Kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ta yi rashin nasara hudu a jere a dukkan fafatawa a bana, wanda hakan ya sa wannan kaka ta zama daga cikin mafi muni gare ta tun bayan watan Nuwamban 2014. Tun farko kungiyar ta fara kakar ta bana da kafar dama, inda magoya baya
suka yi fatan za ta kare kambunta na kofin Premier League da ta dauka, inda a farko ta lashe wasanni biyar a jere a gasar Premier ta Ingila.
Wani abun mamaki cikin kungiyoyin da Liberpool ta yi nasara a kansu su ne Bournemouth da Newcastle, da Arsenal da Burnley da abokiyar hamayya Eberton. Haka kuma Liberpool ta yi nasara kan Atletico Madrid a Champions League da yin waje da Southampton a Carabao Cup.
- Al Hilal Za Ta Biya Yuro Miliyan 53 Don Ɗaukar Nunez Daga Liverpool
- Ɗan Wasan Liverpool, Diogo Jota, Ya Mutu A Hatsarin Mota
Kafin fara kakar bana, Liberpool ta kashe sama da fam miliyan 400 wajen sayen sabbin ‘yan wasa, domin ganin ta mamaye kakar bana, kamar yadda ta yi a bara.
To sai dai bayan fara kakar bana Liberpool kan ci kwallon da ke ba ta nasara ne daf da tashi, in banda karawar da ta doke Eberton. Ciki har da wanda Bournemouth ta farke kwallo biyu, daga baya Liberpool ta sa kwazo ta samu maki ukun da ta ke bukata.
Shi ma wasan da ta yi nasara a kan kungiyar Sifaniya a daf da za a tashi ta ci kwallon a gasar Zakarun Turai da na Newcastle United a Premier League. Tun daga nan alamomi suka fara bayyana cewar akwai tarin matsaloli a Liberpool, wadda kowanne wasa kwallo ke shiga ragarta in ban da wanda ta yi nasara a kan Arsenal 1-0 a Premier League cikin Agusta da wanda ta ci Burnley 1-0 a cikin watan Satumba a Premier League.
Sababbnin ‘Yanwasan da Liberpool ta saya a kakar banamages Giorgi Mamardashbili daga Balencia Jeremie Frimpong daga Bayern Leberkusen, Florian Wirtz daga Bayern Leberkusen,
Milos Kerkez daga Bournemouth, Hugo Ekitike daga Eintracht Frankfurt, Aledander Isak daga Newcastle United, Armin Pecsi daga Puskas Akademia. Giobanni Leoni daga Parma Freddie Woodman daga Preston North, Will Wright daga Salford.
Wasu daga cikin matsalolin Liberpool A Yanzu
- Matsalar masu buga mata tsakiya Liberpool ta samu sauye-sauye da yawa a fannin masu taka mata wasa daga tsakiya, bayan da wasu daga ciki suka bar kungiyar, ya dace a ce ta hada
fitattun da za ta fuskanci kakar bana.
Liberpool ta dauki Florian Wirtz daga Bayern Leberkusen, amma har yanzu dan wasan bai nuna kansa ba, inda yake ta shan suka daga magoya bayan da suke ganin kwalliya ba za ta biya kudin sabulu ba.
- Raunin ‘yanwasa da ke jinya
Raunin da wasu ‘yanwasan Liberpool suka ji sun taka rawar gani da kungiyar Liberpool ke kasa kokari a kakar nan. Daga ciki mai tsaron baya, Giobanni Leoni ya ji rauni a wasansa na farko a kungiyar, wanda ake cewa yana doguwar jinya. Mai tsaron raga Alisson Becker ya ji rauni a lokacin gasar zakarun turai wanda ake cewar zai yi jinya har karshen watan Oktoba, watakila ya wuce hakan.
- Bayan Liberpool na yoyo
A kakar bara bayan Liberpool ya yi yoyo, duk da cewar kungiyar ce ta lashe kofin, amma dai an samu matsaloli da yawa a bayan. Kungiyoyi da dama sun amfana da kurakuren Liberpool a bara daga ciki har da Nottingham Forest da Brighton da kuma Brentford.
Wasu lokutan da zarar Liberpool ta kai kora sai kaga wagegen gibi tsakanin masu tsare baya da ‘yan tsakiya. Haka kuma tun kafin fara kakar bana, Liberpool ta buga wasannin atisaye, kuma tun a lokacin gurbin masu tsare baya ya nuna matasalar da kungiyar za ta iya fuskanta da fara
kakar nan.














