Idris Aliyu Daudawa" />

Shin Ko Wayar Salula Na Iya Warkar Da Ciwon Sikari?

Masana kimiyya sun yi amfani da wayar salula ta smartphone don sarrafa aikin kwayoyin halitta a jikin wata dabba.

An hada kimiyyar rayuwar halittu ce da fasaha don sarrafa yawan sikari a cikin jinin wani bera mai fama da ciwon sikari.

Ana iya amfani da wannan dabara ce wadda aka bayyana a mujallar kimiyya ta Translational Medicine wajen duba lafiyar masu fama da cututtuka nau’oi daban-daban.

Masu binciken na kasar China sun ce dabarar na iya bude wani sabon babi a bangaren fannin ba da magani.

Gwajin dai na iya taimaka wa miliyoyin mutane masu fama da ciwon sikari a fadin duniya ta hanyar takaita yawan sikarin da ke cikin jini.

Sinawa masu bincike sun ce sun kera wasu kwayoyin halittu da ke daidaita sinadarin sikari a cikin jinin bera ta hanyar amfani da wata ‘yar fitila mai haske.

Manhajar wayar salula ce ke sarrafa fitilar daga nesa bayan ta karbo bayanai daga wata ‘yar na’urar kididdige yawan sikari a cikin jinin wadda aka maƙala wa beran.

Mataki na farko ana canza su kwayoyin halittun jiki zuwa wasu masana’antu.

An sarrafa yadda su kwayoyin gadon halittun don samar da magungunan da za su iya takaita karuwar sikari a cikin jini.

Ana kiran wannan fasaha a kimiyyance da suna optogenetics kuma kwayoyin halittu kan fada aiki ba ji ba gani da zarar an dallare su da wani jan haske.

Fasahar dai tana amfani da wani dan kankanin kwan lantarki da kuma wata manhajar wayar salula da take sarrafa shi.

Masu binciken a jami’ar East China Normal da ke Shanghai kan dasa wannan fasaha ce a jikin wani bera, ta yadda za su iya dakile ciwon sikari ta hanyar dan taba fuskar wayar.

Tawagar masu binciken ya ce nazarin “ka iya share fagen wani sabon babi na bayar da magani gwargwadon bukatar mutum ta hanyar fasahar dijital da za ta karade duniya.”.

Masana kimiyyar na bukatar dibar wani dan digon jini don sanin yawan sikari da ke cikinsa ta yadda za su iya kididdige yawan maganin da jiki yake bukata.

Babban manufar su ita ce bullo da wani cikakken tsarin amfani da na’ura don gano yawan sikari da ke cikin jini da kuma daidai kimar sinadarin lakani da za a bayar.

A bayyane take cewar fasahar tana wani matakin farko ne, amma dai ba za a bar shi al’amarin ba wajen magance ciwon sikari ba. Ana iya sarrafa kwayoyin halittu ta yadda za su iya hada magunguna nau’oi daban-daban.

Wani masanin kimiyyar rayuwar halittar curin sinadari, Farfesa Mark Gomelsky a Jami’ar Wyoming, ya ce nazarin wani “cikar wata manufa ce waddai take sa shauƙi”.

Ya kuma kara da cewar: “Nan da wannne lokaci ne za mu sa ran ganin mutane na tafiya a kan titi su.

Hanyoyin Da Za A Kauce Wa Kamuwa Da Ciwon Suga:

An kiyasta cewa mutum miliyan 422 ne ke fama da ciwon sikar, a yayin da kuma ake bukukuwan zagayowar ranar Ciwon Sikari ta duniya, ga abubuwan da ya kamata a sani dangane da ita  wannan cutar, da yadda za ku iya kiyaye kan su daga kamuwa da ita.

Ciwon sikari ko kuma diabetes ciwo ne da kan kasance tare da mai fama da shi na tsawon rayuwa wanda kuma kan yi sanadiyar mutuwar fiye da mutum miliyan daya a ko wacce shekara hakanan kuma kowa na iya kamuwa da ita cutar.

Ana kamuwa da ita ne a lokacin da jikin dan Adam ya kasa sarrafa dukkan sinadarin sikari (gulukos) da ke cikin jini; kuma matsalar kan iya janyo aukuwar bugun zuciya ko shanyewar barin jiki, ko kuma makanta ko lalacewar koda har ma a kan yanke kafafuwan mai fama da ciwon.

Bugu da kari kuma wata matsala ce mai kara yaduwa – saboda kuwa an kiyasta cewar mutane miliyan 422 ne suke fama da cutar a fadin duniya – wanda ya nunka masu fama da ita sau hudu idan aka kwatanta, da shekaru 30 da suka gabata, kamar yadda alkalumman da Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta fitar ke nunawa.

Amma duk da hadarin da mai fama da ciwon kan shiga, rabin wadanda ke dauke ko kuma suka kamu da cutar, ba su mayar da hankali sosai a kanta ba.

Amma kuma shi canza yanayin rayuwa na iya taimakawa a samu kauce ma  kamuwa da cutar.

Ga kuma hanyoyin da za a iya bi.

Me Ke Janyo Ciwon Sikari?

Idan muka ci abinci, jikinmu na sarrafa wani nau’in abinci mai suna kabohaidiret (carbohydrate) zuwa sukari (gulukos). Akwai kuma wani sinadari mai suna insulin da jiki kan samar wanda kan umarci jikin da ya yi amfani da sikarin a matsayin wani makamashi.

Cutar ciwon sikari  ana  kamuwa da ita ne a lokacini da jiki ya daina samar da insulin ko kuma ba ya aiki, kamar yadda ya kamata, al’amarin da kan janyo taruwar sikari a cikin jininmu.

Exit mobile version