Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Shimfida Bututun Gas: Ganduje Ya Jinjina Wa Buhari Bisa Kaddamarwa

Published

on

An yaba wa Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari bisa shimfida bututun iskar gas, wanda zai iya magance matsalar harkokin masana’antu a Jihar Kano.

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne bayyana hakan, ya na mai cewa, kaddamar da aikin shimfida bututun iskar gas din daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano, wanda Shugaba Buhari ya yi a ranar Talatar, shi ne tsarin ingantacciyar siyasa, wacce za ta gaggauta dawo da kimar masana’antu, wanda zai farfado da tattalin arzikin Jihar Kano da kasa bakidaya, kamar yadda babban daraktan yada Labaran Gwamnan Jihar Kano, Malam Abba Anwar ya shaida wa Wakilin LEADERSHIP A YAU.

Kamar yadda Gwamnan ke tare da shugaban kasar a bikin kaddamarwar da a ka gudanar ta kafar sadarwar zamani, daga Ajaokuta dake Jihar Kogi, ya bayyana gamsuwarsa bisa cewar, mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna muhimmacin fara wannan aikin tare da sake kaddamar da aiki da kuma tabatar da ganin an sake dawo da kimar masana’antun Jihar Kano.”

Gwamna Ganduje ya tabbatar da cewa, da wannan gagarumin aiki, Jihar Kano ko shakka babu ztai dawo da kimar tattalin arzikin ta wanda hakan zai bai wa Jihar Kano damar sake rike matsayin ta na cibiyar ciniki da masana’antu a yammacin afirika.

“Ba mu da wata kalma da za mu yi nuna godiyarmu ga shugaban kasa bisa wannan kulawa da soyayyar mutane Jihar Kano, wanda kuma yin hakan zai yi na so zuwa sauran sassan tarayyar Nijeriya, domin lokacin da masana’antun Jihar Kano, Kaduna da sauran sassa zasu sake dawo da kimarsu, amfanin zai zaga Nijeriya da ma makwabtan mu,” inji Ganduje.

Haka kuma Gwamnan ya bayyana cewa, “Mun fahimci wannan aiki zai samar da ingantaccen ci gaba ga aiki samar da wutar lantarki mai zaman kanta guda uku, ta Abuja mai karfin doki (135MW), Kaduna (900MW) da kuma Kano mai karfin (135 MW). Hakan ko shakka babau zai haifar da cigaban da ake bukata ta fuskar iskar gas ga masana’antu a wannan bangaren.”

Lokacin da aka kammala wannan aiki a tsawon watannin 24 da watanni 12 na shirin ko ta kwana. Gwamna Ganduje ya ce, “wannan ke nuna kyakkyawan kokari da jajircewa daga bangaren mai girma shugaban kasa.

Ko shakka babu abinda ke zuciyar shugaban kasa shi ne cigaban al’umma. Da ya ke tsokaci kan karfin wannan aiki idan aka kammla shi, ya ce “duk da cewar aikin shimfida bututun iskar gasa din, wanda ya kasance zai hade wannan lardi na Nijeriya (“TNGP) mai karfin jigilar iskar gasa 2.2 Bef/d, hakan ke nuna damuwa da kuma kulawar kyakkyawan jagoranci.”

Ya kara da cewa, “wani abin alhairi kuma kan wannan aiki, ya zo a lokacin da a ke bukatar sa. Tunda farko an tsara shinfida wanna bututun isakar gas nesa da bututun man fetur dake shimfide a kasa.

A karshe Gwamna Ganduje ya kammala jawabinsa da jinjinawa Shugaban Kasa a madadin Gwamnati da al’umma Jihar Kano kan wannan gagarumin aikin shimfida bututun iskar gasa, wanda ya hakikan ce zai samar da hanyar magance matsalar da ta jima tara addabar masana’antu a Jihar Kano da kasa bakidaya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: