Da farko, shin ina ce kasar Hausa?
Masana da dama sun yi magana a kan inace kasar Hausa? daga cikin su akwai Shehin Malami Farfesa Amfani ya kawo a mukalarsa mai suna “Hausa da Hausawa: jiya da yau da gobe cewa “Gidan Hausa na gado shi ne arewacin Nijereya da kudancin jamhuriyar Nijar. Ya kara da cewa an tabbatar da a can cikin tarihi wani lokaci da mutane suka yi ta yin kaurace-kaurace daga yankin tafkin Chadi suna yin yamma. Babban dalillin yin waddannan kaurace-kaurace shi ne kafewar tafkin Chadi. Gulbin Kebbi shi ne makurar wannan kauna a sashin yamma. Tsakanin Gulbin Kebbi da tafkin Chadi akwai nisa kwarai kuma akwai makekekiyar kasa. A lokacin kaurace-kauracen wadan su mutane sun karasa har gulbin Kebbi wadansu kuwa iyakar su tsaunukan kasar Borno. Mafiya yawan mutanen sun watsu ne awurare daban-daban cikin wannan makekiyar kasa yadda harma ba a san lokacin da suka zo ba. Ba a san su sosai ba sai akarshen karni na sha biyar. Mutanen kabilu ne daban-daban. Da Hausawa da Bolawa da Ngizim da Manga da Margi da Buduma da Kotoko sune manya daga cikin kabilun. Daga cikin manyan kabilun Hausawa sun fi yawa kuma sun fi warwatsuwa cikin wannan makekiyar kasa.…
Kasar Hausa tana daga girma kwarai da gaske. Amike daga arewa zuwa kudu, Kasar Hausa ta fara daga Azben har zuwa kusurwar arewa maso gabas ta tsaunukan kasar Jos. Daga nan sai ta kwasa ta yi yamma har zuwa inda kogin Kaduna ya yi babban doro. Daga nan sai ta buga ta yi arewa maso yamma sai da dangana da wani katon kwari na gulbin Kebbi. Daga wannan wuri sai ta karkata ta nufi arewa maso gabas har Azben. Wannan zagaye shi ya nuna iyakokin kasar Hausa a gabas da yamma da kudu da arewa. Kasar da wadanan iyakoki suka iyakance, ita ce kasar Hausa. Har izuwa yau, wannan kasa wato kasar Hausa ita ce mazaunin hausawa. Hausawa sun zauna a wannan makekiyar kasa fiye da shekaru dubu ashirin. Bai tsaya nan ba ya dora da cewa, wadansu abubuwa sun faru wadanda suka kawo fadaduwar kasar Hausa. Ire –iren abubuwan sun hada har da nashe wadansu al’ummai wadanda asalin su ba Hausawa ba ne. Fadaduwar kasar Hausa ta faru ne a karni na sha biyar, da na sha shida da na sha bakwai.
Hausawa Da Tsarin Zamansu
Tsarin zaman Hausawa tsari ne mai ban sha’awa mai kyakkyawan tsari da al’kibla kyakkyawa. Asalin zaman Baushe. Yana fara wa ne tun daga zama na mutum da iyalinsa wato shi da matarsa su kadai, har su zo su fara hayayyafa, su fara tara iyali, daga nan sai gida ya fara taruwa sai gandu ya kafu daga nan sai gida ya fara tsinkewa, ma’ana yara in sun isa aure ko jikoki sai su fara fita waje suma su kafa nasu gidajen da haka har unguwa ta kafu, daga nan sai kauye ya ginu daga nan sai gari ya fara burunkasa, tare da taimakon hijira ko kaura ta wadansu unguwanni ko kauyuka su tayar da gari daga haka zamantakewa za ta fara ta kuma karfafa. Hakazalika, a tsarin zaman Bahaushe akwai rukunin shugabanci kama da Sarakuna da Hakimai da Dagatai da masu Unguwanni. Zuwan Musulunci ya sa aka sami karin alkalai a rukunin ma su mulki.
Baya ga rukunin masu mulki, da sauran jama’a talakawa, amma a rukunin talakawa suma sun kasu kashi-kashi kamar haka: malamai, da attajirai, sannan sauran talakawa. A wannan rukuni da akwai masu sana’a da sarakunansu. Sai masu tsaron kasa wadanda suka hada da mayaka da dogarai, da kuma yaran masu mulki. Idan aka kalli wannan tsari na zamantakewar Bahaushe da kyau, za a ga cewa babu wani rukuni na mutane wadanda suke zaman kashe wando a cikin al’ummar Hausawa ko a zamantakewarsu.