Shin Ko Ziyarar Blinken A Kasar Sin Za Ta Bude Sabon Babin Kyautata Alakar Sin Da Amurka?
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shin Ko Ziyarar Blinken A Kasar Sin Za Ta Bude Sabon Babin Kyautata Alakar Sin Da Amurka?

byCMG Hausa
2 years ago
Kasar Sin

A baya bayan nan an sanar da shirin sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken na gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin, ziyarar da za ta kasance mai matukar jan hankali, duba da yadda alakar Sin da Amurka ke cikin wani mawuyacin hali a halin yanzu.

Yayin zantawar da ministan harkokin wajen Sin Qin Gang ya yi da Blinken a jiya Laraba, Qin ya sake jaddada matsayar kasar Sin game da yankin Taiwan, yana mai jaddada dadaddiyar aniyar kasar Sin ta kare ikon yankuna, da mulkin dukkanin sassan kasar.

  • Qin Gang Ya Tattauna Ta Wayar Tarho Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Wanda Zai Ziyarci Kasar Sin

Kafin hakan, Amurka ta sha aiwatar da matakan tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, da suka hada da batun Taiwan, da yankin musamman na Hong Kong da batun jihar Xinjiang da dai sauran su.

Don haka masharhanta ke ganin ziyarar aiki da Blinken zai gudanar a Sin a ranaikun Lahadi da Litinin mai zuwa, za ta ba da zarafin tattaunawa kai tsaye tsakanin bangaren Sin da na Amurka, a irin yanayi da ba kasafai ake samun sa ba.

Tabbas hakan wata dama ce ta tattaunawa, tare da warware sabani kan muhimman batutuwan dake janyo hankulan sassan biyu, musamman a wannan gaba da kasashen biyu ke fatan farfado da nagartar alakarsu.

A bangaren kasar Sin dai a bayyane take cewa, babu abun da kasar ke fatan cimmawa illa bunkasa dangantaka da Amurka bisa tsarin mutunta juna, da wanzar da zaman lafiya da lumana, da cimma moriyar bai daya.

Sai dai a bangaren Amurka, yanayin da ake gani daga manyan jami’an ta, da ’yan siyasar kasar na furta kalamai da fatar baki, da aiwatar da sabanin hakan, ya zamo babban dalilin dake mayar da hannun agogo baya, a kokarin da ake yi na dinke barakar kasashen biyu.

Yanzu dai abun jira a gani shi ne, ko ziyarar da Blinken zai gudanar ta wannan karo za ta share fagen warware sabani, da dora alakar sassan biyu kan turba ta gari.

Ta yadda Amurka za ta amince da dakatar da tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, da kaucewa yunkurin dakile ci gaban kasar ta hanyar sanya takunkumai marasa ma’ana, bisa fakewa da batun tsaron kasa ko wata takara maras adalci. (Saminu Hassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Shawarwari 3 Da Shugaban Sin Ya Gabatar Kan Batun Palesdinu Sun Shaida Matsayin Sin Na Neman Adalci A Yankin Gabas Ta Tsakiya

Shawarwari 3 Da Shugaban Sin Ya Gabatar Kan Batun Palesdinu Sun Shaida Matsayin Sin Na Neman Adalci A Yankin Gabas Ta Tsakiya

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version