Manchseter City na da wasanni 15 da suka rage mata kafin kafa tarihin lashe kofuna hudu a wannan kaka, in da a ranar Asabar za ta fara kece raini da Fulham a gasar firimiyar Ingila kafin ta hadu da wasu kungiyoyin a wasu gasannin daban daban.
Tuni kungiyar ta lashe kofin gasar League Cup, sannan tana da damar sake daga kofin firimiyar Ingila a bana duk da cewa, a yanzu akwai tazarar maki 2 tsakaninta da Liberpool mai jan ragamar teburi.
Kazalika ana ganin Manchester City din ce ke kan gaba wajen samun damar lashe gasar cin kofin zakarun Turai ta bana da kuma gasar cin kofin FA wanda a yanzu taje wasan kusa dana karshe yayinda shi kuma kofin zakarun turai sun kai matakin kwata fayinal.
Kungiyar za ta fafata da Brighton a matakin wasan dab da na karshe a gasar FA, sannan kuma za ta kai ruwa rana da Tottenham a matakin wasan dab da na kusan karshe a gasar zakarun Turai wanda za’a buga a wata mai zuwa.
Manchester City ta samu nasara a wasanni 19 daga cikin 20 da ta buga a baya-bayan nan, abinda yasa ake ganin tana da karsashi na musamman wajen samun nasararori a wasannin da za ta yi a gasa daban daban.