Shimfida Game Ga Tsarin Shugabancin Sana’o’in Zamani

Sana'o'in Zamani

Daga Haruna Aliyu,

Ta tabbata cikin wasu garuruwa dake a wannan kasa, hada da kasashe Hausa, tsarin samar da shugabancin sana’o’in ya banbanta da irin yadda ake samar da su yanzu, da kuma tun wasu shekaru da suka shude.

Daga dalili da suka sabba ba irin yadda za a samar da Shugabancin, da yawan wasu sana’o’i a yau, babu su, ko a ce, ba su gudana ba a jiya, misali, sana’ar wankin mota, sana’ar adaidai ta sahu, sana’ar kwallon kafa, sana’ar pos, sana’ar masu gyaran mota, sana’ar gyaran babur, sana’ar shayi, sana’ar chajin waya da makamantansu. Ko ba a fadawa mai karatu irin hanyoyin da ake bi wajen Samar da shugabancin wadannan mabanbantan sana’o’i da ake gabatar ba, hakika zai ba wa kansa amsar cewa, ba a fadodin sarakunan gargaiyar Hausa, ko na ibo, ko na yoruba ne ba ake nada wada da za su Jagoranci kungiyoyin ba. Sabanin irin yadda a can baya tarihi ke fayyace irin yadda sarakuna ke nada sarkin noma, sarkin kira, sarkin fawa, sarkin wanzamai don jagorantar wada da ke yin irin wadannan sana’o’i.

Zamantakewa da kuma bunkasar yanayi ta fuskar kirkire-kirkire, wadda shi ne ya samar da zuwan fasahar zamani. Inda al’umma ke samun gudanar da sana’o’in su asauwake wajen biyan bukatun abokanan harkokinsu.

Duka wadancan sana’o’i da aka lasafta a sama, ba za a sami wata sana’a daya tilo da take zaune kara-zube, ba tare da tsarin Shugabanci ba. Ba ya ga salon fitar da tsarin shugabanci a zamanence, dadin-dadawa ma, gwamnatoci na neman kungiyoyin, da su je ofishin hukumomi su yi rijistar kungiyoyin nasu. Bugu da kari, dole ne kowane rukuni na masu wata sana’a su Samar da tsarin Shugabancinsu, gabanin a yi musu rijistar a hukuma ce.

Sabanin lokutan baya, lokacin da za an nada shugaban wata sana’a, wanda zai yi ta zama jagora kuma shugaba har mutuwarsa. Idan ya mutu, sai a zabi guda daga jinin sa, “ya” yansa ko “yan uwansa na – jini, ya maye gurbinsa. A tsarin sana’o’in zamani, ba a nada shugaba a fada, sannan akwai adadin wasu shekaru da zai yi bisa kujerar jagorancin, sai kuma ya sauka a sake zabe. A tsarin Shugabancin yau, kasantuwar akasarin sana’o’in na da rubutaccen tsarin mulki, a cikin dokoki, akwai irin nau’in laifin da shugaba zai aikata, a sauke shi. Bugu da kari, ba a zama  shugaba ko jagora ta hanyar gado. Amma,jinin wani shugaba da ya sauka, ko ya rasu, ko aka tube shi daga mukaminsa, ya na da yancin da damar iya tsayawa zaben shi ma, Sabanin shugabanci ko jagorancin gargajiya.

Yana da kyau mu kalli sabbi, ko a ce sana’o’in zamani da ake da su a yau, a nazari irin hanyoyin da ake samar da shugabancinsu ko jagorancinsu, tare da yin wani dan tsokaci game da su gwargwadon hali.

Exit mobile version