Muazu Hardawa" />

Shin Da Gaske A Na Yin Yaki Da Cin Hanci A Nijeriya?

Yaki da cin hanci da rashawa a wannan lokaci na mulkin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a Nijeriya na daya daga cikin manyan manufofin wannan gwamnati na ganin cewa ta yaki cin hanci da rashawa da kuma alkawarin kama mutanen da gwamnatin ke kira a matsayin barayin  gwamnati. Alhali irin wadannan mutane sune suka tsaya suka yi amfani  da dukiyar da aka kira dukiyar sata suka zuba jari cikin yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari tun daga lokacin da wasu gwamnoni biyar da suka bar jam’iyyar PDP suka koma APC tare kuma da wasu ‘yan takarar shugaban kasa da ke ganin dasu ji kunyar wucewar cin zaben Goodluck Jonathan gwamma su goyi bayan Buhari duk abin da zai faru ya faru.

Yanzu kuma an sayi gari mai dokar barci ya wuce da gyangyadi yadda ake bayar da kudin a cire sunan Wanda yaci zaben fidda gwani a jefa sunan dan wane mai daurin gindi a gwamnati kuma Buhari ya kasa cewa komai, lamarin da ke nuna gaskiya na zargin da ake masa na yaudara da ko oho ko hassada ga duk wata damuwa da ba tasa ba. Domin da shine ke takara ya ci zabe kamar yadda suka yi 2015 , ace yadda ya ci zabe an cire sunan sa an sa na Atiku ko kwankwaso da har wannan lokacin bakinsa ba zai mutu da sukar yan jamiyyar da duk wani Wanda ke shugabancin Nigeria ba.

Amma tunda yanzu an tukuikuye mutane an bashi takara ba tare da karawa da wani ba yadda deligate na jamiyyar APC za su samu abin kaiwa bakinsu. Amma sai aka take kowa aka ce an bashi takara, duk Wanda aka zalunta kuma ya yi shiru tunda shima ya San abin da ya yi kuma shi da mukarransa sun San dole su amsa tambayar ubangiji madaukakin Sarki.

Saboda ganin wahalar da ake shata rikicin kungiyar Boko haram a lokacin yakin neman zabe duk aka mara masa baya, shima tsohon shugaban kasa goodluck ya wakkala ya mika masa mulki amma duk alkawurran da ya dauka sun gaza cika.

Hatta wanda suka mara baya aka ci gaba da gwagwarmaya har aka samu kaiwa ga nasara, ta yadda a wancan lokacin da ake neman taimakon su don a karya waccan gwamnati babu wani sharadi da aka gindaya na cewa duk wani wanda ya san kudin gwamnati ya sata kar ya zuba jari cikin  tafiyarmu wato a tafiyar Buharin, shiru kurum aka yi aka ci gaba da  fafatawa har aka samu nasara. Bilhasalima akwai labarin da muka ji a wata kafa na cewa akwai lokacin da tawagar yakin neman zabe ta himmatu  zuwa wani yanki na kasar nan kuma ya zamanto sai an dauki hayar jirgin da zai kwashi mutane da yawa kuma babu kudi, sai wani daga cikin wadanda suka yi zaben fidda gwani na shugaban kasa ya fadi,  Buhari ya ci shine ya dauko hayar jirgi ya yi biyan kaza a aljihunsa.

Har aka ce a wancan lokaci Buhari ya tambaye shi ina ya samu kudi yake zubawa tawagar tafiyar yakin neman zabe yace kudin da kuke cewa na sata ne haka aka yi raha aka wuce ba wanda yace ba za mu hau jirgi da kudin sata ba don yin wannan tafiya har aka tafi aka dawo. Bayan haka ance kudi tsaba milyan dubu hudu ya zuba a tawagar kamfen na Buhari, amma bayan an ci babu abin da aka saka musu sai cewar barayine idan an dawo za a kama su.an manta duk yarjejeniyar taimakon juna da aka kulla a baya, alhali talakawa ba abin da suka shaidanwannan gwamnati sai kuncin rayuwa da tsananin talauci da suke sha.

A yanzu kuma an wayi gari wannan mutum  ana tsangwamarsa da cewa tunda  ya zo yana cewa sai yayi takara ya kayar da Buhari shine kamun farko idan an sake kafa gwamnati kamar yadda wannan majiya ta bayyana. Koma me ake ciki abin nufi a nan shine an taimaki wannan gwamnati da kudin da ta kira na haramun ta kafu amma yanzu ne kuma ta bude ido ta san an  taimake ta da kudin haramun ta farga take son rama alheri da sharri.

Yadda su kuma talakawa bisa ga dukkan alamu murna suke yi a kullum da  tunanin wannan gwamnati za ta zo ta yaki barayi wasu murna suke yi suna ganin kamar duk abin da aka karba za a basu ne don su kau da talaucin su da kullam yake kara addabar su da iyalansu.

Amma sun mance a baya lokacin da barayin ke kwasar dukiyar suna rabawa  makusantan talakawan su kuma suna ba talakawan, ana musu kyauta da gine gine da a halin yanzu sai ko su ga motoci da jiniya suna wucewa.Kuma shi talakan Nigeria ba abin da ya ke so I’ll a ya ji an kama mai kudi andaure ko an wulakanta.

Hatta wadanda ake ganin masu tsoron Allah ne sun shiga gwamnatin yanzu sun kauracewa garuruwansu sai sayen manyan gidaje da filaye suke yi suna gina makarantu da asibitoci kurum.  Sabanin tunanin su a baya na canji, sai aka wayi gari a wannan gwamnati  duk wanda ya saci kudin ba abin da ya ke yi saiko daga shi sai ‘ya’yansa yana sayen gidaje da filaye yana fita waje da kudi yana adanawa idan talaka ko da danginsu ne sun kusance su sai su dauki abin da bai kai ayi cefane ba su ba mutum su ce kun san muna cikin gwamnatin Baba Buharine bama samu sai ko ku yi hakuri da abin da ya samu. Idan sun gusa gefe sai su ce basa son bata talaka da kudi kamar yadda waccan gwamnati ta yi saboda sun san ‘yan siyasar su na akida ne basa so su fahimci suna samu a cikin gwamnatin.

Alhali su da iyalansu kullum suna hanyar kasashen waje zuwa kai yara makaranta ko yin sayayya ko zuwa ibada da sauran facaka a kasashen duniya amma kullum maganarsu shine basa samun komai a cikin gwamnatin.

Yawancin su Allah ya jarrabe su da rowa da kuma bukatar sayen manyan gidaje suna gyarawa suna sanya kayan alatu suna rufewa da sayen duk wata kaddara da wani ya karye yasa a kasuwa yake neman a saya a bashi kudi ya biya bukata nan take suke tayin kaza su biya su rufe. Duk wanda ya musa kuma a rubuta ya ajiye a jira idan da rai sai bayan gwamnatin Buhari ta gama wa’adin da Allah ya deba mata kowa zai ji tonon sililin da zai yi mamaki ashe daula tana sa mutum yaki Allah ya sake halayensa, saboda lokacine zai sa ‘yan Nijeriya su san cewa da gaske kowace gauta jace sai ko bata sha rana ba  Idana gwamnatin Buhari na maganar zata kama tsoffin wadanda suka yi  mulki a lokacin PDP  talaka yakan yi murna harma wakoki kala kala ake  yi wa shugaban kasa da mukarrabansa da zimmar cewa wasu dodanni sun zo da za su kama wadanda suka ci musu dukiya a baya, mutane basa tunanin abin da zai je ya dawo a irin wannan yanayi.

Saboda duk wanda ya fi ka ya fika kuma wanda ya tara dukiya ya san yadda duniya ke tafiya ya kuma kafa mutanen sa a cikin gwamnati to duk wani yakar sa da za ka yi tamkar ka dauki dala da gammo ne. Saboda a lokacin da Buhari ke yakin neman zabe ya fara irin wannan magana ta zai kama mutane ya daure idan ya samu nasara amma aka shawarce shi ya sake tunani ta yiwu saboda da  shawarwarin da aka bashi, daga bisani sai ya koma kamfen yana cewa idan ya samu hawa gwamnati zai ja layi daga inda ya samu ya ci gaba daginawa.

Amma yanzu tunani ya sauya yadda kullum tunaninsa shine idan ya dawo zai kama manyan mutanen da suka yi mulki a baya kamar yadda yake zaton zai samu mulkin da sauki bai San cewa yanzu mutane talauci da yunwa da rashin cika alkawari sun sa a na jiran su a hadu a gaban akwatin zabe ba za su gane sun kasa cikawa mutane alkawurra sai izza. Allah ya sa masu zabe su gane masu cutarsu da masoyansu.

Exit mobile version