Daga Ibrahim Muhammad Kano,
A kwanakin baya ne dan majalisar tarayya mai wakiltar Dawakin Tofa,Tofa da Rimin Gado ya kawo wasu ayyukan gina tituna da suka hada dana Rimin gado zuwa Gulu Sai dai bayan kaddamar da soma aikin sai ga wata sanarwa daga Gwamnatin jihar Kano da ta yi umurnin lallai dan kwagilar ya tsaya da aikin kamar yadda Hon. Ahmed Dauda Lawan babban mataimaki ga Gwamna Ganduje ya sanar a madadin Gwamnan.
Sai sun kawo hujjar cewa, dan majalisar bai tuntubi Gwamnatin Kano ba, kafin kawo aikin da al’umma za su mora sai dai Gwamnatin Kano ta bugi kirjin cewa ita za ta yi aikin.
Sai dai wannan matakin da Gwamnatin Kano ta dauka bai yi wa yawancin al’ummar da za su amfani yin aikin hanyar da da dan majalisar ya kawo dadi ba, Sai ya zama murna ta koma musu ciki suka rika guna-gunin wannan mataki mara dadin ji a wajensu. Duk da cewa dai daga bisani Gwamnatin Kanon ta kaddamar da za ta yi aikin da kanta.
Sai dai a yadda ake jin sautin wasu ‘yan siyasa a jihar Kano a yanzu daga tsakar gidan jam’iyyar APC suna shiga kafafen labarai suna kira ga wasu daga cikin ‘ya’yan Gwamna Ganduje akan su fito don neman takarar kujerar ta tarayya na Dawakin tofa,Tofa,Rimin gado tasa wasu ke zargin cewa akwai shirin karkashin kasa da ake na ganin an hana Jobe sake neman takarar kujerar tasa anan gaba.
Wani abu kuma daya faru Wanda ya nuna karara a bayyane dole Hon. Jobe ya fuskanci kalubale in zai sake neman takara ta gaba a farfajiyar jam’iyyar APC shi ne wasu kalamai da aka jiyo Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya furta a ya yin da yaje kaddamar da fara aikin hanya da aka dakatar da dan majalisar Tarayya Jobe daga yin aikin wanda Gwamnatin Kano ta ce ita za ta yi.
A nan ne ma aka jiyo Gwamna Ganduje ya kalubalanci Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe da cewa wai tun zuwansa majalisar tarayya baya komai sai barci hatta kuduri ma baya iya kaiwa, baima iya turanci ba
Sai dai da dama masu lura da al’amura sun ji maganganun na Ganduje akan Jobe wani bambarakwai ya fito da soma yarda da has ashen da ake na cewa ana kokarin a sharewa ko dai daya daga ‘ya’yan Gwamnan ko kuma wani daga ‘yan siyasar yankin da yake da alaka da Gwamna Ganduje hanyar da za’a kauda Abdulkadir Jobe daga takara a nan gaba saboda ana cewa baya yin biyayya sannan kuma ko kafin haka dama ance akwai rashin jituwa da Joben ke dashi tsakaninsa da wani daga cikin jigo a Gwamnatin Ganduje da yake daga yankin Kano ta Arewa da ake zargin ana kutungwilar ganin an kauda tasirin jobe a yankunanda yakewa wakilci.
Sai dai wasu masu lura da yanayi na al’amuran siyasar Tijjani Abdulkadir Jobe a Kananan hukumomin Dawakin Tofa,Tofa,Rimin gado suna ganin zai yi wuya a iya murkushe tasirin karbuwar Jobe a tsakanin mutanen yankin domin kuwa ana ganin a siyasar yankin ya zama tamkar kudan zuma ne tashi a bika ba kawai wadanda suke tare dashi a jam’iyya ba akwai wadanda basu hada sunan jam’iyya da shi ba amma suna tare da shi a mutuntaka da karamci da suka sanshi akai dan haka nema lokacin zabe basa la’akari da jam’iyyar da yake, shi suke zaba. Da wannan ake jin cewa Gwamna Ganduje zai iya kauda tasirin karbuwar jobe kuwa?
Sai dai wasu na ganin akwai yiwuwar Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe zai iya barin jam’iyyar da ya ke muddin aka zo da son rai akansa, kuma shi ne ake hasashen babban ganganci da jam’iyya mai mulkin Kano a yanzu za ta yi muddin ta yi gangancin barin Injiniya Abdulkadir Jobe ya kuma gefe ya zura ido bama ya bar jam’iyyar ba.