashi, musamman ma matsalar fashi da satar mutune da ake fama da ita a kan hanyar motar Abuja zuwa Kaduna, duk kuwa da cewa mahukunta na ikirarin daukar matakan murkushe miyagun da ke aika-aika a kan hanyar da kuma dazukan kewaye.
SendShareTweetShare
Previous Post

Za Mu Fitar Da Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP Daga Arewa- Makarfi

Next Post

Sani Sidi: Shekaru 51 Masu Albarka   

RelatedPosts

Hutun Kirsimeti

Gobarar Sakkwato: Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Tambuwal

by Muhammad
10 hours ago
0

Daga, Sharfaddeen Sidi Umar, Kakkarfar tawagar Gwamnatin Tarayya ta jajantawa...

An Sace Jami’ar Yaɗa Labarun NIS Reshen Jihar Edo

An Sace Jami’ar Yaɗa Labarun NIS Reshen Jihar Edo

by Sulaiman Ibrahim
13 hours ago
0

Masu garkuwa sun yi awon gaba da jami'a mai magana...

Tsaro: Wasu Gwamnonin Nijeriya Na Ganawa Da Shugabannin Fulani Makiyaya

Tsaro: Wasu Gwamnonin Nijeriya Na Ganawa Da Shugabannin Fulani Makiyaya

by Sulaiman Ibrahim
13 hours ago
0

Yau gwamnonin yammacin Nijeriya ke gudanar da wani taro da...

Next Post

Sani Sidi: Shekaru 51 Masu Albarka   

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version