Abubakar Abba" />

Shin Me Ya Sa A Ke Kiran Wannan Tsarin Da Pork?

Wannan tsarin an sanshi a fadin duniya, inda ya kai sama da kashi 40 na naman da ake ci.

Yana dauke da sanadarin (protein) mai yawa da kuma sanadarin Bitamin dana minerals da amino acid wadanda sukkan wadannan sanadaran su na inganta lafiyar jikin dan adam.

Wasu daga cikin samfarin irin wannan naman, kamar wanda ake kira a turance tenderloin da loin chops da  sirloin roast sunfi sanya lafiya ga jikin dan adam fiye da Kifi.

Wannan fannin na kasuwanci, tsari ne da yake sanya lafiya kuma hanya ce ta samun kudin shiga ga masu yin sana’ar.

Tuni ga wasu ‘yan Nijeriya da suka rungumi wannan sana’ar ta ‘Pork Money’ sun samar da wasu tsari ta hanyar ajiye naira 250,000 tare da  abokan cinikayyar su a karkashin jagorancin wani dan wasa kuma dan kasuwa dan kasar Ghana mai suna John Dumelo da Oke-Aro da zasu fara kiwon aladu wadda zata kasance mafi girma a nahiyar Afrika don fara aikin a Nijeriya da kasar Ghana wadda a hankali, sana’ar zata bazu zuwa wasu kasashen dake nahiyar Afrika.

Shirin na ‘Pork Money’ za a kaddamar da shi ne a ranar 4 ga watan Yunin shekarar 2018.

Exit mobile version