Shiga Tsakanina Da Masoyina Ya Sa Na Fara Rubutu – Na’eemerh Sulaiman

Rubutu

Fitacciyar marubuciyar littattafan Hausa, wacce ke sharafinta a yanar gizo Marubuciya Na’eemerh Sulaiman, ta bayyana dalilin shigarta duniyar rubutu da marubuta, a cikin tattaunawarta da wakilinmu Adamu Yusuf Indabo ya yi da ita a yammacin shekaran jiya Talata. Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance:

 

To farko za mu so jin ko wacece Na’eemerh?

Da farko sunana Na’ima Sulaiman Shu’aibu, duniyar marubuta ko kuma na ce a medi ina amfani da (nimcylub)wasu kuma suna kirana da (sarauta). An haife ni a shekara ta 1997 (13/8/1997) a unguwar Sheka dake Jihar Kano, kuma har yanzu ina zaune a garin Kano a unguwar tamu ta Sheka tare da iyayena. Na yi karatuna na islamiya da boko har ma na yi sauka duk a Kano.

 

To duba da yadda sunanki ya karade duniyar rubutu, to shin ya a kai kika tsinci kanki a matsayin marubuciya?

Wow tambaya mai kyau. Ban taba tunanin zan dauki pencil da littafi da niyar rubuta wani abu makamancin labari ba, amma abu ne mai sauki a wajena karatun littafi koma wani abu ne, amma an ce rayuwar duniya na nuna maka wanda yake son ka, kuma zama da mutane yana nuna maka wa kake so, haka kuma yau da gobe na nuna maka wane yake kin ka. To babu shakka haka ne a wajena, dicret ba zan dora abun a kaina ba, amma idan kana so a rayuwa mutane su fahimci wane ne kai kuma har su yi amfani da abinda kake kuma ya ba su sha’awa dole ne kai masu misali da kai karan kanka. Zan iya cewa silar kawata na fara rubutun littafi, ma’ana kamar ta shiga rayuwata da kuma wanda nake so ne, ta yi min karya tare  da fadin abinda ni ban san da shi ba, kuma daga baya ta zage wajan saurayin ta ce ni ce na aikata hakan. Gaskiya wannan abun ya bakanta ran nimcy ƙwarai da gaske, sai dai koda wasa ban nuna mata bacin raina ba, kasancewata mai hakuri da kuma dauke kai. Daga nan na fara tunanin ta yaya zan fidda abinda yake damu na kuma yake damun jama’a musamman ‘yan uwa mata? Kamar sa wasa na dauki littafi na fara rubutu sai na bawa sisterna ta duba, sabida seriously ni ban gama gane hausa ba, ba wai dan ban iya ba, haka nan daga ubangiji domin ko magana nake wani lokacin ina sanya gwaranci cikinta. Tana dubawa tace masha allah amma wannan labarin wanne book kika dauka, sai na yi dariya na ce “a’a kawai na rubuta ne” daga nan tace zan iya amfani da wannan damar domin na isar da sakona, na ce mata “ta yaya?” ta ce ai akwai online writers. Daga nan na fara neman shawara bana mantawa hadda ita kawar tawa na nemi shawara da kuma saurayin. Allah ya sakawa yayana kuma dan uwana da alkairi yaya auwal nuhu sosai ya taka rawar gani a cikin lamarin domin har english story ya rubuta min domin na fahimci wasu abubuwan. Tun daga na fara fadakar da al’umma da baiwar da ubangiji ya ba ni domin dukkan wanda ka ga yana creating story tabbas dan baiwa ne ba kowa ke iya hakan ba, kuma daga nan na yi littafai da dama.

 

Tun wacce shekara kika fara rubutu, kuma wanne littafi ne farko da kika rubuta?

Na fara rubutu ne tun a shekarar 2016. Littafin da na fara rubutawa kuma shi ne ‘Kaddarar Mace’.

 

To zuwa yau kin rubuta littattafai guda nawa?

Zuwa yanzu na rubuta littafai guda Tara, su ne 1)Kaddarar Mace. 2)Ashe ‘Yar Babata Ce. 3)Lamrat. 4)Sai Na Aureta. 5)Raino Ne Sila. 6)Izzar So. 7)Jiddah. 8)Juyayi. 9)The new emir. Wadannan su ne littattafan da na saki aka san su a online. Sai kuma masu zuwa nan gaba akwai: 1)Uncle Ne. 2)Tuggu biyu. 3)Tagwayen Asali.

 

Na ji cikin littattafan naki akwai ‘The New Emir’ ke nan bayan littafan Hausa kina yin na turanci ma?

Ban taba littafin turanci ba amma ina saka ran nan gaba. ‘The new emir’ littafin hausa ne kamar ko wanne kawai na sanya sunan haka ne.

 

To a cikin jerin wadannan littattafan naki, wanne bakandamiyarki?

Za ka sani cikin juyayi domin ni karan kaina ka ba ni aiki. Dukkan wannan littafin da ka fadi sunansu an san ni na rubutasu, amma zan iya cewa  bakandamiyata shi ne The new emir domin nayi shauki a rubutunsa musamman da yake na sarauta, ni kuma dukkan abinda yake na sarauta ne ina son shi sosai amma littafin da nayi suna ta dalilinsa shi ne Lamrat.

 

To cikin wadannan littafai naki guda tara da kin yi, wanne ya fi ba ki wahala wajen rubutun sa, kuma me ya sa?

Nafi shan wahala akan Izzar So kasancewarsa labarin masarautar kuma a kansa na fara labari na masarauta, sau da yawan lokacin nakai tsaida typing sai na je na yi tambaya akan abu kasancewar hadda yaren Igbora koto nayi amfani da shi da ba sa bawa hausawa auran yaransu. Kuma na sha surutu wajan mutane da kuma fans da kuma rashin posting da ba na yi kullum.

 

To cikin wanne yanayi kika fi jin dadin yin rubutu?

Tab idan har ina son nai typing hankali kwance to na fi son na jini ni daya inda babu hayaniya, sannan na fi son na ji kida yana tashi bawai wakar hausa ba, a’a indian music mai dadi,kuma na fi son nai rubutu da daddare.

 

To wadanne nasarori kika samu ta fuskar rubuce-rubucenki?

Fadin nasarorin dana samu a rubutu bata baki ne, babban nasara shine yadda duniyar yanar gizo a harkan rubutu ta san da zamana, zan yiwa kowane babba magana kuma ya saurara ta hanyar kasancewata marubuciya, babban nasara yadda nake da farin jini cikin ‘yan uwana marubuta, da yawa ina zaune za a neme ni, wasu kuma manyan wanda zan karu da su nice nake nemansu, ko’ina ana faɗin Nimcy lub wattpad, istgram, telegram, bakandamiya, facebook da dai sauransu, ina rayuwa cikin farin ciki da jin dadi, domin an sha yi min kyautar abu dalilin rubutuna masha Allah ci gaba kullum samuwa yake tako wanne bangare.

 

To wanne kalubale kika fuskanta dalilin shigar ki duniyar rubutu?

Eh tabbas idan mutum bai samu nakasu abu bama da sauransa. Ni a rayuwa dukkan wacce naga ana son littafin to ina samun hanyar da zan bi na samu kusanci da ita domin sanin dalilin da ya sanya hakan ke faruwa, kuma cikin ruwan sanyi nake fahimtar abu, daga nan na fahimci kawai tauraruwar mutum ke haskawa ba wai finka wani abu ya yi ba, domin da za a bibiya sai a samu ka fishi ta wata hanyar, to dalilin hakan wasu kananun marubuta suke maganar wai na fiye shigewa mutane a tasu fahimtar. Ni kuma ina ga wanda ya san abinda yake shi ne zai nemi dalilin jin wani abun ai.

 

To mene ne babban burinki a rayuwa?

Ba ni da wani buri wanda ya huce na ga na zama shararriyar marubuciya inda kowa zai san ni kuma ya san da zamana, ina so na yi fice sosai duk zuwa yanzu ma Allahamdulillah.

 

Za mu ci gaba sati mai in sha Allah.

Exit mobile version