Connect with us

MU KOYI ADDINI

Shin Lallai Ne Mai Haida Ta Canza Tufafinta Bayan Ta Yi Tsarki?  

Published

on

Tambaya Ta 10:- A rana ta karshe daga cikin ranakun haida amma kafin tayi tsarki matar bata ga gurbin na jinin haida ba, shin za tayi Azumin wannan rana alhali kuma bata ga farin ruwa ba, ko kuma ya zata yi?

Amsa:- Idan ya kasance a al’adar matar bata ganin farin ruwa idan jini ya dauke mata kamar yadda ake samun wasu daga cikin mata, idan jini ya dauke musu basa ganin wannan farin ruwan daga baya, matar za tayi Azumi.

Idan kuma ya kasance a karshen al’adar tana ganin farin ruwa idan jini ya dauke mata to baza tayi Azumi ba har sai taga wannan farin ruwan.

 

Tambaya Ta 11:- Shin lallai ne mai haida ta canza tufafinta bayan tayi tsarki kuma ta san cewa jini bai taba tufafin ba kuma babu najasa a jikin tufafin?

Amsa:- Ba lallai bane ta canja tufafinta domin shi jinin haida baya bata jiki, shi dai jinin haida yana bata abin da ya taba ne kawai, wato idan ya taba abu to sai ya zama najasa saboda huka ne Annabi (SAW) ya umarci mata da su wanke tufafinsu idan jinin haida ya sameshi wato idan jinin ya taba shi kuma suyi Sallah da tufafin bayan sun wanke.

 

Tambaya Ta 12:- Shin danshi da yake fitowa mace wannan danshin tsarkine ko najasa, Allah ya saka muku da alheri?

 

AMSA: Abin da yake sananne dai a gurin ma’abota ilimi shine dukkan abin da yake fitowa daga hanyoyi guda biyu to NAJASA NE sai dai abu daya ne kawai ba najasa ba – shine maniyi. Shi dai maniyi abu mai tsarki ne in kuwa ba shi ba to duk abin da yake fitowa ma’abocin kazanta ne yake fitowa ta hanyoyi guda biyu. To wannan danshi najasa ne kuma yana daga cikin abinda yake warware Alwala kuma karin bayani akan wannan, ya kasance dukkan abinda yake fitowa mace na wannan ruwa najasa ne kuma dole ne ta sake Alwala. Wannan shine abinda aka samu bayan anyi bincike tare da sashin malamai.

Sai dai ni ina da dan damuwa domin sashin mata suna kasancewa tare da wannan danshi ko yaushe to abin da za tayi shi ne tayi mu’amala irin mu’amalar wanda yake da yoyon fitsari. Sai ta dinga yin Alwala a lokacin ko wacce sallah, idan lokacin sallah yayi sai tayi Alwala tayi sallah.

 

Tambaya Akan Alwala

 

 Tambaya Ta 13:- Shin yana halatta nayi AIwala alhalin a jikina ko fatata akwai wani nau’i na maiko ko manshafawa?

Amsa:- ‘E”, yana halatta a gareki kiyi Alwala koda a jikin ka akwai irin wadan nan manshafawi da sharadin wannan man bai kasance wanda zai hana ruwa shiga jikin ka bane kamar (Janfarce). Idan kuma ya kasance mai kauri ne wanda zai hana ruwan shiga fatar jikin wato kamar (Janfarce) to ba makawa sai an cire shi kafin ayi Alwala.

 

Tambaya Ta 14:- Idan mace mai ciki ta ga wani jini kafin ta haihu da kwana daya ko biyu), shin zata bar yin Azumi da Sallah saboda wannan jini ko ba zata bari ba?

Amsa:- Idan mace mai ciki ta ga jini kafin haihu da kwana daya ko biyu tare da ita akwai tabbacin cewa wannan jini na biki ne, to sai ta bar yin Sallah da Azumi a daIilin wannan jini.

Idan kuma babu wata alama da ta nuna yayi kama da na biki, wato idan ba jinin biki bane to wannan jinin ya zama gurbataccen jini, ba zai hana yin Sallah da Azumi ba.

 

Tambaya Ta 15:- Menene Haida?

Amsa:- Haida shi wani jini ne da yake fita da kansa daga gaban mace. Wace zata iya daukan ciki.

 

Tambaya Ta 16:- Kashi nawa ne mata suka kasu dangane da haida?

Amsa:- Mata sun kasu kashi uku: (1) Wacce ta fara (2) Wacce ta saba (3) Mai ciki.

 

Tambaya Ta 17: Nawa ne mafi yawan kwanakin haida ga wacce ta fara?

Amsa:- Mafi yawan kwanakin haida ga wacce ta fara kwana goma sha biyar ne (15).

 

Tambaya Ta 18:- Menene hukuncin wacce ta saba yin haida?

Amsa:- Wacce ta saba al’ada ta san kwanakinta. Amma idan jinin ya wuce mata ya karu akan kwanakin da ta saba, to sai ta kara kwana uku matukar karin kada ya wuce kwana goma sha biyar. Kuma nayi bayanin yadda za tayi karin kwanaki a kowane wata. Nayi bayani a baya.

 

Tambaya Ta 19:- Menene hukuncin mai ciki? AMSA:- Haidar mai ciki bayan ya yi wata uku to haidar ta kwana goma sha-biyar ko kafin sha biyar. Amma bayan ciki yayi wata shida kwana ashirin ne, wato mafi yawan kwanakin haidar. Amma in ya wuce hakan to ya zama jinin ciwo, sai tayi wanka ta cigaba da ibadarta kamar yadda bayani ya gabata a baya.

 

Tambaya Ta  20:- Menene hukuncin mata idan jinin ya dauke?

Amsa:- Idan jinin ya dauke sai ta kirga kwanakinsa har sai ta cika aI’adarta kamar yadda ta saba wato idan jini ya dauke kafin ya kai kwanakin da ya saba yi mata sai kuma ya dawo to sai ta dinga kirga kwanakin har sai ya kai iya kwanakin da ta saba yi. Kamar jinin ya zo yau sai ya dauke gobe sai kuma ya dawo, jibi to sai ta hada na yau dana jibin ya zama kwana biyu kenan to haka za tayi ta lissafi har sai ya cika kwannakin da ta saba.

 

Tambaya Ta 21:- Shin yana halatta ga mai haida tayi Sallah da makamantan sallar?

Amsa:- Baya halatta ga mai haida tayi Sallah da Azumi da Dawafi da shafan Al-Kur’ani da shiga Masallaci.

 

Tambaya Ta 22:- Shin zata rama daga cikin sallah ko a Azumi?

Amsa:- Za ta rama Azumi amma ban da Sallah.

 

Tambaya Ta 23 :- Shin karatunta wato (mai haida ya halatta?

Amsa:- “E”, karatun ta ya halatta

 

Tambaya Ta  24:- Menene ajikinta baya halatta ga mijinta a lokacin da ta ke haida?

Amsa: Farjinita ne ba ya halatta ga mijinta, kuma abin da yake tsakanin cibiyarta zuwa gwiwoyinta a lokacin da take haida, har sai tayi wankan tsarki, wato wankan daukewar jinin haida.

 

Tambaya  Ta 25:- Menene Nifasi?

Amsa:- Shi Nifasi shi ne wani jini da yake fitowa a lokaci haihuwa.

 

Tambaya Ta 26:- Shin Nifasi wato jinin biki kamar jinin haida yake a wajen hukunci?

Amsa:- Jinin biki kamar jinin haida yake wajen haninsa, wato duk abinda ake bari idan jinin haila yazo to haka ake bari idan jinin biki yazo kamar barin Sallah da Azwni da sauran ibada.

 

Tambaya Ta 27:- Nawa ne mafi yawan kwanakin jinin biki?

Amsa:- Mafi yawan kwanakin jinin biki kwana sittin ne (60).

 

Tambaya  Ta 28:- To menene hukuncin mace idan jinin biki ya yanke mata kafin ta cika kwanna sittin.

Amsa:-  Idan jinin ya dauke mata kafin,ta cika kwana sittin to sai tayi wanka tayi Sallah tayi Azumi, idan Iokacin Azumi ne, kuma mijinta zai iya saduwa da ita tunda ta tsarkaka.

 

Tambaya Ta 29:- Sannan kuma me zata aikata idan jinin bikin ya dawo mata?

Amsa: Idan jinin ya dawo mata, idan ya kasance tsakaninsa da na baya wanda ya dauke din nan kwana goma sha biyar ne tsakaninsu ko kuma ya fi kwana goma sha biyar sai ya dawo, to na biyun nan haida ne. Idan kuma tsakanin na farko da na biyun, wanda ya dawo bai kai kwana goma sha biyu ba, to sai ta hada lissafin kwanakin da da farko ya kasance daga cikan lissafin kwanakin jinin biki.

 

Tambayoyi Akan Azumi Dangane Da Mai Jinin Haila Ko Biki

 

Tambaya Ta 30:- Shin mace mai jinin haida da  mai jinin biki za su ci abinci su sha abin sha lokacin Azumin Ramadana?

Amsa: “E”.  Za su ci su sha abin sha a  Azumin Ramarlana, sai dai abinda yafi kyau hakan ya zamo a asirce, idan ya kasance akwai wani daga cikin yara tare da wannan matar a cikin gida, domin cin abincin matar da kuma shan abin shan nata zai rikitar da yara, to don haka sai taci a boye kar yaran su gani. Bayan ya dauke sai ta rama Azumin da ta sha.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: