CRI Hausa" />

Shin Ko Ba Wanda Zai Iya Nuna Shakku Ga Amurka A Gabar Da Take Yin Karairayi Yadda Take So?

A zaman kotun dake sauraron shari’ar da majalisar wakilan kasar Amurka ta yi a kwanan baya kan cutar COVID-19, dan majalisar Harley Rouda, ya yi wa darektan cibiyar kandagarkin cututtuka ta Amurka CDC Robert Redfield tambaya cewa, daga cikin Amurkawa da suka rasu sakamakon cutar Marisuwa, ko akwai wadanda a hakika suka halaka a sakamakon cutar COVID-19? Robert Redfield ya amsa cewa, ya zuwa yanzu dai, an gano irin wannan hali bisa bincike da aka yi kan wadanda suka mutu sakamakon cutar Marisuwa.

Labarin dai ya girgiza mutane sosai, wato ke nan maganar Robert Redfield ta ba da tabbacin cewa, akwai wasu da suka mutu sakamakon cutar COVID-19, sai dai an yi kuskuren cewa, sun mutu ne sakamakon Marisuwa. Har ta shaida cewa, akwai yiwuwar cutar COVID-19 ta samu asali daga Amurka. Har illa yau, ana kara zura ido kan kasar Amurka, saboda ganin kuskure da dama da ta tafka a ayyukan dakile cutar. Hakan ya sa, kamata ya yi Amurka ta yi bincike, da kuma ba da bayani kan lokacin bullar cutar, da kuma asalinta bisa ka’idar kimiyya, wanda ya zama matakin da ya wajaba wajen hana yaduwar cutar, da kiyaye lafiyar jama’ar duniya baki daya.
Ya zuwa yanzu dai, masana kimiyya da fasaha na kasa da kasa na namijin kokarin gano asalin wannan mumunar cutar. Kasashen duniya ma na da mabambantan ra’ayoyi game da wannan batu. Amma ya kamata a nuna shakku ne bisa tushen kimiyya da gaskiya, a maimakon a murguda gaskiya, har ma da shafawa sauran kasashen bakin fenti yadda ake so.
Muna fatan a yayin da Amurka ke gudanar da aikin kandagarkin cutar, a wani bangare kuma, ta hada kai da sauran kasashe su yi kokarin binciken asalin cutar bisa ka’idar kimiyya, fasaha da gaskiya, don amsa tambayar jama’ar duniya. (Mai Fassarawa: Amina Xu)

Exit mobile version