Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home Mai Ido A Tsakar Ka

Shin Ka San Rami Mafi Zurfi Da Mutum Ya Taba Hakawa Da Hannu?

by Muhammad
December 25, 2020
in Mai Ido A Tsakar Ka
3 min read
Zurfi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Wasu mutanen suna son sanin yadda har mutum ya iya haka rami mai zurfi sosai a cikin kasa, wanda a kan haka ne muka dukufa domin gano irin kokarin da bil’Adama ya yi na kaiwa karshen kasa.

Ga binciken Dabid Robson.

samndaads

A duk lokacin da muke duba irin gagarumin cigaban da mutum ya yi a fannin gine-gine, muna kallon sama ne. Ka duba Dalar Masar da Cocin St Peters Basilica ta fadar Paparoma ko kuma Taj Mahal da ke Indiya: dukkaninsu manyan gine-gine ne masu tsawon gaske.

To amma abin da ba a sani ba sosai shi ne gagarumin kokarin da aka yi na kaiwa ga karshen karkashin kasa. A binciken da muka yi kan wannan yunkuri, mun bayyana irin nasarorin da aka yi. Daga irin tambayoyin da mutane suka yi game da wannan cigaba, wani yana son sanin yadda dan’Adam ya iya gina ramin karkashin kasa na tsawon daruruwan mita. A kan haka ne muka sake bincikawa domin kara duba wannan kokari.

Yankin na Cappadocia yana karkashin wani yanki ne mai duwatsu marasa karfi sosai, kuma ana ganin mazauna birnin kila sun fara haka ramin ne tun shekara 700 kafin bayyanar annabi Isa (AS). A tarihi mutane sun yi ramuka masu zurfi a karkashin kasa, amma kuma da ‘yan abubuwa na fasaha irin tasu, wadda za a iya cewa kusan da hannu suka yi.

Leburori 50,000 a yankin Kimberly da ke Afrika ta Kudu, sun tona tan miliyan 22 na kasa a aikin da suka fara na tonon dutsen daimon tun a farkon shekarun 1870 har zuwa 1914, inda a karshe suka kai zurfin sama da mita 240 ko kafa 790, kafin a daina aikin.

Ramin wanda ake kira ”Big Hole” a yanzu ana ganin shi ne mafi girma da aka gina da hannu, ko da yake babu cikakkun bayanai, wanda kuma zai iya kasancewa akwai wasu ramukan da aka gina na hannu wadanda suka fi shi.

Rijiyar Woodingdean Well da ke kusa da Brighton a Burtaniya, ita ce rijiya mafi zurfi da dan’Adam ya gina a doron kasa. Rijiyar wadda ta kai zurfin mita 390 ko kafa 1,285 ta kai tsawon ginin Empire State Building me hawa 102 wanda yake birnin, New York a Amurka, amma kuma duk da haka fadin bakinta da kadan ya wuce mita daya.

An rika aikin gina rijiyar ba dare ba rana, inda ake amfani da kyandir idan dare ya yi, kuma masu hakar rijiyar suna turo kasar da suke hakowa waje ta wani winci, sannan kuma a tura musu tubalin da suke daure ramin. A yau fasaha ta ba mu damar gina ramukan da ke da zurfi sosai ta hanyoyi da kaya iri daban-daban. Ta hanyar amfani da nakiya da sauran na’urori, a kasar Afrika ta Kudu aka gina ramin hakar ma’adanai na Tautona da Mponeng, inda aka fasa dutse har nisan kilomita hudu.

Na’urar hawa bene ta kan dauki sa’a daya kafin ta kai karshen wannan rami, wanda zafin cikinsa ya kai 59 a ma’aunin selshiyas (59C), abin da ke nufin sai an sa katafariyar na’urar sanyaya wuri a cikin kafin mutane su iya aiki a ciki. Watakila tsananin zafi da rashin iskar da ke wadannan ramuka masu zurfi, na hakar ma’adanai, za su iya sa mu fahimci yadda rayuwar wasu halittu da ba a doron kasa suke ba, tun da yanayin muhallin daya ne da na sauran duniyoyi.

Haka kuma ta irin wadannan ramuka na hakar ma’adanai masu bincike za su iya gano abubuwan nan masu daure kai, wadanda masana kimiyya suke ganin su ne suka yi duniya. Yadda aka samu ci gaban fasaha a yanzu mutanen da ke kokarin kutsawa cikin karkashin kasa na cigaba da raguwa, tun da yanzu da na’urori ake aiki. Sai dai fa wannan ba zai hana wasu mutanen tona karkashin kasar ba. Al’adar mutum ce neman sanin kwakwaf kan komai a duniyar nan, kama daga tsauni mafi tsawo zuwa karshen ramin da ya fi kowane rami zurfi.

SendShareTweetShare
Previous Post

Al’ajabi Game Da Wani Kauye A Nijeriya

Next Post

Mu’ujizozin Annabi Isah (AS) Da Aka Bai Wa Annabi (SAW) Har Da Kari (II)

RelatedPosts

Samaniya

‘Black Hole’: Wurin Da ‘Ya Fi Duniyoyi Girma’ A Samaniya

by Muhammad
3 days ago
0

A ranar 10 ga Afrilun 2019 aka bayyana hoto na...

Ban Mamaki

Wani Shirgegen Dutse A Sararin Samaniya Ya Gilma Ta Duniyar Dan Adam

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Wani shirgegen dutse mai girman kilomita biyu da digo bakwai...

Aksum

Aksum: Garin Da Ya Yi Suna Wajen Haramta Gina Masallaci

by Muhammad
2 weeks ago
0

Mabiya addinin Kirista Kibdawa a kasar Habasha suna kallon birnin...

Next Post
Annabi Isah

Mu’ujizozin Annabi Isah (AS) Da Aka Bai Wa Annabi (SAW) Har Da Kari (II)

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version