Da farko dai kungiyar kwallon kafa ta Barcelona bata buga kakar wasa ta bana ba da nasara bayan wasannin da kungiyar ta buga da farko-farko b atare da samun nasara ba wabda hakan yasa akayi hasashen cewa abune mai wahala kungiyar ta iya abin kirki a bana.
Ranar Lahadi Barcelona ta doke Athletic Bilbao da ci 2-1 a wasan mako na 21 a gasar La Liga da suka fafata a filin wasa na Camp Nou duk da cewa Athletico Bilbao din c eta doke Barcelona a wasan karshe na cin kofin Spanish Super Cup a kwanakin baya.
Lionel Messi ne ya fara ci wa Barcelona kwallo ta bugun tazara kuma kwallo ta 650 da ya ci a kungiyar sannan har ila yau kwallo ta 49 da ya zura a raga a bugun tazara a tarihinsa tun lokacin da ya fara buga kwallo.
Wannan sakamakon ya kai Barcelona ta koma ta biyu a kan teburin La Liga da maki 40 iri daya da wanda Real Madrid ta uku a teburi take da shi kuma Barcelona ta yi wasanni 10 a jere a gasar La Liga ba ta tare da an doke ta ba, wadda ta ci karawa takwas da canjaras biyu.
Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, na yin wannan kokarin ba tare da ‘yan wasan kungiyar da suka hada da Gerard Pikue da Ansu Fati da Philippe Coutinho da kuma Sergi Roberto ba sakamakon jinya da sukeyi.
‘Yan kwallon Barcelona Oscar Mingueza na taka rawar gani daga baya haka ma Antoine Griezmann da kuma Frenkie de Jong da ke cin kwallaye sannan Ousmane Dembele da ya kara tsayawa da kafafunsa.
Kuma salon da Barcelona ta koma bugawa na 4-3-3 ya ba ta damar buga wasa mai kayatarwa da kai hare-hare da dama a lokacin da take wasanninta bayan da kociyan kungiyar Roland Koeman ya canja salon wasan nasu a ‘yan kwanakin nan.
Barcelona tana ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki 10 tsakaninta da Atletico Madrid ta daya tana kuma cikin gasar Copa del Rey, sannan ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League a bana.
Yanzu da aka fada zagaye na biyu a gasar La Liga ga kuma wasannin bana sun fara shiga gangara, kuma Barcelona na saka kwazo kawo yanzu sai dai abin tambaya ko kungiyar za ta kai labari nan da karshen kakar bana?