Shiga Yajin Aiki Ba Shi Ne Mafita Ba -In Ji Hasan

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

An bayyana cewar Nijeriya kasa ce wadda wasu marasa kishin kasar suka yi mata mummunar illa a shekaru da dama, a bisa haka ne gwamnatin Muhammadu Buhari ta kudiri aniyar shawo kan manyan matsalolin da suka addabi kasar nan musamman ta fuskar tattalin arziki da tsaro da kuma walwalar jama’a. Hassan Hassan, shugaban tsangayar koyon aikin jarida ta gwamnatin tarayya da ke Bauchi ne ya bayyana hakan a hirarsa da wakilinmu

Ya ci gaba da cewa, a duk lokacin da za a yi gyara dole ne sai an sha wuya ,a bisa hake ne ya yi kira ga al’umman kasar nan da cewar su sanya kishin kasa da son ci gaban kasar kan gaba kafin komai. “Idan kowa zai shiga yajin aiki kan matsalarsa ta kashin kai, ta yaya ne za a samu gyara a Nijeriya, yanzu lokaci ne da gwamnatin nan ta fuskanci shawo kan manyan matsalolin da suka dabaibaye kasar nan don haka akwai da bukatar masana da sauran jama’a kasar nan su rungumi halin hakuri domin a samu kai wa ga nasarar da aka sanya a gaba”. In ji shi.

Hassan ya kara da cewa, wasu tsirarun mutane a kasar nan ne suke haifar wa kasar nan cikas wajen samun nasarar da aka sanya a gaba. Inda ya ce, “An zo an cire wa malamai wani kashi a cikin hakkokinsu, an yi haka ne domin a tunzura su, su shiga yajin aiki a hana komai tafiya a kasar nan. Haka sauran sassan gwamnati su ma hakan ake son su ma su yi, yanzu ka ga idan aka sanya yajin aiki ya dabaibaye gwamnatin nan aikin da aka sanya gaba ba zai iyu ba kenan”.

“Matsalar da muke fuskanta wasu tsiraru suke hana ruwa gudu, cikin kowane lamari ribar da za su samu kawai suke dubawa, matukar ba su da riba ko wani kaso a ciki to ba za su bai wa wannan abu muhimmanci ba, sai dai su sanya hanu a wajen tabarbarewar wannan abin. Daman kiyayya ce ma a tuntuni a zuciyarsu”, in ji Hassan.

Dadindada wa, malamin ya ce, masu korafin ganin cewar an samu kudi a Nijeriya ko an tara kudi an ki sakewa ga jama’a ya ce Nijeriya ta sanya gaba wajen inganta asusun ajiyarta na banki ta kasar waje wanda hakan babban ci gaba ne ga kasar nan “Da yardar Allah mun iya tabbatar da asusun Nijeriya na kasa na waje yana nan yana kara bunkasa, duk kudaden da kasa take samu ta hanyoyin kwastam da mai, ko ta wasu hanyoyi daban an adana shi ne zuwa kashi uku, na farko kudaden Nijeriya suna tafiya ne ta hanyar bayar da kudaden tallafi wa manoma domin inganta harkar noma, na biyu kuma bunkasa da gyare-gyaren hanyoyi da kuma sauran abubuwan da ake so na kasa, sannan na uku kuma sanya kudi a cikin asusun nan na Nijeriya na waje. Ta yawan kudin da asusun ku ke da shi ne kasashen waje za su amince su sanya jarisuna a Nijeriya ba tare da taraddadin za su yi asara ba, koda sun yi jarinsu ya samu matsala suna da inda za a biyasu wannan fa kuma ci gaba ne sosai wa kasa. Yanzu haka wannan asusun ya karu sosai fiye da gwamnatocin baya”.In ji sa

Ya kuma bayyana cewar a sakamakon shawo kan matsalolin da Nijeriya ke fuskanta ne ya sanya wasu suke neman hanyoyin lalata komai a Nijeriya domin hana wannan gwamnatin kai wa ga gaci, ya bada misali da rikicin da Nnamdi Kanu da kuma yawaitar ma’aikatu masu shiga yajin aiki a halin yanzu “Bamu ce wasu basu da bukatun da ya dace gwamnati ta cika musu ba; amma meye sa sai a irin wannan lokacin da aka gangaro magance manyan matsalolin kasar nan. Idon kowani ma’aikata suka ce zasu shiga yajin aiki me kenan aka yi? A tsaya da muhimman ayyukan da aka nufa domin bukatun wasu ne ko kuma a samu akai yadda ya dace? Abin da muke fada wa jama’a shi ne da gangan wasu ke ingiza malamai da sauran ma’aikata shiga yajin aiki domin cimma muradinsu na kashin kai”. In ji sa

Hassan ya bayyana cewar manufar shigan ma’aikata yajin aiki da manufar da shugaban masu neman kafa Biafira Kanu yake da shi a matsayin dukkaninsu manufa daya suka zo da ita, ya ce manufar tasu ita ce hana Nijeriya kai wa ga samun nasara na fita daga cikin wannan matsatsin na tattalin arziki.

Daga karshe, sai ya kalubalanci ma’aikatan gwamnati musamman kungiyar malamai da suke ci gaba da yajin aiki da cewar, su zauna su yi karatun ta-nutsu domin al’umman Nijeriya su samu kai wa ga samun nasarar da aka nufa.

 

Exit mobile version