Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MAKALAR YAU

Shin Haram Ne Taya Kirista Murnar Kirsimeti?

by Muhammad
December 24, 2020
in MAKALAR YAU
6 min read
Bikin Kirsimeti
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Musulunci addini ne wanda aka gina shi kan umarni da hani, dalilin da Allah ya yiwa musulmi kirarin cewa K3:110 “Kun kasance mafi alherin al’umma wadda aka fitar daga mutane, ku na umarni da alheri kuma ku na hani daga abin da ake ki” wato cikar kamala ta al’umma shine haduwa a tallafi ayyukan alheri tare da yakar sharri. Amma a yau, za mu iya kiran kan mu da cancantar wannan matsayi kuwa?

Maganar halal da haram hurumi ne na Allah, kuma shi Allah ba ya kauron fadar abinda ba ya so da wanda ya ke so, amma sai a ka wayi gari an yi kutse cikin wannan hurumin sakamakon malamai na iya cewa wannan ko wancan halal ne ko haram ba tare da gamsashshiyar hujja daga cewar Allah ko ma’aiki ba. Domin tabbatar da halasci ko haramci na kowane abu madogarar farko ita ce hukuncin Allah a Kur’ani. Kuma duk wani abu da Allah ya sanar da cewa halas ne, misali yin aure, to har tashin duniya ba wani dalili da zai zo ya canza wannan hukunci, Haka nan idan Allah ya ce abu kaza haram ne, misali sata, babu wani dalili da zai dawo ya halasta sata.

samndaads

Bari mu dubi maganar taya kiristoci murnar bikin kirsimeti shin ya halatta ko kuwa haramun ne? Akwai wadanda ke cewa haramun ne, haramci wanda daidai ya ke da kisan kai (kun ji fa), amma masu wannan ikirarin ba su da wata shaida daga Kur’ani ko hadisi da ya tabbatar da hakan. Domin a Kur’ani kaf babu inda Allah ya haramta hakan duk da cewa su Ahlul Kitabi sun kasance makwabtan annabi tsawon kusan shekaru 13 da ya yi, ya na karbar wahayi a Madina. Sakamakon umarnin Allah da ya saukar cewa K60:8 “Allah bai hana ku, daga wadanda ba su yake ku ba saboda addini, kuma ba su fitar da ku ba daga gidajenku, ga ku kyautata musu kuma ku yi musu adalci. Lalle Allah na son masu adalci” Dalilin wannan aya ya sa Kundin tsarin mulkin Madina, wadda masana ke cewa shine kundin tsari na farko da wata kasa ta taba yi a rubuce na hadaddiyar kasa wadda ke dauke da al’ummomi daban daban masu mabanbanta al’adu da addinai, wanda annabi ya tsara ya samar da al’umma daya karkashin yarjejiniyar zama tare da kare juna duk da banbance-bancensu cikin adalci. Annabi ya dauki alkawarin kare rayuka da dukiyoyin Ahlul Kitab da ke cikin madina tamkar yadda zai kare na musulmi. Duk wanda ya taba duk wani jinsi da ke cikin yarjejeniyar tamkar ya taba dukkan mutanen madina ne, kuma za su taru su yake shi kamar yadda ya faru a lokacin yakin Khandak.

A zamaninsa a Madina, Annabi ya aiwatar da wani umarnin tsakaninsa da masu sauran addinai inda Allah ya umarce shi da cewa K4:86 “Kuma idan an gaisheku (musulmi) da wata gaisuwa, to ku yi gaisuwa da abinda ya ke mafi kyau daga gare ta, ko kuwa ku mayar da ita” Wannan ya nuna irin burin musulunci na kyautata mu’amala tsakanin al’ummomi domin ya umarci a mayar da gaisuwa mafi kyau daga wadda aka yi maka kuma mafi karanci shine ka mayar da daidai  yadda aka yi maka. Don haka tsawon rayuwarsa a Madina annabi na amsa gaisuwar abokan zamansa a doron wannan sharadi, idan ban da wasu lokatai da wasu shakiyan Yahudawa su ka rika yi masa wata gaisuwa ta makirci inda su ke cewa “As-sam-u alaika” wadda ke nufin su na masa fatan mutuwa inda shi kuma annabi ya bi waccan koyarwa ta Allah da amsa musu daidai da yadda su ka yi da cewa “Wa alaikum” wato kuma haka. Sakamakon wannan hali sai Allah ya sake saukarda ayar da ke cewa K2:104 “Ya ku wadanda su ka yi imani, kada ku ce ‘Ra’ina’, kuma ku ce ‘Jinkirta mana’ kuma ku saurara. Kuma kafirai su na da azaba mai radadi”

A farkon musulunci cikin umarnin Kur’ani da koyarwar manzon Allah, musulmi sun zauna da makwabtansu Ahlul kitabi cikin kyautatawa da adalci da auratayya da mikawa juna gaisuwa ta fatan alheri. Kuma kamar yadda shahararren marubucin sirah na farko wato Ibn Ishak ya ruwaito cikin littafinsa, labarin Kiristocin Najran da su ka kawo wa annabi ziyara a Madina. Wannan gungu na kiristoci guda 60 sun iso Madina kuma kai tsaye aka kai su masallacin annabi inda ya tarbe su a ciki. Sun zauna sun yi doguwar muhawara ta addini musamman game da lamarin Allantakar Annabi Isa. Daruruwan marubuta tsawon shekaru sama da dubu daga cikin musulmi da wadanda ba musulmi ba sun yi sharhi sosai daga mahangogi daban-daban na wannan ziyara saboda irin darussa da ziyarar ta nuna na yadda abubuwa su ka wanzu a lokacin, wanda ya kamata kowacce al’umma ta yi kwaikwayo. Babban abinda ya fi birge ne a wannan ziyara ba kawai zancen muhawarar Allantar Isa ba ce wadda a karshe ta kare da kiran Mubahalah wadda annabi ya kalubalance su domin tabbatar da waye mai gaskiya, kamar yadda Kur’ani ya kawo cikin K3:58-61 “Lalle ne misalin Isa a wurin Allah kamar misalin Adama ne, Allah ya halitta shi daga turbaya, sannan kuma ya ce masa “Kasance: sai yana kasancewa. Gaskiya daga ubangiji ta ke saboda haka kada ka kasance daga masu shakka. To wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abinda ya zo maka daga ilimi, to ka ce “Ku zo mu kirayi ‘yayanmu da ‘yayanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku sannan kuma mu kankantar da kai sannan kuma mu sanya la’anar Allah a kan makaryata” Kiristocin Najran su kaucewa wannan mubahalah amma ni abinda ya fi burge ni shine yadda ana cikin wannan mukabala da kiristocin sai su ka nemi Annabi ya basu wani waje da za su yi ibadarsu a lokacin da musulmi su ka tashi sallah, sai annabi ya debar musu wani sashi a cikin masallacin nasa inda su ka kebe su ka yi addu’oinsu kamar yaddda su ke yi a coci. Kada mu manta cewa wadannan kiristoci masu da’awar Allah uku ne da Allantakar Isa amma hakan bai hana Annabi ba su damar yin sallarsu a masallacinsa mai alfarma ba. A gaya min, shin haka za ta iya faruwa a wani masallacin musulmi ba ma na annabi ba a yau?

A wannan duniyar da mashahuran malamai irinsu Zakir Naik ke cewa “Taya Kirista murnar kirsimeti ta fi kisan kai muni” Shin ina malamin ya samo wannan fatawa? Ni dai na tabbata ba a Kur’ani ba ne ballantana a hadisi? Ya ilahi kisan kan da Allah ke cewa K5:32 “…wanda ya kashe rai ba da wani rai ba, ko barna a a bayan kasa, to kamar ya kashe mutane duka ne, kuma wanda ya raya rai, to kamar ya rayar da mutane ne gaba daya” Wannan fa shine irin mahimmanci da Allah ya dauki ran mutum da shi, kuma ayar ba ta ce na musulmi ba kawai, kowanne rai kashe shi ba hakki tamkar hallaka duniya ne. Ba wani addini da ya zo da irin wannan hukunci amma shine wani zai kwatanta gaisuwar kirsimeti da kisa? bayan abubuwan da su ka fi kirsimeti a kiristanci an halatta su, kamar aurensu da cin abincinsu da barinsu su yi ibadarsu a masallatanmu idan ta kama?

Wani Malami, Seyid Akrami ya ce “A wannan hargitsatstsiyar duniyar da mu ke ciki wadda ke cike da rikice-rikicen addini, al’adu, siyasa, rashin yarda da juna da yiwa juna mummunar fahimta, assasa fahimta tsakanin addinai na da matukar mahimmanci kuma aiki ne da ake bukatarsa cikin gaggawa musamman ga duk wani wanda ya ke hankoron samun zaman lafiya, da gyara mu’amala da fahimtar juna”

Hakika musulunci ya na tunkaho da taken zaman lafiya, amma a gaskiya halayyar mu ta rashin hakuri da nuna rashin fahimta ga duk wanda mu ka yi sabani, ya sa da yawa wadanda ba musulmi ba ke yin dariya idan an ce musulunci addini ne na zaman lafiya. Duk da addinin cike ya ke da hukunce-hukunce da babu irinsu wajen samar da zaman lafiya, amma a aikace mun gaza matuka. Ya kamata mu tashi mu kwaikwayi rayuwar annabi a Madina, domin ta kawo mana maslahohin dukkan wata matsala da mule fuskanta a yanzu. Lokaci ya yi da za mu fara aiki a aikace ba wai karantawa ba, wadda ba za ta canza komai ba sun mun rungumi aikin.

SendShareTweetShare
Previous Post

Farfado Da Tattalin Arziki Ne Farko, Ba Maganin Korona Ba – Gwamnan Kogi Ga Buhari

Next Post

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutun Kirsimeti Da Sabuwar Shekara

RelatedPosts

Dabi'u

Al’adu Da Dabi’u: An Saki Reshe An Kama Ganye

by Muhammad
12 hours ago
0

Kowace al'umma na da al'adu da dabi'unta wadanda ke bambanta...

Kan Iyakokin Najeriya

Baya Ba Zani: Wadanne Dalilai Suka Sa Aka Bude Kan Iyakokin Najeriya?

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Gwamnatin Najeriya mai abin mamaki, wani lokaci idan ta yi...

Barna

Taimako Ko Barna? 24

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Idan ka gabatar da wannan maudu’in a matsayin tattaunawa a...

Next Post
Kirsimeti

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutun Kirsimeti Da Sabuwar Shekara

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version