Peter Gloor bai mallaki mulmulallen gilashin duba (crystal ball) ba, kuma ba ya ramlin ganyen shayi, inda zanen layukan hannunka ke ikirarin yin magana da matuna “daga wani bangare.” Duk da haka masu binciken kimiyya a Cibiyar Fasahar kere-kere ta Massachusetts (MIT) sun yi ikirarin iya gane abin da zai faru nan gaba.
Dauki misalin yadda jam’iyyar Republican ke kokarin tsayar da dan takarar zabe, a shekarar da ta gabata, inda kuri’un Newt Gingrich suka yi ta hauhawa, inda wasu masana su ka yi kyakkyawan zaton shi zai doke abokin karawarsa Mitt Romney. Amma Gloor ya yi hasashen cewa ba zai ci ba.
Gaskiya ta tabbata cewa cece-kucen da ake ta yi a kafar Twitter, alamu sun nuna yadda tsohon Shugaban majalisa ke samun galaba, amma masu nazarin bayanan da aka tace a shafin Wikipedia, Gloor ya yi hasashen cewa Romney zai doke shi. Daga karshe dai ta tabbata Gloor ya canki gaskiya mai cin daidai: Romney ya kayar da Gingrich da wawakeken gibi da daddare.
Tabbas akwai yiwuwar a ce hasashensa cankar sa a ce kawai. Sai dai Gloor ya ce hasashensa ya sha tabbata tsawon lokaci akai-akai. A wasu lokutan ma, yadda yake nazarin al’amura (dalla-dalla) kan taimaka wajen fitar da sakamakon zaben inda jin ra’ayin jama’a ya gaza.
“Mutanen sun yi wa masu tattara kuri’un jin ra’ayin karya, saboda ba sa so a dauke su masu nuna wariya.” inji Gloor.
Tsarin bincikensa ya bunkasa a jerin nau’ukan aikin kimiyya, wanda ake yi wa lakabi da nazarin hangen abin da zai auku gaba. Wani fanni ne da ke daukar hankalin kowane mutum kama daga kan hamshakan masu shiryawa da kasuwancin fina-finai, wadanda ke kokarin gano fina-finan da za su shahara a wajen jiga-jigan jan rangamar harkar, da wadanda ke son cikakkun bayanai game da hannayen jari su ke samun nasara.
Su kuwa wadanda ke sha’awar harkokin siyasa, sukan yi amfani da wannan dabarar ne wajen hasashen gano wanda zai lashe zaben da ke karatowa. ‘Binciken Dimbin Al’amura”
Bibiyar kadin al’amuran bayanan da ke tattare a bainar jama’a don gano abin da zai auku nan gaba ba sabon al’amari ba ne, amma yunkurin da aka yi ta yi a baya sun mayar da hankali ne kacokam kan labaran kafafen yada labarai.
Gabanin fara yakin duniya na biyu, Gwamnatocin Amurka da Birtaniya sun yi ta bibiyar kafafen yada labaran duniya don gano musababbin tashe-tashen hankulan, sannan a lokacin yakin cacar baki, Gwamnatin Amurka ta dauki nauyin malaman jami’a don su bullo da dabarun lissafi da za a rika amfani da su wajen bibiyar rahotanni kafafen yada labarai don gano matakan da Tarayyar Sobiyat ka iya dauka (abubuwan da za ta aiwatar a gaba).
Shekaru goman da suka gabata kafafen shafukan sada zumunta irin su facebook da Twitter sun bullo da makwararar labaran duniya. Kalebe Leetaru, masanin kimiyya kwamfuta a Jami’ar Illinois ya kwatanta shafukan sada zumuntar da wani abu kamar “Kafar Shiga Mutane” saboda dimbin bayanan da suke tattare a wurin.
“Akwai biliyoyin al’amura da aka baza a Facebook kullum tare da aikewa da sakonni miliyan 200 a twitter,” in ji shi.
Dabarar dai ita ce a fahimci abin da bayanan ke nufi shi ne muhimmin al’amari a darussan. Misali, Gloor ya ce Twitter na da matukar alfanu wajen gano dabi’ar da ke da tasiri kan dimbin al’umma. Abin la’akari wajen kallon sabon fim, alal misali, abin da cincirindon mutane suka ce na da tasiri kan al’umma; yana da kyau ko fim din ya yi muni?
Dangane da zabuddukan fitar da gwani na Republican, bibiyar kadin al’amuran nazarin Gloor a Disamba ta yi nuni da cewa kodayake talakawa a shafin Twitter sun nuna cewa Gingrich ne zai yi nasarar lashe zaben, inda bimbin bayanan Wikipedia ma na nuni da cewa Romney ne ke kan gaba.