Abba Ibrahim Wada">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Shin Neymar Da Mbappe Za Su Bawa Pochettino Hadin Kai?

by Abba Ibrahim Wada
January 4, 2021
in WASANNI
2 min read
Neymar Da Mbappe
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Yanzu babban abinda sabon mai koyarwa Mauricio Pochettino zai nema a kungiyar daga wajen ‘yan wasa bai wuce hadin kai daga wajen shahararrun manyan ‘yan  wasan kungiyar ba, Kylian Mbappe da Neymar.

Manyan ‘yan wasan kungiyar, Neymar da Kylian Mbappe suna daya daga cikin wadanda zasu taka muhimmiyar rawa wajen nasarar sabon mai koyarwa duba da irin tasirin da suke da shi a kungiyar saboda kwarewarsu da kuma girmansu a idon duniya.

samndaads

Tuni wasu rahotanni daga kasar Ingila suka fara bayyana cewa korar da kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta yiwa kociyan kungiyar Thomas Tuchel zata iya hana dan wasa Kylian Mbappe komawa Real Madrid a karshen kakar wasa idan har yaga kamun ludayin Pochettino.

A ranar Alhamis din data gabata ne kungiyar kwallon kafa ta PSG ta kori Thomas Tuchel, dan asalin kasar Jamus sanarwar da akasarin kafafen yada labaran Faransa dana nahiyar turai suka yi ta yadawa ta tabbata.

Rashin lashe kofin zakarun Turai ya sa magabatan kungiyar ta PSG suka yanke shawarar korar Tuchel bugu da kari a wannan kakar wasan kungiyar bata buga abin arziki a gasar lig one ta kasar Faransa kuma tuni kungiyar ta shiga tattaunawa da wani makusancin Tuchel, dan kasar Argentina Mauricio Pochettino.

Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa tafiyar mai koyarwa Tuchel, wanda basa shiri da Mbappe zata iya sanya dan wasan ya zauna a kungiyar duk da cewa wasu daga cikin manyan kungiyoyi ciki har da Real Madrid da Liverpool suna bibiyar dan wasan dan asalin kasar Faransa.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai tayi alkawarin sayan dan wasa Mbappe idan an kammala kakar wasan bana wanda hakan ne yasa kungiyar bat sayi dan wasa ko daya ba a kasuwar data gabata saboda tana tara kudin sayan Mbappe.

A kwanakin baya dan wasan shima ya bayyana cewa bashi da burin ci gaba da zaman kungiyar kuma yana fatan a karshen kakar wasa zai koma daya daga cikin kungiyoyi manya a nahiyar turai.

Shima dan wasa Neymar, wanda baiji dadin korar da akayiwa Tuchel ba, yana bukatar tsayawa domin karatun ta nutsu akan yanayin da kungiyar zata kasance nan gaba duba da har yanzu ba’a san wanda kungiyar zata dauka ba.

A kwanakin baya Neymar ya bayyana cewa zai iya barin kungiyar ta PSG idan har shugabannin kungiyar ba suyi kokarin sayo dan wasa Messi ba wanda yake shirin barin Barcelona a karshen kakar wasa ta bana.

Sai dai PSG zata fuskanci kalubale daga wajen wasu daga cikin manyan kungiyoyi kamar Manchester City, wadda kociyan kungiyar yake da alaka mai kyau da Messi sai kuma kungiyoyin Chelsea da Inter Milan.

SendShareTweetShare
Previous Post

Tabbatar Da Tsaro: NAF Ta Gundunar Da Gagarumin Atisaye A Hanyar Abuja-Kaduna

Next Post

Manchester United Za Ta Sayar Da Pogba A Karshen Kakar Wasa

RelatedPosts

United

Manchester United Za Ta Iya Bawa Duniya Mamaki

by Abba Ibrahim Wada
14 hours ago
0

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Robert Pires,...

Zura Kwallaye

Ronaldo Yana Shirin Zama Wanda Ya Fi Zura Kwallaye A Duniya

by Abba Ibrahim Wada
14 hours ago
0

A daren ranar Larabar data gabata dan wasa Cristiano Ronaldo...

Lampard

Ana Dab Da Korar Lampard A Chelsea

by Abba Ibrahim Wada
2 days ago
0

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa shugabannin kungiyar ta...

Next Post
Pogba

Manchester United Za Ta Sayar Da Pogba A Karshen Kakar Wasa

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version